Please Wait
Dubawa
5307
5307
Ranar Isar da Sako:
2013/10/09
Takaitacciyar Tambaya
Yiwa mace auren dole da hukuncin Dan da ta haifa.
SWALI
Idan aka yi wa mace auren dole ta hanyar tsorata ta da yi mata kashedi sai ta yarda da auren, bayan nan sai ta haifi da to shin auren na ta ya inganta? kuma shin Dan da ta Haifa na halal ne?
Amsa a Dunkule
A auren dole idan bayan an yi auren (ko da kuwa gwargwadon sakan ne) sai matar ta ji cewa ta yarda da auren to ya inganta, amma a ko wane hali Dan da ta ambata ba zai zama ba na shar’a ba, domin samun Karin bayani a komawa jigo mai numba 10338 (hukuncin yin auren dole da kuma Dan da aka Haifa) da kuma 37363 (Yarda da aure bayan an kulla aure da kuma ingancin auren)
Karin bayani:
Ga yanda amsoshin mar’aja’ai masu girma ta ke dangane da wannan mas’alar kamar haka:-
Mai daraja Ayatullah Sayyid Ali khamna’I (Allah ya tsawaita rayuwarsa).
Idan aka yi wa mace da namiji auren dole ko kuma daya daga cikinsu, bayan da aka gama Daura auren sai suka yarda da auren ko kuma suka faDa da bakin su cewa sun yarda to auren ya inganta.
Mai daraja Ayatullah Makarim Shirazi (Allah ya tsawaita rayuwarsa).
Auren dole baya inganta idan kuma ya tabbata cewa bayan auren ma bisa dole ake zama da juna to dan da aka samu ba shege ba ne.
Mai daraja Ayatullah Ali Sistani (Allah ya tsawaita rayuwarsa).
Idan bayan da aka yi auren mijin ko matar ta zartar da shi (ta hanyar nuna yardar ta) to auren ya inganta.
Mai daraja Ayatullah NUri Hmadani (Allah ya tsawaita rayuwarsa).
Idan a sarira bisa tilas ta yarda da auren kuma aka san cewa a zuciyarta ta yarda da auren ko kuma bayan da aka Daura ne ta nuna yardarta da auren, to ya inganta.

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga