A zamanin boyuwar Imam Mahadi (a.s) "jagorancin malami" wani asasi ne tabbatacce kuma doka gama gari ta duniya wacce take daga tsarin siyasar musulunci, kuma matsayin malami dole ne ya kasance a matsayin jagora a matsayin shugaba mai yanke hukunci da bayar da umarni kuma ya kasance sama da duk wani mai gudanarwa a kasa.
Idan dai akwai wani tsari[1] da shiri na siyasar musulunci da za a yi magana kansa, to daya daga cikin asasin tsarin shi ne jagorancin malami a lokacin boyuwar Imamai ma'asumai (a.s). kamar yadda tabbatar jagorancin Imami (a.s) yana nufin jagorancin halitta da shari'ar ubangiji madaukaki ko kuma mu ce jagorancin imamai ma'asumai (a.s) wanda ya samo asali daga jagorancin cikamakon annabawa manzon rahama Muhammad (s.a.w) zuwa ga wasiyyansa har zuwa wasiyyin karshe Imam Mahadi (a.s), a matsayin wani tunani da yake jigo a cikin tsarin siyasar musulunci.
Don haka ne idan dai zamu karbi jagorancin malai to wannan wani abu ne da ya samu asali daga asasi tabbatacce na duniya gama gari a siyasar musulunci, wanda duk ko yadda wannan shakalolin wannan tsarin zasu bambanta a waje da yanayoyin siyasa, to wannan lamarin na "jagorancin malami" zai kasance yana tare da kowane lamari daga cikinsu, kuma babu wani abu da zai girgiza shi, kuma shakalolin hukumomi da kawai zai kasance wani abu karbabbe a musulunci shi ne wanda a cikin tsarinas ya kasance a zamanin boyuwar Imami (a.s) ya zamnto malami ne a matsayin saman wannan tsarin a matsayin wuka da nama wurin zartarwa, kuma yana saman duk wani mai gudanarwa a kasa.
Karin bayani:
1. Mahdi Hadawi Tehrani, Wilayat wa Diyanat, Mu'assar Al'adun Khaneye Khirad, Kum, bugu na biyu, 1380.