Please Wait
11908
Kalmar Wali da larabci tana da ma'ana guda uku: 1-masoyi, 2-aboki, 3-mataimaki. Bayan haka akwai wasu kalmomi kuma da suke nufin; 1-Salladuwa 2-Jagoranci da shugabanci.
"Wilaya" kalma ce da ake amfani da ita da ma'ana biyu a isdilahin fikihu:
1- Wuraren da wanda ake da wilaya kansa ba shi da ikon tafiyar da lamurransa, kamar mamaci, wawa, mahaukaci, yaro, to a nan Kalmar wilaya tana nufin daukar nauyin lura da lamurra. Kuma ma'anaunin yin hakan shi ne shi wanda ake da wilaya kansa ya zama ba zai iya yin lamurransa ba da kansa.
2- Wuraren da wanda ake kula da lamarinsa zai iya tafiyar da lamarinsa, sai dai akwai wasu lamurran da yake bukatar mai kula da lamurransa. A nan wilaya tanan nufin tafiyar da lamurran mutane wato jagorancin siyasa ke nan.
"Wilaya" a harshen larabci an ciro da daga Kalmar "Walya" ce wacce take da ma'ana guda daya ne da take nufin kusanci[1]. A larabci an yi amfani da Kalmar "walya" da ma'anoni uku ne; 1- so. 2- Kauna. 3- Taimako. Kuma an yi amfani da Kalmar "wilaya" da wadannan ma'anoni da karin wasu bayan hakan da suka hada da[2]: 1- Jagoranci. 2- Iko da tafiyar da hukuma[3].
A harshen farisanci an kawo ma'anoni masu yawa ga wannan kalma kamar aboki, mataimaki, sahibi, mai kiyayewa, wanda yake an sanya shi kula da wani abu, haka nan aka kawo ma'anar tafiyar da hukuma[4].
Yayin da aka yi amfani da Kalmar wilaya ga malami to abin da ake nufi ana amfani da ita ne a kan jagoran hukuma ne, wato shugaba, wanda yake yana da ikon gudanarwa kan lamurran al'umma na hukuma[5].
Wannan yana koma wa zuwa ga tafiyar da lamurran al'umma ne wadanda yake da hakkin tafiyar da lamurransu, kamar dai yadda aka sani cewa shugaban mutane shi ne mai yi musu hidima[6]. Shi jagora ne kan mutane ba kaya ba ne a kansu.
Ta wani bangaren kuwa a fikihu a nan amfani da wannan kalma ta "wilaya" kamar haka ne:
1- Wuraren da wanda ake da wilaya kansa ba shi da ikon tafiyar da lamurransa, kamar mamaci, wawa, mahaukaci, yaro, to a nan Kalmar wilaya tana nufin daukar nauyin lura da lamurra. Kuma ma'anaunin yin hakan shi ne shi wanda ake da wilaya kansa ya zama ba zai iya yin lamurransa ba da kansa.
2- Wuraren da wanda ake kula da lamarinsa zai iya tafiyar da lamarinsa, sai dai akwai wasu lamurran da yake bukatar mai kula da lamurransa. A nan wilaya tanan nufin tafiyar da lamurran mutane wato jagorancin siyasa ke nan.
"wilaya" a nan tana nufin tafiyar da lamurran al'umma wacce ita ce jagorancin siyasa, kuma duk da cewa Kalmar "wali" tana da wannan ma'ana guda biyu kuma duk za a iya amfani da ita game da jagorancin malami, sai dai a nan muna nufin ma'ana ta biyu ce, domin malami jagoancinsa yana shafar lamari na biyu ne da ya shafi al'umma baki daya wanda ya hada da malamai da sauran 'ya'yan al'umma.
Wannan lamarin bai kasance domin takaituwar al'umma a matsayin al'umma ba ne da wasu suke neman kwatanta jagorancin malami da lamarin kula da lamurran raunana cikin al'umma kamar mamaci ko yaro[7], wannan ya kasance ne domin ita al'umma tana bukatar jagora mai tafiyarwar ne. Imam Ali (a.s) yana cewa: "Babu makawa ga al'umma su kasance suna da shugaba na gari ne ko fajiri[8]. Wannan wani abu ne da al'umma take bukatarsa matuka
Kuma duk sa'adda aka samu wata al'umam, to dole ne a samu wasu abubuwan da suna bukatar tsari da zai kasance karkashin jagorancin wani mutum daya a matsayin jagora.
Don haka ne malamin da ya kasance a matsayin jagora kan al'umma yake sanya wannan al'ummar kan hanya da shiryarwar musulunci, don hakan ne jagoranci ba komai ba ne sai jagorancin shiriyar addini.
Karin bayani:
1. Mahdi Hadawi Tehrani, Wilayat wa Diyanat, Mu'assar Al'adun Khaneye Khirad, Kum, bugu na biyu, 1380.
[1]. Makayisul Luga: j 5, s 141. Alkamusul Muheed: s 1732. Almisbahul munir: j 2, s 396. Assihah: j 6, s 2528. Tajul Arus: j 10, s 398.
[2]. Almuntazari: Dirasatun fi wilayatul fakih wa fikhuddaula; j 1, s 55.
[3]. . Alkamusul Muheed: s 1732. Almisbahul munir: j 2, s 396. Tajul Arus: j 10, s 398.
[4]. Muhammad Mu'in, Farhange Farsi, j 4, s 5054 da 5058.
[5]. Mahdi Ha'iri Yazdi, hikmat wa hukumat, s 67 da 177.
[6]. Biharul anwar: majlisi: j 76, s 273. (Shugaban mutane shi ne mai yi musu hidima).
[7]. [7]. Mahdi Ha'iri Yazdi, hikmat wa hukumat, s 67 da 177.
[8]. Nahjul balaga, Subhi Salihi: Khuduba 40, s 82.