Lambar Shafin
fa12557
Lambar Bayani
24204
Jimilla
Hakoki da Hukuncin Shari'a,گوناگون
Takaitacciyar Tambaya
Idan akwai dige-dige a wani bangare na fatar mace shin za a iya kawar da ita ta hanyar na’ura tare da sanin mijinta?
SWALI
Ina da fata marar kyau ta yadda zaka ga akwai dige-dige a kan fatar na yi kokarin kawar da ita ta hanyoyi da dama ban samu nasara ba yanzu sai dama ta samu shi ne ta hanyar amfani da hasken wuta a asibiti duk da cewa akwai dora wa kai nauyi ga kuma wahalarsa bayan tsada da yake da shi amma ina da damar na jure wahalar tasa, tambayata ita ce shin zan iyayin hakan tare da yardar mijina kuwa?
Amsa a Dunkule
Ra’ayoyin wasu malamai daga muraji’an taklidi a kan mas’alar kawar da wannan ta hanya hasken wuta (radiation) su ne kamar;
AYATULLAHI SYSTANY (MZ)
Idan cikin ba zai haifar da kallo ko shafa ta haramci ba kuma babu cutarwar da zata haifar da tawaya ga wanda aka yi wa aikin babu laifi a yi hakan.
AYATULLAHI SYSTANY (MZ)
Idan ta takurawa mai ita babu komai.
AYATULLAHI MUKARIMUSH SHYRAZY (MZ)
Shi yin aikin a kan kansa babu laifi matukar bai cakuda da haram ko cutarwa ba, amma da zai zamanto dole a yi tare da cewa akwai haram a ciki (kamar kallo ko shafa ) a nan bai halatta sai dai a halin larura.