Akwai hanyoyi mabanbanta domin tabbatar da “shugabancin malami” sai dai a nan za mu isu da ambaton dalilai guda biyu na hankali da na ruwaya domin tabbatar da ita.
- Dalili na hankali:
Hankali ya tabbatar da wajabcin samun mutumin da ke da masaniya mai dabi’u na gari saman ko wace hukuma ta akida wacce ke da asasi, a shari’ar musulumci kuwa, malamai su ne ainihin wanna mutumin wanda yake masanin hukunce-hukunce da tushen sani wanda yake daga Allah.
- Dalili wanda a ka nakalto:
An kafa hujja da ayoyi da ruwayoyi masu yawa domin tabbatar da shugabancin malami. Daga ciki akwai:
- Marigayi Saduk ya nakalto daga shugaban muminai (amincin Allah ya tabbata a gare shi) yana cewa manzon Allah (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) yana cewa: “ya Allah ka ji kan halifofi na, sai aka ce da shi su waye halifofin ka sai ya ce? Sai ya ce : wadanda za au zo a abaya na su rika nakalto hadisai na da sunna ta”
- Tauki’in (wasikar da ke zuwa daga imam mahdi ( Allah ya gaggauta bayyanar sa) a likacin rayuwar wakilan sa hudu) nan madaukaki da marigay aSaduk ya rawaito shi a cikin littafin ikmalud din daga ishak dan yakubu a inda imam (amincin Allah ya tabbata a gare shi) yake ba shi amsar tambayoyinsa da rubutun hannunsa mai albarka:
“amma dangane da abubwan da suke faruwa, (yau da kullum) ku koma ya zuwa marawaita hadisan mu hakika su hijja ne a kan ku ni kuma hujjar Allah ne a kansu”
Akwai hanyoyi mabanbanta domin tabbatar da “shugabancin malami” sai dai a nan za mu isu da ambaton dalilai guda biyu na hankali da na ruwaya domin tabbatar da ita.
- Dalili na hankali:
Babbu shakka kan cewa alumma na da bukatar shugaban da za ta koma ya zuwa gare shi, ta wani bangaren kuma zaka ga cewa tabbas al’amuran hukunci ba sa fice wa daga gewayen addini, ballantana ma hakika gabaki dayan tushen dadini wanda ya hada komai da komai (na duniya baki daya) sun bayyana a hannu cikamakin annbawa (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) bisa tsari cikakke kammalalle. Kuma hannkali baya ganin akwai wani dalili da zai hana addini ya yi kane kane a cikin lamarin mulki, ba wannan kawai ba! Ya kamata ya zama haka ne kamar yadda hikama ta hukunta, idan har muka kalli hukuma a mahangar addini za mu ga cewa kuma muka dauka cewa babban aiki na asali ga wannan hukuncin shi ne shi ne kiyaye halayya da dabi’un da Allah ya yarda da su da kuma tsayar da hunuce-hukuncen addini, to lalle hankali na wajabta samuwar wani mutum da ke jagorantar wannan gwamnatin kuma ya zama masain Allah ta’ala da hukunce hukuncen addini da wajibai kuma wanda zai iya shugabantar al’umma.
Idan kuma ma’asumi yana raye to hankali na hukunta ya zama shi ne shugaban, amma idan aya faku shi ne wanda zai yi hukunci da cewa malamai masana adalai wadanada suka cancanci shugabance (suke da kwarewa a a kai) ne za su hau wanna matsayin.
Da wani yaren, hakika hankali na hukunta larurar samuwar wani mutum wanda ya san jiga-jigai ko asasin addini yana jagorantar hukuma ta akida mai al’adu (wadanda a ddini ya tsaya a kan su), kuma a addinin musulunci wannan asasin shi ne dokoki da hukunce-hukuncen Allah ta’ala, kuma ainihin wannan masanin su ne malamai.
- Dalili na nakali:
Za a iya kafa hujja da ruwayoyi masu yawan kan tabbatar da shugabancin malami, daga ciki akwai:
- Abin da marigayi Saduk ya nakalto daga shugaban muminai (amincin Allah ya tabbata a gare shi) cewa manazon Allah (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) ya ce “Allah k aji kan halifofi na”, sai aka ce masa su waye halifofin ka? sai ya ce:
“wadanda za su zo a baya na su rika rawaito hadisai na da sunnata”, a nan sai mu ce; ko wace ruwa ana yin bahasi biyu mihammai a kan ta.
