Please Wait
Dubawa
36882
36882
Ranar Isar da Sako:
2017/05/22
Takaitacciyar Tambaya
Shin zai yiyu a sami alaKa tsakanin Mutum da Aljani?.
SWALI
Shin zai yiyu Dan’adam ya yi akaKa da aljani? Idan har zai yiyu, ya hukuncin yin haka yake?
Amsa a Dunkule
Kur'ani mai girma ya tabbatar da samuwar aljani kuma ga wasu daga cikin bayanai kan aljani.
1- Aljani halittace da aka yi shi da wuta saBanin mutum shi da kasa aka halicce shi.[1]
2- Yana da ilimi da idraki da tantance Karya daga gaskiya, yana iya yin magana kuma yana kafa dalili.[2]
3- An wajabta masa ayyuka (na ibada da dss) da kuma nauyaye nauyaye.[3]
4- Wasu daga cikin su muminai ne salihai wasu kuma kafirai.[4]
5- Za a tashe su ranar alkiyama kuwa za a yi musu hisabi.[5]
6- Suna iya keta sararin samaniya su sato ji amma daga baya an hana su.[6]
7- Suna kulla alaka da wasu daga cikin mutane kuma suna yin amfani da masaniyar da suke da ita na wasu Boyayyaun sirrika su halakar da mutane.[7]
8- A cikin su akwai waDanda suke da karfin da iko na gaske kamar yadda ake samu a cikin mutane.[8]
9- Suna da ikon yin wasu ayyuka da mutane ke bukatuwa zuwa gare su[9].
10- Su aka fara halitta a doron kasa kafin ahalicci mutane[10].
11- A cikin Kissar Annabi sulaiman (as) lokacin da Ifritu daga cikin aljanu ya yi da’awar cewa zai iya kawo gadon BilKisu wajen Annabi Sulaiman (as) kafin ya tashi daga mazauninsa[11], Annabi Sulaiman (as) bai Karyata shi ba duk da cewa wannan maganar ba ta zo a cikin Kur'ani ba cewa ya kawo gadon ba[12].
Daga cikin abin da aka amabata a cikin yoyiyn da muka kawo zamu fahimci cewa aljanni ba halitta ce irin ta tatsuniya da labara ba, shi halitta ne samamme a haKiKa, mai jiki wanda za a iya yin alaKa da shi, kuma wasu daga cikin mutane sun yi alaKa da shi, duk da cewa a zamanin da an fadi wasu nau’o’i na alaka daban daban tsakanin mutane da aljani, amma mu zamu takaitu da irin wacce muka samu a cikin Kur'ani da hadisi, da ita zamu isu don wannan kawai muka yarda da shi.
A nan za mu yi nuni zuwa ga yanayin alaKar da muka samu a cikin Kur'ani da ruwayoyi da kuma maganganun da aka naKalto daga wasu maKiya:
A. Neman tsarin Allah daga aljanai; ya zo a Kur'ani mai girma cewa: {haKiKa wasu mazaje daga mutane sun kasance suna neman tsari wajen wasu mazaje daga aljanu sai suka kara jefa su cikin bala’i da “wahala”}[13].
Al’adar larabawa ta kasance duk lokacin da suka shiga daji mai ban tsoro (misali mai duhuwa) suna neman tsari daga aljanun wannan kwazazzabon, kuma musulunci bai hana yin haka ba kuma ya yi umarni da a nemi tsari daga shaiDanun mutane da na aljan[14].
B. Tasarrufi da aljani; yin tasarrufi da aljani da yin amfani da su wajen yin hidima duk da cewa abu ne mai yiyuwa, sai dai malamai sun yi bahasi kan cewa shi ya halatta ko kuwa? Gwargwadon abin da suka yarda da shi, shi ne lalle ne kar wannan aikin ya zama ta hanyar da shari’a ta haramta, ko kuma ya zama sanadin cutuwar aljanu. Kuma lalle ne ya zama aikin da suke yi ba wanda shari’a ta haramta ba ne. kuma lalle yin aikin da shari’a ba ta yarda da shi ba ya haramta daidai ne da wasiDa ko babu wasiDa.[15]
An tambayi Marja’I Mai girma Sayyid Ali (as) Khamna’i kan hukuncin zuwa wajen mutanen da ke tasarrufi da rauhanai da aljanu wajen yi wa mutane magani tare da la’akari da cewa bisa yaKini su aikin alkhairi kawai suke yi, sai ya bada amsa da cewa: wannan aikin ba shi da mushkila a kan kansa da sharaDin cewa ya zama yana yin aiki ta hanyar da shari’a ta halatta[16].
Domin samun Karin bayani a komawa jigogi masu zuwa:-
1. Abin da sheDan a aljani suke iya yi, tambaya ta 883.
2. SheDan mala’ika ne ko aljani? Tambaya ta 857.
3. Littafin aljani da sheDan na Ali Ridha, Tehrani. wanda aka yi tahKiKinsa a mahanga ta Kur’ni da ruwaya da hankali da ilimin rijalu (mazajen hadisi).

[1] Surar rahaman aya 15.
[2] Ayoyi mabanbanta a cikin surar Jinni.
[3] Ayoyi mabanbanta a cikin surar Jinni da Rahaman.
[4] Ayoyi mabanbanta a cikin surar Jinni da Rahaman.
[5] Adreshin da ya gabata 15.
[6] Adreshin da ya gabata 9.
[7] Adreshin da ya gabata 6.
[8] Surar Namli aya 39.
[9] Surar Saba’i aya ta 12 da 13.
[10] Surar Hijiri aya ta 27.
[11] Surar Tururuwa aya ta 30 – 40.
[12] Jawadi Amuli Abdullah a cikin tafsirul maudhu’I j1 shafi 119.
[13] Surar Jinni aya ta 6.
[14] Biharul Anwar j 92 shafi 148 (almahasin) Manzo (saw) ya ce: “Idan masihirtan aljanu su ka motsa, ku kare sharrinsu da kiran salla”.
[15] Mihajus Salihin na sayyid khu’I j 2 shafi na 8.
[16] Taudhihul masa’il (mai hashiya na Imam khomaini) j 2 shafi 980, 1232.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga