Halaccin takalidi na daga cikin lamuran da ke wajabta wa mai yin takalidi ya yi iya kokarinsa a cikin lamarin kuma lalle fatawar mujtahidi ba ta isar wa mai yin takalidi, saboda haka wannan mas’alar na daga cikin mas’ala mafi girman mihimmanci.
Sananne ne cewa shi mukallidi yana yin takkalidi da dayan mujtahidai bisa daya daga cikin dalilai masu zuwa:
- Hakika a dabi’ance hankali na hukunta wa mutumin da ke neman ya zurfafa masaniyar sa har ya kai ga kokkoluwar sani a cikin wani lamari a yayin da ya zama bai da cikakken sani game da wannan lamarin, da ya komawa wadanda suke da kwarewa (sepacialization) a wannan fagen. Lalle ne a koma ga kwararru masu masaniya ta yau da gobe a wannan fannin, kamar dai yadda ake komawa ga likita domin warkar da mara lafiya, wannan mahangar ta hankali a dabi’ance tana wajabtawa mukallafi kuma hankali na hukumta masa komawa ga mujtahidai a cikin hukunce hukncen shari’a wandanda suke kwararru ne kuma malamai ne su a wannan fagen.
- Dukkanin musulmi ya san cewa a kwai nauyaye nauyaye na wajibi da kuma wadanda a ka haramta a musulumci, kuwa wannan dunkulalliyar masaniya ita kadai ta isa ta sa mutum ya zama abin tambaya a kan abubwan da suka hau kansa, kuma domin tsayawa da wadanan ababan da suka hau wuyansa babu wata hanya a gabansa im ba wadananna guda ukun masu zuwa ba:-
Na daya:- shi da kansa ya yi iya sa’ayin sa har ya kai ga sanini wadannan hukunce- hukuncen sannan ya yi aiki da su bisa asasin masaniyar sa.
Na biyu:- idan har ya kasance bai kai ga zuzzurfan sani ga hukunce-hukuncen ba, sai ya yi aiki da sanin sa ta yadda zai iya kaiwa ga tabbatccen yakini kan hukuncin da ya isa zuwa gare shi a yayin zuwa wajibai dama sauran nauyaye-nauyayane da suka hau kansa, wannan na nufin ya bi hanyar ihtiyadi (riga kafi) a cikin dukkanin hukncin da yake tsamanin wajibi ne ko mustahabbi. (sai ya dauke shi a matsayin wajibi).
Na uku:- ya dogara a kan ra’ayin kwararre masani malami sai ya bi maganganunsa a wajen tantance wajibi da haram a cikin ko wace mas’ala.
Ta hanyar wadanna hanyoyin guda uku ne baligi zai iya sauke nauyin da ya hau kansa.
Amma hanyar nan ta farko tana bukatar lokaci mai tsawon gaske kafin mutum ya isa zuwa gar eta, kuma shi kansa baligin a yayin da yake kan hanyar cimma wannan matsayin yana da bukatar ya jingina zuwa daya daga cikin sauran hanyoyi biyun.
Amma hanya ta biyu, kari a kan bukatuwar sa ga cikakkaen sani da faffadan tsinkaye dangane da wajibai da haramce-haramce da kuma sanin yadda ake yin ihtiyadi a cikin ko wace matsala, hakika yana da walar gaske, a wani lokacin ma ba shi yiyuwa sam sam, don haka ba wata hanya da ta rage wa baligi sai hanya ta uku.
Wannan dalilin na tanbbatar da wajabcin yin takalidi da mujtahidi a cikin matsalolin da yake tsammanin wajabci da haramci a cikin su haka ma matsalolin da yak e tammanin mustahabbanci a cikin su wadannan ake so a zo da su. Sai dai dalili na farko ya tabbatar da halaccin takalidi a cikin dukkanin mas’aloli.
Amma mas’alolin da ake yin takalidi a cikin su ne reshen addini kamar irin mas’ala da ta halatta wanzuwa kan takalidin mamaci na daga cikin mas’alolin da baligin ba zai iya isa zuwa gareta da sanin sakamakon ta in ba mujtahidi ba ne shi. Kuma babau makawa a gare shi da ya bi wadannan hnayoyin gida biyu a cikin ta, hanyar ihtiyadi da kuma ta takalidi.
Kuma akwai karin wasu dalilai kan halaccin yin takalidi ko kuma wajabcin wanzuwa a cikin wata iyaka da kewaye na ijtihadi da kuma ra’ayin wani mujtahidi, a irin wannan matsayar babu makawa da a riki ra’ayin mujtahidi a fatawarsa kan hakan.