- Sanadin ruwaya (silsilar marawaita hadisin)
- Abin da hadisin ko yin nuni gare shi, domin tsayar da hadisin da kuma iyakance shi kan abin da yake yin nuni zuwa gare shi.
Muna da cikakkiyar nutsuwa kan cewa wannan hadisin ya zo ne daga manzo (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) kuma ba wani kokwanto kan ingancinsa domin ya zo ta hanyar sanadodi mabanbanta kuma a cikin litattafai daban daban na masu yawa.[1]
Amma yin sharhin wannan hadisin na bukatar waiwayar wasu abubuwa guda biyu:-
- Manya-manyan ayyukan Annabi guda uku ne.
Isar da sako: wato isar da sakon ayoyin Allah ta’ala da kuma bayanin hukunce-hukuncen shari’a da kuma shiryar da mutane.
Hukunci (alkalanci): shi ne yin hukunci kan abin da mutane suka yi sabani a kan sa da kuma waware rikici.
Shugabanci: shi ne jagorancin al’umma musulma da kuma gudanar da lamuranta.
- Wadanada ake nufi da “wadanda za su zo bayan Annabi su rika rawaito hadisan sa da sunnar sa”, su ne malamai ba masu rawaito hadisi ba, ba masu karantoshi ba, domin marawaici ba zai iya banbance tsakanin abin da ake kira hadisin manzon Allah (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) da kuma sunnar sa ba, ta yiyu ya zama ya ji maganar ne ko kuma ya ga wani aiki ne sai ya nakalto shi bai yi wani abu da ya wace haka ba, ba zai iya tabbatar da dalilin wannan maganar ko aikin ba, ko kuma ya iyakance abin da ke bijirowa aikin ko zance ko kuma abin da ya kebance shi ko ya iyakance shi ba, kamar yadda bai san yadda zai daidaita tsakanin sa da kuma tsakanin abin da ke kishiyantar sa ba, kadai mutumin da zai iya yin wannan shi ne mmutumin da ya kai martaba da matsayin yin ijtihadi da bada fatawa wanda ya kai kololuwar fahimta mazaukakiya.
A karkashin wadannan matakan biyu da muka ambata zai zama abin da ake nufi shi ne “malamai (fakihai) halifofin Annabi (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) ne su” kuma tun da Annabi (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) na da ayyukan da nauyaye-nauyayen da suka hau kan sa, tare da cewa hadisin bai iyakance ayyukan da halifan zai yi ba, to kenan zai halifanci Annabi a cikin dukkanin sha’noninsa.[2]
Wasu sashi sun tattauna, kan kafa hujja da wannan ruwayar da ma makamanctan ta da na daga ruwayoyin da suka zo da lafazin halifa, kuma su ka yi da’awar abin da zai zo nan gaba:-[3]
“halifa na da ma’ana biyu: na farko ma’anar ta ta luga (wato yare) ta asali kuma a bin da ya zo a cikin alkur’ani mai girma na daga wannan kalmar kuma ta zo ne da wannan ma’anar, kamar misalin fadin sa madaukaki {lalle zan sanya ka halifa a bayan kasa}.[4] Ko kuma fadinsa madaukaki {ya dawud hakika mun sanya ka halifa a bayan kasa ka yi hukunci tsakanin mutane da gaskiya}[5], halifanci a aya ta farko al’amari ne kasantacce wanda aya bukatar nadawa ko shar’antawa, duk da cewa ma’anar halifancin a a ya ta biyu lamari ne na shari’a sai dai ya kebanta ne kawai da hukunci da alkalanci.
