Please Wait
50458
Abdulqadir Jilani da ake yi wa laqabi da gausul a’azam shi masani ne sufi da aka haife shi a arewacin iran a qarni na biyar, wanda ya mutu a bagdad a qarni na shida.
Amma alaqarsa da imam Sadiq (a.s) da savawarsa gare shi to tarihi yana qaryata wannan, domin tsakaninsu akwai tsawon zamani mai nisa, don haka abin da ake danganta masa na ya sava wa imam Sadiq (a.s) bai inganta ba.
Shi ne abdulqadir xan abi salih, musa xan abdullahi, xan yahaya jilani wanda ake yi wa laqabi da muhyiddin[1], an haife shi a arewacin iran, ya rayu a bagdad ya mutu a nan, kuma an binne shi a nan…[2], haqiqa ya zo a qamus xin bayanin malamai da mamaqa cewa shi nasabarsa tana tuqewa zuwa ga imam Hasan mujtaba (a.s) ne, wato yana daga sharifai hasanawa[3], kuma yana daga manyan arifan qarni na shida hijira, kuma shi yana daga cikin manya mutane da aka yi jayayya game da su a duniyar musulmi, kuma kabarinsa yana daga wuraren da suak shahara a bagdad, an haife shi a shekarar hijira 471, ya rasu a shekara ta 561, da shekarun da suak kusa casa’in[4].
Ya shiga bagdad a lokacin samartakarsa shekara ta 488 H[5]. sannan sai ya yi karatu a hannun abu zakariyya tabrizi a ilimin lugar larabci[6], da fiqhu da hadisi a hannun Ali xan Husain almakhrami albagdadi[7], sannan ya karvi hanyar xariqa gunsa[8].
Sannan an faxi cewa yana da talifofi a usul da furu’ da fiqihu da sufanci, daga ciki akwai basha’irul khairat, da algunya lixalibi xariqil haqqi, da gunyatux Xalib lixariqil haqqi, da fatahur rabbani fal faidhur rahmani, da futuhul gaib, da malfuzatun qadiriyya, da alfuyudhatur rabbaniyya fil auradil qadiriyya, da malfuzatu gilani, da adabus suluk wattawassul ila manazilil muluk, da diwan,; wanda yake waqa ce sananniya da aka sani da “diwanu gausul a’azam[9].
Ibn arabi ya ambace shi a littattafansa musamman a cikin futuhatul makiyya tare da girmamawa da xaukakawa.
Yana da kuma girma na musamman a cikin sufaye, kuma da yawa daga wasu qungiyoyin sufaye suna da’awar dangantuwa zuwa gare shi.
Daga qarshe muna nuni da tambayar alaqarsa da imam Sadiq (a.s) da savawarsa da cewa wannan qarya ce a tarihi domin tsawon zamanin da yake tsakaninsu yana da tsayi matuqa, don haka abin da ake danganta masa bai inganta ba.
[1] Lugat nameh dehkhuda, j 10, shams abad – Ali, s 15713, mu’assasar intisharat wa xab’I jami’atu Tehran, bugu na biyu daga daurar sabuwa, 1377.
[2] Majmu’atu aasari ustad shahid mutahhari, j 14, s 570, j 23, s 57.
[3] Lugat nameh dehkhuda, j 10, shams abad – Ali, s 15713.
[4] Muhammad ma’asum shirazi, xara’iqul haqa’iq, (tashih wa muqaddame Muhammad Ja'afar mahbubu) j 2, s 362, intisharate sinayi, bugu na biyu.
[5] Abdulqadir gilani, futuhul gaib, s 10, darul hadi maktabatu daruz Zahra, bairut, 1428 h q, 2007 m.
[6] Lugat nameh dehkhuda, j 10, shams abad – Ali, s 15713.
[7] Futuhul gaib, s 10.
[8] Xariqul haqa’iq, j 2, s 362.
[9] Lugat nameh dehkhuda, j 10, shams abad – Ali, s 15713.