An samu sabanin ra’ayoyi tsakanin malamai maraji’ai game da limancin mace ga mata a sallar jam’I da zamu kawo bayanin kamar haka:
1. Mafi yawan marja’ai sun tafi a kan cewa bisa ihtiyadi wajibi ne limancin mace ga ‘yan’uwanta mata ba ya inganta[1].
2. Wasu kuwa suna ganin ya halatta mace ta yi limancin ga mata[2].
3. Wasu kuwa suna ganin yin limancin mace ga mata karahiya ne in ba a sallar mamaci ba[3].
4. Wasu kuwa suna ganin bisa ihtiyadi mustahabbi wanda zai yi wa mata limanci ya kasance namiji ne[4].
[1]. Ayatullahi Gulfaigani (in ban da sallar mamaci); Imam khomain, taudhihul masa’il (hashiya), daga: Banu Hashimi Khomain, sayyid Muhammad Husain, j 1, shafi 791, Daftare Intisharate islami, Kum, Bugu na takwas, 1424 K.
[2]. Marja’o’I bahjat, Khamna’I, makarim shirazi, makarim (bisa ihtiyadi wajibi mace mai istihadha ba ta da hakki ta yi wa mata limancin jam’i); bahjat, Muhammad Taki, istifta’at, j 2, s 293, mas’ala 2618, ofishin ayatullahi bahjat, Kum, bugu na farko, 1428 h.k; Taudhihul Masa’il (hashiya), j 1, s 791, 793 da 811.
[3]. Marja’o’I da suka hada da Safi, khurasani, hashiyar Taudhihul masa’il, s791, wahid Khurasani, Husain, taudhihul masa’il, shafi 286, m 1461, makarantar Imam Bakir (a.s), Kum, na tara, 1428, h k.
[4]. Subhani, Ja’far, risalar taudhihul masa’il, s 297, mu’assar Imam Sadik (a.s), Kum – Iran, na uku, 1429 h.k.