advanced Search
Dubawa
15064
Ranar Isar da Sako: 2007/03/17
Takaitacciyar Tambaya
mi ake nufi da makamta a ranar lahira?
SWALI
mi Allah madaukakin sarki yake nufi inda yake cewa: {mutanen da suke makafi a wannan duniyar makafi za a tashe su a ranar lahira}? shin mutumin da yake makaho a duniya ranar lahira ma zai zamo makaho wanda ba zai iya ganin komi ba?
Amsa a Dunkule

Abun nufi da makamta a cikin wannan ayar[i] da sauran ayoyi makamantanta[ii] ba shi ne rashin gani irin na duniya ba {wato mutun ya zamo bai gani da idanuwan da yake dasu} , sai dai abun nufi shi ne mutun da kan shi da kuma niyar kan shi yaki gani; wato duk da cewa mutun ya tabbatar da samuwar Allah subhanahu da kuma gaskiyar annabi sa mai tsira da aminci da kuma waliyin sa yarda Allah ta tabbata agare shi da iyalan shi amma cikin zuciya ya ki yin imani da su. Kamar cewa idamuwansa ba su ganin wannan gaskiyar. Ta yanda yake kin aiki ta addini kamar bai gani ko baijin abunda addinin ya ke cewa ballantana ya yi biyyaya, saboda haka bai son fadin gaskiya kuma bai son jin gaskiya kur'ani ya kira irin wadannan mutane makafi, kurame, marasaji {wadanka suka maida kansu haka da gangan}.

Ranar lahira ayukan mutun zasu bayyana a fili duk abunda mutun ya boye zai bayyana kuma akin shi zai zamo kamar jiki ta yadda za a rika ganin mutun da surar aikin sa kuma a yi masa hukunci da haka. Saboda haka makamtar da suka boye a zuciya zata bayyana da zamo masu abun azabtarwa, ranar da ayoyin Allah da kuma ni'imominsa da hasken muminai da ni'imar aljanna zasu bayyana amma ba zai samu damar ganinsu ba kuma ba zai samu ikon ganin hanyar zuwa ga aljanna ba. Sai dai bayan ya shiga jahannama domin a kara masa azaba sai abude idanuwan sa domin ya ga azabobin Allah daban daban, kamar yadda ya zamo a duniya ya rufe idanuwansa a kan gaskiya amma yana bude su a kan bata da barna. Don haka bawai zai zamo bai gani da idanuwa ba a a ranar kiyama kowa yana ganin abubuwan da ke boye kamar samuwar Allah madaukaki da wahayi da mala'iku da aljanna da jahannama, ganin na yakini ta yadda ba wanda zai iya karyatawa.

 


[i] Wanda ya kasance makaho a wannan duniya ranar lahira za a tashe shi makaho sun bace hanya, isra'I, 72.

[ii] Zamu tashe su ranar kiyama suna makafi, sai suce; ya ubangiji miyasa ka tashe mu makafi bayan mun kasance a duniya muna gani, taha, 124 zuwa 125.

 

Amsa Dalla-dalla

Halittar dan adam ta ginu ne akan abubuwa da dama wasu afili suke ta yadda za'a iya ganin su wasu kuma aboye suke ba yadda za'a iya ganin su irin wadannan sun shafi ruhin mutun ne; kamar yadda halittun fili suna taimakama gangar jiki ta hanyar jin dadi da kuma abunda jikin ke bugata {kamar yadda suke da irin wannan amfani a jikin dabbobi}. Hanyoyi ne na isar da sako zuwa ga zuciya da samar da ilimi da motsar da tausai da fushi, saboda haka suna tai makon mutun a cikin rayuwa shit a yau da gobe. Don haka da mutun zai yi amfani da wadannan ni'imomi na fili da aka yi masa musamman ji da gani ta hanya mai kyau wajan biyyaya ga Allah da daukaka mutuntaka sa, da zai iya zama mai ji {jin gaskiya} da kuma gani {ganin gaskiya} ba wai kawai gani na idanu ba da kuma ji na kunnuwa ba, amma in mutun baiyi amfani da wadannan ni'imomin bat a yadda ya dace ilimin da ya ji ya kuma gani dasu kuma yaki fadi da harshen sa ya zamo kamar kurma da makaho. Domin idanun sa da kunnuwan sa ba suyi masa anfanin da ya dace ba. Kuma wannan rashin amfani ba domin idanuwansa ko kunnuwansa na da matsala ba, sai dai domin mumunan zabin da ya yi ma kansa. ta rashin amfani da abunda ya ji kuma ya gani na gaskiya.

