Akan ayar da aka yi tambaya a kan ta, akwai bayanai da mahanga da ra'ayoyi da dama da aikiyi bayani a kai sai mu za mu yi nuni ne da wasu kawai.
1. abun nufi da mabiya Isa, su ne mutanen manzon Allah akwai mahanga ukku dan gane da wannan ra'ayin
A. saboda ta bangaren zamani al'ummar manzon Allah ta zo ne bayan annabi Isa.
b. soboda annabin mu Muhammad (s.a.w) ya kasance mai gasgata isha ne da littafin sa duk wanda ya gasgata wani to ana ce ma sa mabiyin wane.
c. shari'ar annabin mu da sauran annabawa ta fuskar tauhidi wanda shi ne asali da tushen addini sun hadu kuri daya {wato kadaita Allah} saboda haka manzon Allah mai girma mabiyi ne gare shi {annabi Isa}
2. abun nufi da mabiya a cikin ayar su ne ma su bin gaskiya, su ne mabiyan da Allah ya yarda da su, saboda haka wannan jumlar da take cewa wadanda suka yi biyayya gare ka ta na nufin nasara ne kafin bayyanar musulunci da kuma musulmi bayan bayyanar musulunci wadanda suka dake cikin biyayya ga ga musulunci.
3. abun nufi da wannan ayar shi ne Allah madaukaki zai daukaka nasara akan yahudawa {idan muka lura da ayar afili za mu ga wannan tafsirin yafi da cewa da ita}.
4. abun nufi baki daya shi ne nasara da musulmi kuma ayar na so nu na mana cewa yahudu za su ci gaba da zama cikin kaskanci har ranar kiyama kuma dukkan wanda yai imani da annabci Isa (a.s) yana sama da su.
Amma me ya sa musulmi ba su cikin wadanda suka kafirce ma annabi Isa (a.s) saboda a nan kafirci yana nufi inkari kuma al'ummar yahudawa ne kadai suka yi inkarin annabi Isa (a.s) amma musulmi bacin ba su yi inkari ko karyata ko kafirce ma annabi Isa (a.s) sai ma dai mu ce mabiyan Isa (a.s) na gaskiya su ne musulmi wadanda suka ba da labarin tayar da manzon musulunci.
A wurin musulmi annabi Isa (a.s) yana cikin manyan annabawa kuma shi ne na ukku cikin ulu'lazam kuma ya zo da shari'a da littafi saboda haka don Allah madaukakin yana cewa mabiyan Isa (a.s) an daukaka su kan kafirai har zuwa ranar kiyama, to a gaskiya abun nufi da kafirai a nan ba zai zama musulmi ba saboda ba zai yiyu ba wannan Kalmar a dora ta kan musulmi ba.
Fasarar da a kayi a cikin tambayar baiyi dai dai da ayar ba, saboda haka kafin mu ba da amsa ya kama ta mu fasara ayar yanda ya dace:
Da wadanda suka bi ka Isa (a.s), mun daukaka su a kan wadanda suka kafirta har zuwa ranar kiyama sannan gare ni ku ke komawa sannan zanyi hukunci a tsakanin ku a kan abin da ku kayi sabani a kai[1].
Saboda samun amsa cikaka ya kama ta mu lura da wasu mas'aloli. A cikin bahasin za mu samu cikarka amsa.
Dan gane da ayar da a kayi tambaya a kanta, a kwai jawabai da mahangu masu yawa a kanta sai dai za mu yi nu ni da wasu ne kawai.
1. abun nufi da mabiya Isa (a.s) su ne al'ummar annabi Muhammad {s. a. a w} sai dai akwai mahanga ukku akan cewa al'ummar annabi Muhammad {s. a. a. w} su ne mabiyan annabi Isa (a.s).
A. saboda al'ummar annabi Muhammad sun zo ne bayan al'ummar Isa (a.s) wato ta fuskar zamani sun rigayi al'ummar manzon Allah. Inda za a ce wane mabiyin wane ne wato yana nufin ya zo ne bayan sa.
b.. soboda annabin mu {Muhammad s. a. w} ya kasance mai gasgata isha ne da littafin sa duk wanda ya gasgata wani to ana ce ma sa mabiyin wane ne.
c. shari'ar annabin mu da sauran annabawa ta fuskar tauhidi wanda shi ne asali da tushen addini sun hadu guri daya {wato ka daita Allah[2]} saboda haka manzon Allah mai girma mabiyi ne gare shi {annabi Isa}. Da ma'anar cewa yana da akida irin ta annabi Isa (a.s).
2.. abun nufi da mabiya a cikin ayar su ne ma su bin gaskiya, su ne mabiyan da Allah ya yarda da su, saboda haka wannan jumlar da take cewa wadanda suka yi biyayya gare ka ta na nufin nasara ne kafin bayyanar musulunci da share shari'ar Isa kuma suka tambata akan nasarancin da kuma musulmi bayan bayyanar musulunci wadanda suka dake cikin biyayya ga musulunci; saboda biyaiya ga musulunci yana nufin biyaiya ga gaskiya ne da ga karshe kuma biyaiya ga Isa[3] (a.s).
Allama taba taba'I yana danganta wannan mahangar ga wasu masu tafsirai kuma yana kore wannan mahangar[4].