Ma niyu: ma’anar kalmar a siyasance a tarihance (yadda a kayi amfani da ita a sha’anin mulki a tsawon tarihi), wancce (ma’anar kalmar) ta bayyan ya a cikin musulumci da kuma bayan wafatin Annabi (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi), hakika wannan man’ana duk da cewa an yi amfani da ita a duniyanci kuma an yi ta yin wasa da wannan kalmar an dauke ta aka rika mannawa wanda ya dace da wanda bai dace ba, to lalle wannan bai da ko kwarzane na alaka da matsayin imamanci da manzanci wadanada suke matsayi ne da Allah ta’ala da ke ba wanda ya so”
Amma idan muka zurfafa tunani kan ma’anar nan ta “halifa” a yarance (yare ko harshe ko luga) wacce ke nufin “wanda ke wakiltar mutum” mun samu cewa baki daya an yi amfani da wannan kalmar da aka yi a cikin alkur’ani da hagisi kai har ma da tarihi ya kasance da wannan ma’anr ta ta ce ta luga, idan ma har akwai wani sabani da ya shafi yanayin wakilcin da aka yi ne kawai, wani lokaci wakilcin kan kasance bisa lamarin ne kasantacce tabbatacce wani lokaci kuma ta kan kasance a cikin lamarin shari’a da daukar nauyin kiyaye abu bisa doka.
Kodama a ce kalmar “halifa” ta bayyana ne bayan wafaitn Annabi (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) tana nan dai da ma’anar nan ta ta ta wakilci ko kuma mutumin da zai gaji Annabi (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) a cikin jagorancin mutane. Halifa nai da wata ma’ana ta daban wacce ta wuce wannan, ballanatana ma’ana daya kawai take da ita duk da cewa ana amfani da wannan kalma a warare mabanbanta, a ruwayar nan da aka nakalto kalmar halifa ta zo da ma’anar matemaki kuma tun da har ba ta ayyana ko fayyace wani bangare na wakilci ba, to za a dauke ta mudlaka[6] kuma ta mamaye ko wane bangare kuma tana nuni bisa cewa malamai magada Annabi (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) ne a ko wane bangare.
2. Tauki’in[7] nan madaukakai wanda marigayi Saduk ya rawaito shi, a cikin littafain nan na ikmaluddin daga ishakdan Yakuba a yayin da imamin zamani (Allah ya gaggauta bayyanar sa) yake bada amsa da rubutun hannuun sa mai albarka “amma fare faren da ke abkuwa (yau da gobe) ku koma wa masu rawauto hadisan mu domin su hujja ta ne a gareku ni kuma hujjar Allah ne a kan su”.[8]
Marigayi shekh dusi ya rawaito ainihin wannan ruwayar a cikin littafin sa algaiba tare da dan sabani a karshen hadisin, ya zo da cewa: “ni hujjar Allah ne a kanku a maimakon ni hujjar Allah ne a kansu” [9]
Marigayi shekh dabrasi ya nakalto wani hadisi a cikin littafin sa “ihtijaj” sai dai abin da ya zo daga cikin wannan shi ne “ni hjjar Allah ne a kan su”[10] duk da cewa wannan banbancin na nakaltowa ba zai yi tasiri ba a wajen manuniyar ruwayar ba kamar yadda zai zo a cikin sharhi:-
Amma ta bangaren sanadi hakika wannan ruwayar har ya zawa is’hak dan Yakubu sanadi ne mai karfi domin wani adadi na marawaita ya nakalto shi ta wata hanya daga kulaini daga ishak dan yakuba. Baba wata nagartarwa[11] (wasaka) ta musamman da ta zo kan ishak dan yakub, a daga a cikin litattafan mazaje kuma wasu sun yi kokarin cewa wai shi dan’uwan marigayi kulaini ne[12], sai dai wannan kokarin wanda bai kai ga nasarar da ake bukata ba, ba abu ne mai tasiri sosai ba, ingantacciyar hanyar tabbatar da nagartar sa ita ce kamar haka: bisa la’akari da yanayin da imam ma’abocin zamani (amincin Allah ya tabbata a gare shi) yake ciki a lokacin da ya yi karamar fakewa tare da la’akari da tsananin da ake ciki a wannan lokacin wadanada su ne suka sabbaba boyuwar sa daga idnun mutane da kuma takaita saduwa da shi ta hanyar wakilansaguda hudu, hakika zawan ko wace wasika (tauki’I ) daga gare shi na nuni ya zuwa cewa yana raye kuma yana jagorantar mutane kuma ba zai ba da wannan wasikar ga kowa ba har sai ya tabbatar da amincin sa, don haka shi kan sa ba da wasikar a wannan lokacin na nuni ya zuwa nagartar wannan mutumin da ya nakalto hadisin.[13]
Idana aka ce ta ina maka tababbatar da cewa ya sami wannan wasikra daga ma’abocin zamani ( Allah ya gaggauta bayyanar sa) sai ya zama karya ya yi kenan a cikin abin da ya ke da’awa?
Za mu iya amsa masa da cewa : da yake kulaini ya nakalto wannan tauki’in daga gare shi – bisa la’akari da abin da ya gabata baba makawa ya kasance yana ganinsa managarci in ba don haka ba, ba zai taba yin wannan aikin ba. Saboda haka ba wani kokwanto da zai yi saura kan sanadi wannan rauwayar.[14]
Mafificiyar hanyar kafa hujja da wannan ruwayar – bisa abin da muka yi la’akari da shi a cikin shashin ruwayoyin malamai wadanda suka gabata – shi ne kamar haka:-
Iamam (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya fadi jimloli duga biyu “hakika su hujja ta ne a kan ku” da kuma “ni huujjar Allah ne a kan su” wannan a sarari yana nuni ya zuwa kasancewar ruwayar su hujja ce- kuma wadannan bayain Allah su ne fakihai kamar yadda aka ambata a a baya a yayin bayyana ma’anar fakihai- daidai wa daida kamar yadda shi ma yake hujja ne shi, wannan na nufin cewa malamai za su gaji imam ( Allah ya gaggauta bayyanar sa) kuma la’akari da lokacin da wannan wasikar ta zo a cikin sa – ma’ana lokacin fakuwar gajeren lokaci- da kuma dubawa ya zuwa cewa imam ya kasance yana tarbiyantar mutane da kintsa su domin – abin da ke gaban sa - na fakuwar dogon lokaci a yayin da ya kasance yana ba su umarni kuma yana yi musu wasiyyoyi na karshe, kuma yana zartar da hukunce-hukunce na karshe, hakika ita ma kanta wanna ruwayar tana yin nuni zuwa doguwar fakuwa kuma kamar yadda malamai da dama suka bayyana cewa wannan ruwayar na nuni ya cewa fikohai hallifofin kuma wakilan imam ne a fagage mabanbanta wanda gudanar da lamarin jama’ar musulmi ke ciki.
Wasu sun tattauna kan manuniyar wannan hadisin kuma sun yi maganganu kan kafa hujja da shi, kuma lamari ne da muka sami shi a cikin da yawa daga maganganunu fakihai sai dai ba wanda ya kai ga gano wannan sakamakon sai Muhakkikun Naraki – kuma ya kara da cewa hakika wannan ya faru ne saboda rashin bibiyar da karantar ma’anar hujja da kuma rashin samun cikakkiyar kwarewa a cikin ilimin yare ko harshe sannan sai ya yi bahasi kan yadda da kuma inda ake yin amfani da kalmar “hujja” a ilimin mandik da falsafa da usulul fiihi, sai ya kai ga sakamakon da ba yadda za a iya fita daga gare shi.[15]
Abin da ake nufi da hujja a wanna ruwayar kamar yadda yake a wanin ta na daga ruwayoyi ita ce abin da za a iya kafa hujja[16] da shi. Lalle imam (amincin Allah ya tabbata a gare shi) hujjar Allah ne domin idan ya yi umarni da wani abu mutane suka ki bin umarnin, to Allah madaukakin sarki zai kafawa mutane hujja da maganar (umarnin) imami kuma a wannan halin ba su da wani uzuri da za su gabatar a gaban Allah ta’ala kan saba umarni sa da suka yi. Idan kuma suka aikata a bin da imam ya ce su yi sai aka tambaye su me ya sa kuka yi?
Ya isar musu su su bada amasa da cewa imami ne ya sa mu, saboda haka kasancewar fakihi hujja imami ne shi, na nufin cewa idan ya bada wani umarni – daidai ne fatawa ce ko fitar da hukunci ne ko kuma bta bangaren jagoranci da zartar da hukunci – sai mutane suka saba masa to da sannu imam (amincin Allah ya tabbata a gare shi) zai kafa musu hujja da umarnin fakihi (malami masani) .
kamar yadda wadanda suka bi umarnin za su ce dalili kan hakan shi ne umarnin da ya zo daga malami, a bisa ko wane hali , kamar yadda muka samu a cikin da yawa daga rubuce-rubucen malamai magabata cewa baba wani kwarzanon kokwanto bisa nuni wannan ruwaya kan shugabanci da jagorancin lamami da kuma wakilcin sa ga imami ma’sumi (amincin Allah ya tabbata a gare shi).