Ta haka ne mutun zai iya ganin dalilan da suke tabbatar da samuwar ubangiji da halittun shi da rahamar shi da inayar shi amma yaki imani da Allah;yana ganin abubuwan da suke tabbatar da gaskiyar annabi mai tsira da aminci da iyalain sa da mu'ujizojin shi, amma yaki gaskata shi, kuma yana jin bayanan manzon Allah da hadisai shi dan gane da waliyin shi mai aminci {aliyu bin abi talib (a.s) } da kuma falaloni shi waliyin da karamomin shi, amma sai yai inkarin su ya kuma kore samuwar waliyin ya kuma gi yin biyayya ga waliyin ya dauki gaba da shi {waliyin} duk da tunatarwar da Allah ma daukakin sarki yake yi {ta hanyar kur'ani} da kuma gargadin da manzon Allah mai tsira da aminci da yayan gidan shi da kuma gaskiyar su da ayoyin ta ke tabbatar da kiyama, amma sai yai inkarin samuwar rayuwar lahira da aljanna da jahannama {wuta}. Duk mutumin da tsawon rayuwar sa ta zamo haka wato ya rufe idanuwan sa daga mutuntaka da ma'anawiya kuma yaki yin amfani dasu wajen bauta ma Allah da biyayya ga ma aikinsa mai tsira da aminci da waliyin sa mai aminci. Tabbas a ranar lahira lokacin da ayukan mutun suke bayyana zu zoma tamkar gangar jiki domin karbar sakamako mai kyau ko mara kyau, sai Allah madaukakin sarki ya hana shi ganin girma da jalala ta ubangiji da fuskar mai haske ta annabin sa mai tsira da aminci da kuma waliyyan Allah da muminai ya kuma haramta mai ganin ni'imomin sa wato aljanna. Ya kuma kora shi zuwa ga wutar jahannama kamar yadda a duniya ya makamtar da zuciyar shi ya kuma toshe ma kan sa hanyar zuwa ga sa'ada, a ranar lahira ma haka zai tashi wato makaho ta yadda ba zai iya gani hanyar zuwa aljanna ba.

Acikin kur'ani mai girama ya zo cewa wadannan abubuwan suna kawo makamta a ranar kiyama gasu kamar haka.

Kin biyayya ga Allah mai girma da daukaka, son duniya, da kuma bautawa zuciya[1] sai kuma taurin kai da neman dalili mara sa tushe a cikin al'amuran da suka shafi addini[2], manta lahira da kuma rashin imani da samuwar ta[3], hana mutane zuwa ga karbar gaskiya, da kuma danganta karya zuwa ga Allah[4] karyata ayoyin Allah da kuma kin gasgata annabin sa mai tsira da aminci da yayan gidan sa[5], yanke zumunci {kin yarda da wulayar waliyin Allah} sabo da shishigi da wuce gona da iri[6].

Acikin ruwaya ya zo wadannan abubuwan sune hakikanin makamta da kin ganin gaskiya, gasu kamar haka, rufe wulaya Ali bin abi talib (a.s) kin yarda da cewa imam Ali (a.s) shi ne khalifan manzon Allah bayan sa, da kuma wanda yaki zuwa aikin hajji bayan Allah ya bashi damar yin hakan har yabar duniya[7].

Makamta a ranar lahira ba yana nufin mutun ba zai iya ganin komi ba, kamar yadda ya kasance a duniya {bai iya ganin komi}. Sai dai zai iya fahimar makamtar shi a ranar mahashar ya gane cewa nan filin ba irin na duniya ba ne acan yana da idanu amma anan bai da su. Saboda haka sai ya fara tsogumi da jayayya kamar yadda dama aikin shi ke nan a duniya[8].