3. abun nufi da wannan ayar shi ne Allah madaukaki zai daukaka nasara akan yahudawa [5] {wadanda suka kafirce ma Isa kuma suka kulla masa makirci} abun nufi shi ne Allah zai saukoma da al'ummar yahudu azaba kuma Allah madaukaki zai tsananta azaba akan su[6]. idan muka lura da ayar afili za mu ga wannan tafsirin yafi da cewa da ita, kuma wannan ayar tana cikin ayoyin mu'ujizozin da suke ba da labarin gaibi a cikin Kur’ani cewa mabiyan Isa kowane lokaci suna sama da yahudawa da suke sabani da shi.
A duniyar yau muna ganin wannan gaskiyar da idanun mu cewa yahudawan sahayoniya inda ba taimako da goyan bayan masihai ba dai dai da lokaci guda ba zasu iya ci gaba da rayuwar su ta siyasa da rayuwar yau da gobe ba[7].
Ta wannan mahangar abun nufi da mabiya annabi Isa (a.s), su ne nasara saboda kowane lokaci da kuma kowane waje yahudawa suna kasa da nasara kuma muna ganin hakan a kulun cewa yahudawa sai sun ne mi taimako a wajen nasara kuma mulki da hukumomi a yanzu suna hannu kasashe turawa yahudawa sun zama yan ka ka gida kuma haka zasu ci gaba da zama cikin kaskanci har zuwa ranar kiyama sannan kuma nasara za su ci gaba da zama saman yahudawa har karshen duniya[8].
4. abun nufi baki daya shi ne nasara da musulmi kuma ayar na so nu na mana cewa yahudu za su ci gaba da zama cikin kaskanci har ranar kiyama kuma dukkan wanda yai imani da annabci Isa(a.s) yana sama da su[9].
Amma za a iya lissafa musulmi a cikin wadanda suka kafirce ma annabi Isa (a.s) ?
Ma'anar kafiri shi ne wanda ke inkarin wani abu[10], amma musulmi ba wai suna karyata ko kuma suna inkarin annabi Isa (a.s) ba ne, sai ma dai sun dauke shi daya ne da ga cikin manyan annabawa kuma na ukku a cikin ulul'a azam kuma musulmi sana daukar annabi Isa a matsayin wanda ya zo da shari'a da kuma littafi. Allah madaukaki yana cewa: {na take Isa ya fara magana} ya ce: {ni bawan Allah ne ya kuma bani littafi daga sama ya kuma sani annabi [11]}
Amma al'ummar yahudawa sun kasance masu kiyayya da shi kuma daga karshe ma suka kasha shi.
Saboda haka don Allah madaukaki ya ce na daukaka mabiya Isa (a.s) saman kafirai har zuwa ranar kiyama to ma'anar kafirai a nan bayana nufin musulmi ba ne domin wannan Kalmar bata doruwa a kan musulmi.
Saboda haka jumlar {allazinattabauka} ta hada dukkan mabiya annabi Isa (a.s) saboda in muka lura da fassarar wannan ayar to za mu ga musulmi suma suna cikin mabiyan annabi Isa (a.s) saboda haka ayar ta hada musulmi da nasara ma'anar ayar shi ne mun dora wadanda suka bika {annabi Isa a. s} har zuwa rana kiyama saman wadanda suka kafirta, gareni zaku koma sannan zanyi maku hukunci tsakaninku akan abin da kukayi sabani a kai.
Daga karshe ya kamata mu yi ishara da wani abu, kamar haka. Idan mutum na kan hanyar gaskiya sai ya rika fuskantar matsaloli ko kuma ya dauki hanyar bata amma sai ya rika samun budi da ci gaba. Mahanga ta farko ita ce tafi wato mutum na kan gaskiya amma ya na fuskantar matsala a rayuwar sa kamar yadda imam hussain (a.s) ya kasance. Saboda haka idan muka tabbatar da gaskiyar musulunci amma domin ne man duniya ko mulki ya sa muka bar addini musulunci muka koma na nasara {kiristanci} hakan ya saba ma hankali kuma ya saba ma ayar Kur’ani mai girma kamar wadda ta zo cikin bakara aya ta 120.
[1] Fasarar ayatollah mukarim.
[2] Tabarasi fazil bin hussain, majamulbayan fi tafsir kur'an, masu fassara, jildi na 4, shafi na 94, yadawa ;intisharat farahani, tahran bugu na farko 1360 shamsi
[3]Taba taba'I, Muhammad Husain, tafsirin mizan, musawi hamadani, sayid Muhammad bakir, jildi na 3, shafi na 326 da kuma jildi na 3 shafi na 327, yadawa: ofishin yada musulunci na jami'e mudarisin hauze kom, kom, bugu na biyar, 1374 shamsi.
Taba taba'I, Muhammad Husain, tafsirin mizan, musawi hamadani, sayid Muhammad bakir, jildi na 3 shafi na 328-329[4]
[5] Tabarasi, fazil bin Hassan, majmulbayan fi tafsir kur'an, masu tarjama, jildi na 4 shafi na 94
[6] Jildi na 3 shafi na 330 Taba taba'I, Muhammad Husain, tafsirin mizan, musawi hamadani, sayid Muhammad bakir
[7] Mukarim shirazi, nasir, tafsirin namune jildi na 2, shafi na 570, yadawa :darulkitab islami, bugun tehran, 1374 shamsi.
[8] Tabarasi fazil bin Hassan, majmulbayan fi tafsirilkur'an, masu tarjama, jildi na 4, shafi na 94.
[9] Jildi na 3, shafi na 330. Taba taba'I, Muhammad Husain, tafsirin mizan, musawi hamadani, sayid Muhammad bakir
[10]Farhadi khalil bin ahmad, kitabulain, jildi na 5, shafi na 356, bugu na biyu, yadawa hijrat, kom 1410 k.
Maryam, 30[11]