Domin Karin Bayani Ka Koma Wa
- Mahdi hadawi daharani wilayat wa diyanat “al waliya wad diyana” mu’assatu farhang khane dar “mu’assatu darul akali al sakafiyya” Kum bugu na 2 1380, hijiri shamsi.
- Mahdi hadawi daharani , a cikin alhukumul islami fi asril gaiba.
[1] Ka duba Saduk, da man la yahdhuruhul fakih, juzi’I na 4 shafi na 420 (babaun nawadir hadisi na 5919), assuduk, kitabul aamali, shafi na 109 (majlisi 34 hadisi na 4); asSaduk a cikin uyunu akhbaru rudha alaihis salam juzui na 2 shafi na 37 hadisi na 94. AsSaduk ma’anil akhbar juzu’I na 2 shafi na 374 babina 423, al hurrul amuli a cikin wasa’ilush shi’a juzu’I na 18 shafi na 65-66 a cikin (littafin kadha’I da da kuama siffofin alkalibabai na 8 hadisai na 50- 53); marigayi nuri a cikin mustadrakul wasa’il (littafin hukunci babobin siffar alkali babi na 8 hadisai na 10-11.48.52) allama majliisi a cikin biharul anwar juzu’I na 20 shafi na 25 (kitabul ilmi babi na 9 hadisi na 83); alhindi a cikin kanzul ummal juzu’I na 10 shafi na 229 (littafin al ilmu min kismil akwali , babi a 3 hadisi na 29209).
[2] Ana kiran wannan da idlakin da ya tsayu a kan shafe kk gore ko hazafin wanda hukuncin ya rataya a kan sa domin neman karin bayani ka duba Imam khomaini a cikin kitabul bai’I juzu’I na 2 shafi na 468. Da kuma assayi kazin ha’iri a cikin asaul hukumatul islamiyya shafi na 150, da muntazari a cikinlittafin sa wulayatul fakih juzu’I na 1 shafi na 463.
[3] Ka guba mahdi alha’irim a ciki hikimat wa hukumat shafi na 186- 187 (tare da yin tasarrufi a acikin maganar).
[4] Surar bakara aya ta 30.
[5] Surar sad, aya ta 26.
[6] “al idlaku” shi ne kin iyakancewa ko kebancewa a ainihin lamari na musamman.
[7] Ta kasance ruwaya c eta rubutun hannu da take danganewa da wakilan imama Mahdi ( Allah ya gaggauta bayyanar sa) Allah ya gaggauta bayyanarsa, a lokacin fakuwa kuma ana kiranta da (tauki’i).
[8] AsSaduk a cikin littafin kamalud din juzu’I na 2 shafi an 483, babi na 45 (attauki’at) (tauki’I na hudu).
[9] Shuhud Dusi a cikin littafimsa alkaiba shafi na 177.
[10] Ka duba Alhurrul amuli a cikin wasa’ilush shi’a juzu’I na 18 shafi na 101 ( littafin hukunci babobin sifffir alkali, babi na 11 hadisi na 9.
[11] (Nagartarwa) a cikin ilimin marawaita hadisi na nufin cewa marawaicin managarci ne za a iya dogara da ruwayar sa.
[12] Ka duba tastari, kamusur rijal juzu’I na 1 shafi ma 786.
[13] Wannan maganar ta zo a cikin littafin tahrirul makal a cikin kulliyatu ilmir rijal ala wasakatil amah. (ka duba mahadi hadawi daharani sikin tahrirul makal a cikin kulliyatu ilmir rijal shafi na 109-111).
[14] Ka duba sayyid kazim alha’iri a cikin littafin walayatul amri fi iasaril gaiba shafi na 122-125.
[15] Ka duba mahdi al ha’iri a; yazdi a cikin hikmat wa hukumat shafi na 207-214.
[16] “al ihtijaj” yana nifi kafa dalili da kuma tsa da hujja a kan wani abu da ake da’awa.