advanced Search
Dubawa
44835
Ranar Isar da Sako: 2012/11/12
Takaitacciyar Tambaya
Yaya zan tuba daga kallon film mai batsa?
SWALI
Ni saurayi ne din shekaru 23 da na jarrabu da kallon fim din batsa shekaru masu yawa, kuma saboda samun satalite a gidanmu sai lamarin hakan ya yi sauki gare ni, don Allah ku taimaka mini da yadda zan tuba na daina kallon batsa?
Amsa a Dunkule
Sabo kamar wani jiki ne mai wari da duk sa'dda aka nutse cikin yin sa to sai mutum ya rika jin warinsa ya ragu sakamakon ya zama jikinsa, domin zai daina jin warinsa daga karshe ya dulmuye cikinsa sosai. Kuma idan mutum ya yi azamar komawa daga sabon komai nisan kuwa da ya yi to wannan lamarin ne babba. Kuma duk wanda ya samu kansa a wannan halin to ya yi kokarin karfafa wannan azamar tasa sosai don cimma wannan nasarar.
Marhalolin da zai kai ga cin nasarar yin mubaraza da sabonsa zamu yi nuni da wasu abubuwa da suka hada da:
1. Lura da abubuwan cutarwa da sabo yake da shi
2. Duba mutuncin kansa
3. Duba girman Allah madaukaki da kiyaye umarninsa
4. Duba kimar da take cikin tsarkake rai wurin gaba da sabo da son rai wanda yake wani lamari ne na cin nasarar rai.
Sannan kuma duk sai ya cike lokacin da ba ya komai da duba litattafai, motsa jiki, hardar Kur'ani, ibada, azumi da sauranibadoji don neman kusanci da Allah. Da watsar da duk wani abu da yake iya jawo masa yin sabon.
Babbar lamari a nan shi ne ka da mutum ya yanke kauna daga samun rahamar Allah ko barin dogaro da shi. Don haka ka da mu sake mu samu yin sanyi wurin yin tuba, don haka sai mu tashi mu yi mubaraza da yin sabo tare da kiyaye abubuwan da muka yi nuni da su a sama. Idan muka neman taimakon Allah da tausayinsa ne zai taimaka mana cikin samun nasarar wannan lamarin.
 
Amsa Dalla-dalla
Sabo kamar wani jiki ne mai wari da duk sa'dda aka nutse cikin yin sa to sai mutum ya rika jin warinsa ya ragu sakamakon ya zama jikinsa, domin zai daina jin warinsa daga karshe ya dulmuye cikinsa sosai. Kuma idan mutum ya yi azamar komawa daga sabon komai nisan kuwa da ya yi to wannan lamarin ne babba. Kuma duk wanda ya samu kansa a wannan halin to ya yi kokarin karfafa wannan azamar tasa sosai don cimma wannan nasarar.
Mu lura cewa fahimtar munin kallon wannan batsar kawai wani irin farkawa ce da da tausayawar Allah gare ka, kuma kokarin da kake yi na ganin ka bar wannan kallon shi ma wani kokari ne da rai take yi don cin galaba kan rai da munanan ayyukanta wanda yake nuni da kama hanyar tuba ga mutum wanda yake lamari mai kima matukar gaske.
Amma dole ne mu sani cewa tuba tana da wasu marhaloli kamar haka:
  1. Niyyar barin sabo
  2. Barin sabo
  3. Gyara halaye (maye gurbin munana da kyawawan halaye)
Kuma saboda ka kama hanyar neman tuba a matakin farko muna taya ka  murnar farkawa. Amma kai kuma dole ne ka gaugauta taka marhaloli na gaba, don haka sai ka tambayi kanka don me kake son barin sabo da watsar da shi gefe, don ka karfafi niyyarka. Ka sani idan ba ka karfafi azamar ka ba to ba zaka iya ci gaba ba. Imam Sadik (a.s) yana cewa: Aljanna an cakuda ta da wahala ne, amma wuta kuwa an cakuda ta da abubuwan jin dadin rai ne[1].
A nan zamu yi nuni da wasu lamurra masu sanya karfafa niyya da azama ga mutum mai son barin yin sabo kamar haka:
  1. Duba zuwa ga cutarwar da sabo yake yi wa mutum da maganin wannan, domin idan mutum ya  duba cutarwar abu to zai fi sanin hadarinsa sai ya guje shi.
  2. Duba kimar da mutum yake da ita, ya san cewa shi mutum ne halitta mai daraja, kuma yin sabo yana fado da matsayinsa kasa ne.
  3. Ya san cewa ubangijin da yake sabawa yana da matsayi mai girma kuma yana duba ayyukan da muke yi baki daya kuma zai yi mana hisabi kansu.
  4. Duba cewa a matsayinsa na saurayi da yake rayuwa a cikin al'umma to yana da wani tasiri mai kyau mai amfani da al'umma da zai yi wanda yake lamari ne mai yiwuwa kawai idan ya bar sabo.
  5. Ya san cewa lallai idan ubangiji ya hana bayinsa wani aiki to lallai wannan aikin yana da hatsari da cutuwa domin ubangiji mai tausayi ne ga bayinsa, don haka ba yadda zai hana wani abu mai amfani ga bayi.
  6. Ya sani cewa dadin sabo dan lokaci ne kawai, amma cutarwarsa mai dawwama ce tana nan har abada.
  7. Ya sani cewa yin sabo ba burgewa ne ba, burgewa ita ce mutum ya tsaya ya hana son ransa daga fadawa tarkon shedan.
  8. Sannan sai mutum ya nisanci duk wani abu da zai jawo masa kebewa shi kadai, da nisantar duk wani wuri ko wani abu da zai sanya shi yin sabo, sannan kuma duk sai ya cike lokacin da ba ya komai da duba litattafai, motsa jiki, hardar Kur'ani, ibada, azumi da sauranibadoji don neman kusanci da Allah. Da wakar da duk wani abu da yake iya jawo masa yin sabon.
Idan bai yi aure ba sai ya yi saurin yin aure domin biyan bukatar sa ta hanyar halal[2] domin samun abin da zai taimaka masa kawar da duk wani sabo[3].
Abokina ka sani yakar sabo yana tare da waswasin shedan da yawa, sai dai yana da matukar kima da jin dadin cin nasara kan shedan. Don haka ka yi kokari matuka ka karfafi azamarka ta barin sabo, kuma a kowane hali ne kake kana da wani karfi mai taimako shi ne Allah madaukaki mai tausayi da jin kai, don haka sai ka dogara gaer shi ka nemi taimakonsa.
Ka da ka yanke kauna daga rahamar Allah a kan wannan tafarkin, ka nemi taimakonsa ka dogara gare shi, zai taimaka maka in Allah ya so.
 

 [1] wasa'ilus Shi'a: j 15, sh 309, b 42.
[2] Muminun: 7.
[3] Saboda karin bayani sai a koma wa tambaya ta 326.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa