Shi wasan a kan kansa ba haramun ba ne, sai dai idan yakan cutar da mutanen da ke kusa ko na nesa kamar makoci yakan samu hukunci daban kamar yadda malamai masana tunanin dan Adam suka fada cewa ya kamata gare shi ya kula sosai da irin wadannan abubuwan da zasu iya kai shi ga rashin tsari a ciki ko kuma zubar da mutunci, zaka ga malamai da yawa na Magana da iri wannan salo na nuna a kula da muru’a (mutunci) a cikinsa
MAGANAR AYATULLAHIL KHAMANA’IY
Idan hakan idan hakan zai cutar da mutane ko kasa mai tsarki da sabo ko kuma shari’a ta yi hani da shi to ya zama haram
AYATULLAH MUKARIMUSH SHYRAZY (MZ)
Dole a nuisance shi ko da kuwa ba kowane lokaci yakan cutar da makoci ba idan har yana cutar da makocin
AYATULLAHI KULY KHANY (MZ)
Babu laifi idan kawai kiwonsa ne ko aje shi domin kallonsa da jin dadin zama da shi sai dai in har zai wuce gona da iri ta yadda zai shagalar da mutum fiye da kima, a nan kiwon akwai matsala don kuwa zai jaza samun zunubi wanda ke iya zama haram.
AYATULLAHI SYSTANY (MZ)
Babu laifi shi yin kiwon (tsarewar)
AYATULLAHI TDAHRANY (DB)
Idan kiwata tsintsayen ana yinsa ne domin wani abu mai amfani, kamar kai su wajan da babu irinsu ko domin yalwata su da sauransu a nan ya halatta kuma ba a bin kyama ba ne, amma in har zai haifar da akasin hakan to ya zama makaruhi. Idan kuwa zai cutar da muminai ko haifar da aikata haram bai halatta ba sam.
Don karin bayani kan haka duba bangaren fatawa lamba 1115