Amma kamar yadda yake a zahirin kur'ani da wani bangare na ruwayoyi da kuma bincike na masu tafsiri yana nunawa cewa kiyama ta na da mataki daban daban har zuwa lakacin da yan aljanna zasu shiga aljanna yan wuta kuma su shiga wuta; domin haka makamtar wadannan gunkiyar ya shafi mataki mahashar ne, wato kafin su shiga wuta, domin su haramta daga ganin jalalar ubangiji da ta bayin sa, sai bayan sun shiga jahannama sannan idanuwan su zasu bude, domin suyi hasara na rashin ganin ni'imomin ubangiji da waliyan sa masu daraja, kuma suka watu da yan wuta domin su sha azabar malinkiya.

Wasu masana sun dauka cewa {wanda yake a duniya makaho a lahira zai tashi makaho} makamtar jiki ake nufi, wato wadanda suke makafi a duniya komi sani da iliminsu, ranar lahira makafi za a tashe su. Alhali ba haka ayar ke nufi ba, abun nufi da {a cikin ta makafi} shi ne makamtar zuciya a rayuwar duniya kuma abun nufi da {aranar lahira za a tashe su makafi} makamtar zahiri da bayyanar ayyukan su a fuskokin su domin su dan dani azaba. Kamar yadda mu ka yi nuni a baya makamta iyakarta a filin mahashar ne da zarar sun shiga wuta idanuwan su za su bude domin suka munanan ayukan su da kuma azabobi daban daban. Kamar yadda ya kasance yana yi a duniya wato yana mai rufe ido daga ayoyin Allah da waliyan sa masu daraja kuma a lokaci guda yana bude idanun sa zuwa ga abun duniya da abokan sabon sa. {Allah ya tsare mu daga sharrin zukatan mu}.

Sunaye na littafan daka yi amfani da su domin bada amsa wato masdarori.

1} javadi amuli, abdullahi, fitira a cikin kur'ani, jildi na 12, isra'I, qom, bugu na biyu, 1379, shafi na 97 zuwa 104 da kuma 139 zuwa 140.

2} javadi amuli, abdullahi, ma'arifat shinasi a cikin kur'ani {ilimi sani a ciki kur'ani} jildi na 13, isra'I, qom bugu na biyu, 1371, shafi na 357 zuwa 362.

3} tabataba'I, sayyid Muhammad Hussain, almizan {da harshen farisanci} ofishin yadawa na musulunci, qom, jildi na 13, shafi na 232 zuwa 233 da kuma jildi na 14, shafi na 314 zuwa 316.

4} tabataba'I, sayyid Muhammad Hussain, tibulbayan, jildi na 8 masaidar da littafai ta musulunci, Tehran, bugu na biyu, shafi na 287 zuwa na 388.

5} kara'ati, muhsin, tafsirin nur, zuwa ga gaskiya, qom, bugu na daya, 1374

6} qumi mashhadi, Muhammad dan Muhammad riza, kanzildakayik, mu'assasar bugawa da yadawa, Tehran, bugu na daya, 1411 hijra, jildi na 7 shafi na 463 da kuma na 523 zuwa na 524 sai kuma jildi na 8 shafi na 368 zuwa 371.

7} makarim, nasir, tafsirin namune, darulislamiya, Tehran, bugu na sha bakwai, 1374.

 


[1] Taha, 124 da kuma 127 da kuma isra'I, 72 zuwa 97.

[2] Fussilat, 17

[3] Namli, 66.

[4] Hud, 18 zuwa 28

[5] An'am, 4 zuwa 5 a araf, 64, bakara, 17 zuwa 18

[6] Muhammad, 22 zuwa 23.

[7] Tibbulbayan, jildi na 18, shafi na 287 zuwa na 288, almizan, jildi na 4, shafi na 314, kanzil dagayik, jildi na 7, shafi na 523 zuwa na 524 da kuma 456 zuwa 462 da kuma jilidi na 8, shafi na 368 zuwa na 371.

[8] Taha, 124 zuwa 127.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa