advanced Search
Dubawa
6102
Ranar Isar da Sako: 2014/11/19
Takaitacciyar Tambaya
Shin riwayoyin da suke cewa salmanul Farisi da Abuzarri lokacin dawowar imam zaman (as) suna daga cikin matamaimakansa riwayoyi ne ingantattu Salamu alaikum shin Hadisin da aka nakalto daga littafin biharul anwar da cewa wasu daga cikin sahabban Manzon Allah (s.a.w) da sahabban imam Ali (a.s) misalin salmanu da abuzarri lokacin bayyanar imam Mahadi (as) zasu dawo wannan duniya kuma zasu kasance daga mataimakan imam zaman (as) shin wadannan riwayoyi suna da ingantaccen tushe ko kuma daga raunana suke?
SWALI

Amsa a Dunkule
  1. Kamar yadda ka sani shi batun raja’a lamari ne yake daga akidojin shi’a imamiya, kuma ita raja’a ma’anarta ita ce: dawowa duniya bayan mutuwa gabanin tashin kiyama, sannan raja’a ba ta shafi kowa da kowa ba, ta kebanci muminai tsantsa da mushrikai tsantsa.
Akwai ruwayoyin da aka nakalto daga ingantattun masadirai dangane da batun raja’a, daga cikinsu akwai ruwayar:
 «وَ رَوَى الْمُفَضَّلُ بْنُ عُمَرَ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ (ع) قَالَ‏ يُخْرِجُ الْقَائِمُ ع مِنْ ظَهْرِ الْكُوفَةِ سَبْعَةً وَ عِشْرِينَ رَجُلًا خَمْسَةَ عَشَرَ مِنْ قَوْمِ مُوسَى (ع) الَّذِينَ كَانُوا يَهْدُونَ بِالْحَقِّ وَ بِهِ يَعْدِلُونَ‏ وَ سَبْعَةً مِنْ أَهْلِ الْكَهْفِ‏ وَ يُوشَعَ بْنَ نُونٍ وَ سَلْمَانَ‏ وَ أَبَا دُجَانَةَ الْأَنْصَارِيَّ وَ الْمِقْدَادَ وَ مَالِكاً الْأَشْتَرَ فَيَكُونُونَ بَيْنَ يَدَيْهِ أَنْصَاراً وَ حُكَّاما
  1. Mufaddal bin Umar ya rawaito Abu Abdullah (a.s) ya ce: ka’im (as) zai fito da mutum 27 daga garin kufa mutum 15 daga mutanen Musa (a.s) wadanda suka kasance suna shiriya da gaskiya suna yin adalci da ita da kuma mutum bakwai daga Ashabul kahfi da Yusha’u bin nun da salmanu da Abu Dujanatal Ansari da Mikdadu da Malikul Ashtar  sai su kasance alkalai a gabansa kuma mataimaka. [1] [1]
  2. wannan ruwayar duk da cewa ta zo daga masdari ingantacce misalin littafin Irshad  da Tafsirin Ayyashi, [2] [2] sai dai cewa ka sani bai da ma’anar cewa dukkanin riwayar da aka nakalto ta daga ingantaccen littafi ba lallai ne ita ruwayar ta kasance ingantacciya ba, dole a kowanne waje a lura da isnadi da matani.
  3. Da yawa daga ruwayoyi da suka zo kan raja’a ba su ambaci sunaye ba, sannan wadanda suka zo da amabton sunaye mutane misalin Manzon Allah (s.a.w), A’imma (a.s) hadhrat isa (a.s) da annabawa misalin zakariyya hizkilu (a.s) wadanda a kan tafarkin Allah suka fuskanci azaba da wahalhalu, haka ma wasu ruwayoyin sun ambaci cewa Imami na farko da zai fara dawowa shi ne imam Husaini (a.s).
 
[1] Mufid muhammad bn muhammad isrhad juz 2 sh 386
[2] Ayyashi mohd bn mas’ud juz 3 sh 33 mabugar ilimiya Tehran.
 
[1] Mufid muhammad bn muhammad isrhad juz 2 sh 386
[2] Ayyashi mohd bn mas’ud juz 3 sh 33 mabugar ilimiya tehran
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa