advanced Search
Dubawa
12819
Ranar Isar da Sako: 2012/04/16
Takaitacciyar Tambaya
Mene ne Dalilin wilayar Ma'asumai (a.s)?
SWALI
Mene ne Dalilin wilayar Ma'asumai (a.s)?
Amsa a Dunkule

Ana iya tabbatar da Wilaya da jagorancin ma'asumai (a.s) a cikin madogarar dalilai hudu na shari'a da ya hada da Littafi, Sunna, Hankali, Ijma'.

Dukkan malaman Shi'a kalmarsu da maganarsu ta hadu gaba daya ba ma tare da koma wa maganganunsu ba, kai hatta da masana da malaman sauran mazhabobi sun tabbatar da cewa malaman Shi'a gaba daya sun tafi a kan wajabin biyayya ga jagorancin Ahlul-baiti (a.s).

A game da dalilin hankali, wasu malamai sun yi amfani da dokar nan ta "Ludufin Allah" don tabbatar da wannan lamarin na jagorancin Ahlul-baiti (a.s) ga al'umma da suke ganin dalili ne da ya wadatar, sai dai wasu suna ganin bai wadatar ba, don haka ne suka kara da dalilin "Hikimar Allah".

Ayoyin Kur'ani mai daraja da yawa ne suka zo domin tabbatar da annabtar annabi (s.a.w), da tayiwu wacce ta fi kowacce bayyana karara ita ce ayar nan ta "Annabi shi ne ya fi cancanta ga muminai fiye da kawukansu".

Haka nan ruwayoyi masu yawa ne suak zo game da jagorancin imamai (a.s), daga cikinsu akwai maganar Imam Ja'afar Sadik (a.s) da ya fada karkashin tafsirin wannan ayar mai cewa: "Kawai majibancin lamarinku shi ne Allah da manzonsa da muminai…" sai ya ce:

Cewa abin da wannan ayar take nufi shi ne cewa mafiya cancanta da ku, mafiya hakki a kanku da al'amuranku da kawukanku, da dukiyoyinku, su ne; Allah da manzonsa, da wadanda suka yi imani, da yake nufin Ali (a.s) da 'ya'yansa har zuwa ranar kiyama.

Amsa Dalla-dalla

A cikin al'adun musulunci bayan fuskantar cewa akwai wajabcin samun jagora ba kowane yake da wannan hakkin na jagoranci ba sai ubangiji madaukaki wanda dukkaln hakkin sha'anoni da lamurran mutane suna hannunsa, kuma don haka haka ne ma ya sanya dole ne a kan mutum ya yi biyayya ga umarninsa da kuma nisantar haninsa[1]. Don haka da zai kira shi domin yin biyayya ga wani mutum ko wasu mutane to dole ne mu yi biyayya ga wannan, haka ma idan ya yi bayanin wasu sharuda ya ayyana cewa wanda ya cika wadannan sharudan yana da hakkin yi masa biyayya to dole ne mu bi duk wanda ya ci wannan sharadin.

Musulmi mun yi imani da cewa wannan jagorancin ubangiji madaukaki ya ba wa manzon Allah (s.a.w) shi, kuma bayan manzon Allah (s.a.w) sai ya ba wa imamai ma'asumai daga tsatson manzon Allah (s.a.w) wannan hakkin na biyayya garesu bisa mahangar mabiyansu, kuma za a iya tabbatar da wannan lamarin da dalilai guda hudu da suka hada da: Kur'ani, Sunna, Hankali, da Ijma'i.

Ijma'in malamai ya bayyana a fili ta yadda idan mun koma maganganunsu babu bukatar bayani, domin ya bayyana ta yadda hatta da sauran masanan sauran mazhabobi ba su da wani kokwanto a kai. Ta yadda imamanci ya kasance daya daga cikin asasin addini gun Shi'a, ta yadda bayan wucewar manzon Allah (s.a.w) kai tsaye Imamai daga zuriyar manzon Allah (s.a.w) zasu kasance su ne jagorori kai tsaye.

Don haka ne Shi'a suka yi imani da cewa manzon Allah (s.a.w) bayan matsayin annabta da manzanci da yake da shi, haka nan yana da matsayin imamanci[2]. Shi matsayin imamanci wani matsayi ne na sanin sirrin ubangiji a duniyar halitta da shari'a, sai dai da matsayin manzanci ne annabi yake samun umarnin isar da abin da ya sani zuwa ga mutane kuma ya shiryar da su. Matsayin imamanci matsayi ne na jagorancin al'umma da tafiyar da lamurransu.

A hankalce kuwa; wasu sun yi riko da ka'idar nan ta "Ludufin Allah" domin tabbatar da imamanci, kuma sun yi amfani da wannan a matsayin dalilin cewa annabi (s.a.w) shi ne mai tafiyar da lamurran al'umma. Wannan dalilin kuwa wasu ba su yarda ya isa ba, suna ganin dalili ne, sai dai yana bukatar karfafa shi da "Dalilin Hikima"[3].

Muna iya yin bayanin Dalilin Hikima a takaice da cewa:

Bayan tabbatar da samuwar Allah madaukaki, da duniyar halitta mai jiki, da makoma alkiyama ga mutum, to muna iya tabbata da cewa duk wani abu da yake wannan duniya da yake faruwa daga mutum yana iya tabbata ya dawwama har abada a lahirarsa sai dai hankali da kansa yakan kasa ya gaza wurin tabbatar da samwuar wannan tasirin. Don haka hikimar Allah madaukaki a wannan halittar tasa da halittar dan Adam ta hukunta cewa lallai ne ya tanadar wa mutm hanyar rayuwar mai sa'ada da arzuta, kuma ya aiko musu wani dan aike daga mutane. Ta wani hangen kwa domin cimma hadafin aiko manzonni wanda shi ne hadafin shiryar da mutane ya zama dole ne su wadanann annabawan su kasance ma'asumai kuma ba sa kuskure wurin karbar sakon Allah da isar da shi ga mutane. Sannan da bayanin hankali zamu iya cewa ismar karbar sako da isar da shi da kuma isma daga kuskure da rafkanwa a dukkan sha'anonin rayuwa suna da alaka sosai.

Don haka manzon Allah dole ne ya kasance ma'asumi a kowane fage, a nan ne hankali zai yi hukunci da cewa hikimar Allah ta hukunta sanya irin wannan mutumin a matsayin jagoran al'umma, don haka dole ne manzo mai jagorantar al'umma ya kasance ta fuskacin addini yake. Idan hankali ya fuskanci wannan mas'ala ta imamanci, zata ga Imami a matsayin mai fassara sakon Allah ne ta hanyar da dalilinta yake kama da na farko. Don haka hankali yana hukunci da isma ga manzo da Imami a bisa hikimar Allah da cewa dole ne su kasance su ne masu tafiyar da lamurran al'umma, kuma da haka zamu ga cewa ma'anar wilaya yana nufin jagorancin al'umma da tafiyar da lamarinsu. Kuma da wannan zai zama mun tabbatar da wannan jagorancin ta Dalilin Hikima.

Akwai ayoyi masu yawa da suka zo game da tabbatar da jagorancin annabawa[4] wacce mafi bayyana a cikinsu ita ce wannan ayar mai girma: "Annabi shi ya fi cancanta da muminai daga kawukansu"[5]. Wacce ma'anarta take tabbatar da wilaya da jagoranci ga annabi mai daraja a kan dukkan muminai idan an kwatanta da kawukansu. Wato idan da zasu iya daukar wani matakin yin wani abu da kawukansu, to annabi (s.a.w) shi ne ya fi cancanta ya dauki mataki kan mutane kuma ya ba su umarni su bi cikin dukkan lamurransu. Kuma su ba su da hakkin su sabawa don haka dole ne su yi biyayya, abin ya shafi lamarinsu na daidaiku, ko ya shafi lamarinsu ne na jama'a[6]. Kuma wannan ma yana tabbatar da jagoranci (wilaya) gamammiya ta annabin rahama (s.a.w) a fagen halal din shari'a da rayuwar al'umma domin a wadannan fagage ne zasu iya daukar matakin rayuwarsu.

Annabi mai girma (s.a.w) ya yi nuni da wannan a cikin wata ruwaya mutawatira a kissar Gadir yana mai nuni da wannan ayar yayin da yake bayani ga mutane cewa: "Shin ba ni ne na fi cancanta ga muminai ba fiye da kawukansu"? kuma bayan mutane sun yarda da hakan sai ya ce: "To duk wanda nake jagoransa, Ali ma jagoransa ne"[7], don haka wilayar annabi (s.a.w) ita ce dai wilayar Ali da sauran imamai ma'asumai (a.s) ita ce dai wilayar annabi (s.a.w)[8].

Akwai kuma wata ayar mai nuni zuwa ga jagorancin manzon rahama da Imam Ali, wannan ayar mai daraja ita ce: "Kawai jagoranku shi ne Allah da manzonsa da wadanda suka yi imani suke tsayar da salla suek bayar da zakka alhalin suna masu ruku'u"[9].

A wannan ayar akwai abin da ya shafi akidar Shi'a game da imani da wilaya, ta fara da Allah madaukaki da kansa, sannan sai manzonsa, sannan kuma sai wadanda suka yi imani suka tsayr da salla suka yi sadaka alhalin suna cikin ruku'u. Duk da cewa wannan siffofin suna iya yiwuwa su dabbaku ga kowane mutum, sai dai furucin da masu ruwaya na Sunna da Shi'a suka yi kan wannan lamarin na saukar aya da cewa abin da ake nufi shi ne Ali (a.s)[10].

Wannan ta tabbatar da wilaya sake babu wani dabaibayi ga manzon Allah (s.a.w) da imamai ma'asumai (a.s).

Sannan akwai ruwayoyi masu yawa game da wilayar imamai ma'asumai (a.s) da muka yi nuni da wasu a cikin bahasinmu, mu a nan zamu kawo misali ne a fadin nan na Imam Ja'afar Sadik (a.s) da ya zo a bayan wannan ayar mai cewa: "Kawai jagoranku shi ne Allah da manzonsa da wadanda suka yi imani suke tsayar da salla suek bayar da zakka alhalin suna masu ruku'u". sai ya ce:

Abin da ake nufi da wannan shi ne; wanda ya fi cancanta da kawukanku, mafi hakkinku a kanku, da al'amuranku, da kawukanku, da dukiyoyinku, su ne Allah da manzonsa da wadanda suka yi imani, yana nufin Ali (a.s) da 'ya'yansa har zuwa ranar kiyama[11].

Mahdawi Hadawi Tehrani, Wilaya wa Diyanat, cibiyar al'adu, Gidan Khirad, Kum, Bugu na Biyu, 1380.

 

 

 


[1] R.K: Jawadi Amuli, Wilayatul Fakih (Rahbari dar Islam) shafi: 29.

[2] Abin da ake nufi da "imamanci" shi ne jagorancin al'ummar musulmi, sai dai a wasu wurare ana nufin jagorancin imamai ma'asumai daga tsatson annabi (s.a.w). Suna amfana daga ilimin Allah (s.a.w) kamar yadda annabawa suke. (R.K: Mahdi Ha'iri Yazdi, Hikmat ba Hukumat: shafi; 171)

[3] Sabanin wasu da suke ganin kawai Ka'idar Ludufin Allah ta wadatar ba tare da la'akari da shubuhohin da aka kawo karnoni masu yawa da suka gabata kamar na Fakhrur Razi- da suka yi tunanin kamar shi ne farkon wanda ya kawo suka game da wannan Ka'ida, kuma ya toshe kofar hankali da raddin wannan. (R.K: Mahdi Ha'iri Yazdi, Hikmat ba Hukumat: shafi; 173 - 176)

[4] R.K: Muntazari, Wilayatul Faki, J 1, shafi 37 – 73.

[5] Ahzab: 6.

[6] R.K: Sayyid Kazim Ha'iri, Wilayatul Amr fi Asril Gaiba, shafi 153; Muntazari, Wilayatul Fakih, j 1, shafi 37 – 40.

[7] R.K: Majlisi, Biharul anwar, j 37, shafi 108; Muntazari, Wilayatul Fakih, J 1, shafi 41.

[8] R.K: Sayyid Kazim Ha'iri, Wilayatul Amr fi Asril Gaiba, shafi 153.

[9] Ma'ida: 55.

[10] R.K: Suyudi, Durrul Mansur, j 2, shafi 293; Bahrani, Tafsirul Burhan, j 1, shafi 479. 

[11] Usulul Kafi, j 1, shafi 288.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa