advanced Search
Dubawa
12696
Ranar Isar da Sako: 2019/05/15
Takaitacciyar Tambaya
Kasantuwar ya zo cikin hadisi cewa Sayyida Fatima (a.s) a wata rana bayan wafatin Manzon Allah (s.a.w) ta yi shaukin ganin Salmanul farisi sannan Fatima (a.s) lokacin haduwar ta da Salmanu ta sanya gajerun kaya, yaya za a iya fuskantar da wannan hadisi?
SWALI
Ya zo a hadisi: «عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ سَلْمَانَ الْفَارِسِیِّ عَنْ‏ أَبِیهِ قَالَ: خَرَجْتُ مِنْ مَنْزِلِی یَوْماً بَعْدَ وَفَاةِ رَسُولِ اللَّهِ ص بِعَشَرَةِ أَیَّامٍ... فَقَالَ ع یَا سَلْمَانُ ائْتِ مَنْزِلَ فَاطِمَةَ بِنْتِ رَسُولِ اللَّهِ ص فَإِنَّهَا إِلَیْکَ مُشْتَاقَةٌ تُرِیدُ أَنْ تُتْحِفَکَ بِتُحْفَةٍ قَدْ أُتْحِفَتْ بِهَا مِنَ الْجَنَّةِ... قَالَ سَلْمَانُ الْفَارِسِیُّ فَهَرْوَلْتُ إِلَى مَنْزِلِ فَاطِمَةَ ع بِنْتِ مُحَمَّدٍ ص فَإِذَا هِیَ جَالِسَةٌ وَ عَلَیْهَا قِطْعَةُ عَبَاءٍ إِذَا خَمَّرَتْ رَأْسَهَا انْجَلَى سَاقُهَا وَ إِذَا غَطَّتْ سَاقَهَا انْکَشَفَ رَأْسُهَا فَلَمَّا نَظَرَتْ إِلَیَّ اعْتَجَرَتْ ثُمَّ قَالَ یَا سَلْمَانُ جَفَوْتَنِی بَعْدَ وَفَاةِ أَبِی ص‏ قُلْتُ حَبِیبَتِی أ أجفاکم [لَمْ أَجْفُکُمْ‏] قَالَتْ فَمَهْ اجْلِسْ وَ اعْقِلْ مَا أَقُولُ لَکَ... فَقَالَتْ لِی یَا سَلْمَانُ أَفْطِرْ عَلَیْهِ عَشِیَّتَکَ فَإِذَا کَانَ غَداً فَجِئْنِی بِنَوَاهُ...». Daga Abdullah bin Salmanu farisi daga babansa ya ce: wata rana na fito daga gidana bayan wafatin manzon Allah da kwanaki goma, sai Ali ya ce: ya Salmanu ka je gidan Fatima (a.s) lallai tana shaukin ganinka tana son baka wata tsaraba da aka bata ita daga aljanna, sai Salmanul farisi ya ce: sai na yi gaggawar zuwa gidan Fatima (a.s) yar muhammad (s.a.w), kwatsam sai na same ta zaune kanta akwai wani kyalle daga abaya wacce idan ta lullube kanta kwaurinta zai yaye idan kuma ta rufe kwaurunta kanta zai yaye yayin da ta kalle ni sai ta gaza sannan tace ya Salmanu ka yi mini jafa’i bayan wafatin babana amincin Allah ya kara tabbatata gare shi da iyalansa, sai na ce ya masoyiyata ni ban yi muku jafa’i ba, sai ta ce yi shiru zauna ka hankalci abin da zance maka sai ta ce ka yi bude baki da wannan danyen dabinon sannan idan aka wayi gari gobe ka zo mini da kwallonsa. Da farko bisa zahirin wannan hadisi Sayyida Fatima ta yi shaukin ganin Salmanu wanda shi ba muharraminta ba ne ta kuma so ganinsa, me ya sa hakan? Sai dai cewa a sani nifa ba wai ina son kore ma’asumancinta ba ne, ina neman tsarin Allah daga haka, amma kuma menene ya sanya macen da take abar koyi cikin kamewa da kunya kai hatta gaban makaho tana sanya hijabi amma kuma ace a nan zuciyarta na begen ganin wanda ba muharraminta ba? Ko da kuwa wannan wanda ba muharramin ba mutum ne shi misalin Salmanul farisi, na biyu mai girma Salmanu da kansa yake cewa cikin wannan hadisi duk sanda Sayyida Zahara ta nemi lullube kanta da abayarta sai kwaurinta ya yaye haka ma duk sanda ta nemi rufe kwaurinta da abayar sai kanta ya yaye, ma’ana dai a wannan wajen shi mai girma Salmanu ya ga kwaurinta ya kuma ga kanta, me ya sanya hakan? Ko kuma misali mu ce Manzon Allah (s.a.w) da sarkin muminai Ali (a.s) su ne suka tura mai girma Salmanu zuwa gidan sayyida Fatima domin ta gaya masa wani lamari, ok shin cikin wannan hali ba zai yiwu ba ta wata hanyar ba wannan lamari ya zo gare ta ba, ta yadda za a aminta da ganin junansu tun da su ba muharraman juna ba ne?
Amsa a Dunkule
  1.  Kasancewar Sayyida Fatima (a.s) ta yi shaukin ganin Salmanul Farisi hakan ba shi da wata matsala da ma’asumancinta saboda da za ka lura da farkon hadisin da ma karshensa zaka fuskanci cewa wannan haduwa da su ka yi ta kasance bayan wafatin manzon Allah (s.a.w) sannan zaka ga cewa imam Ali da Fatima suna cikin kwanakin bakin ciki da zaman makoki da jimami suna kauna da begen cewa Salmanul farisi - wanda ya kasance mai matsayi mai girmama da hatta manzon Allah (s.a.w) yana cewa game da shi (Salmanu daga cikinmu yake Ahlilbaiti) ya kamata ya yi saurin riskarsu ya je wajensu ya yi tarayya da su cikin bakin cikinsu.
  2. Sayyida Zahara (a.s) cikin kowanne irin yanayi da wurin da yake ba na muharraminta ba ne, tana kiyaye hijabi da kamewarta, tare da lura da wannan gaba, shi Salmanu yana cikin mukamin siffanta tufafi ne wanda ke nuna saukin kan Sayyida Zahara (a.s) ba wai ya nuna cewa hakika shi ya ga kwaurin kafarta ba tsirara wanda ya kamata mu nemi tsarin Allah daga tunanin faruwar hakan gare ta, sannan kari kan haka ruwayoyi sun yi bayani karara kan cewa mataye ma’abota addini a wancan zamani suna kasancewa a karkashin abayar da suke sanyawa akwai dogon wando da yake kai wa har dunduniya, saboda haka ita ma Sayyida Zahara (a.s) tana sanye da wandon da ya rufe dukkanin kafarta cikin wannan gajeriyar abaya.
 
Amsa Dalla-dalla
Ruwayar da take da alaka da haduwa Salmanul farisi da Sayyida Zahara (a.s) wacce aka kawo ta kan wancan tambaya- a wasu litattafan shi’a an nakalto ta daga cikinsu akwai littafin muhujul da’awat da minhajul ibadat na wallafar Sayyid ibini Dawus wanda ya yi wafati a shekara 664 hijri, wanda isnadin wannan ruwaya ya kasance kamar haka: daga Shekh Ali bin Abdus-samad ya ce shekk kakana ya ba mu labari ya ce masanin fikihu Abu Hassan Allah ya jikan rai ya ba mu labari ya ce: Sayyid Shaik Alimi Abu barakat  Ali bin Husaini Hasani aljauzi ya zantar da mu ya ce shekh Abu Jafar Muhammad bin Ali bin Husaini bin Musa bin babawaihil kummi masanin fikihu (r.a) ya zantar da mu ya ce: Hassan bin muhammad bin Sa’id kufi ya zantar da mu ya ce: Furatu bin Ibrahim ya zantar da mu ya ce: Jafar bin muhammad bin Bishrawaihi kaddanu ya zantar da mu ya ce: muhammad bin Idris bin Sa’id Ansari ya zantar da mu ya ce: Dauda bin Rashid da walid bin shuja’u bin marwanu daga Asimu daga Abdullah bin Salmanu farisi daga babansa ya zantar damu ya ce:[1]
Wannan ruwaya ce mai tsayi wacce a wannan mahalli da muke ciki ka dai za a tarjama iya inda a ka yi tambaya kansa: ya zo cikin ruwayar cewa: Salmanu farisi yana cewa: kwanaki goma bayan wafatin manzon Allah (s.a.w) na fito daga gida na nufi gidan Sayyida fatima (a.s) sai Ali ya ce mini” ya kai salmanu bayan wafatin manzon Allah ka yi mana jafa’i ya masoyina ya Abu Hassan ni ban yi muku jafa’i ba, sai dai cewa bakin ciki da jimamin rashin manzon Allah (s.a.w) ya hana ni zuwa ziyarar ku, sai Imam Ali ya ce mini: ya kai salmanu taho mu tafi gidan fatima yar manzon Allah; saboda ita tana son yi maka wata kyauta kuma tana begen ganinka tana son baka tsarabar da aka kawo mata daga aljanna,  Salmanu yana cewa: sai na nufi gidan Fatima (a.s) bayan na shiga cikin gidan sai na ga Fatima (a.s) zaune sannan tana lullufe da wata yankin abaya sai dai cewa abayar duk sanda ta yunkura jawota kan kwaurin kafarta kanta zai yaye haka ma duk sanda ta jawota kanta sai kwaurinta ya yaye, lokacin da ta ga Salmanu sai ta lullufe kanta da wannan abaya, sannan Sayyida Fatima ta ce: ya kai Salmanu hakika kai tun bayan wafatin manzon Allah (s.a.w) ka yi mana jafa’i ko? Sai na ce: ya ke yar manzon Allah, shin zai iya yiwuwa a ce ni na yi miki jafa’i? Fatima (a.s) ta ce to zauna ka saurari abin da zan gaya maka ka hankalce shi sosa.[2]
 
Idan ana son samun ingantacciyar fahimta daga wannan ruwaya dole a nutsu a lura da wadannan nukdodi:
  1. Wasu daga cikin marawaitan wannan ruwaya mutane da ba a ma san sunayensu ba ne a litattafan ilimin mazajen hadisi saboda haka ruwayar isnadinta ba ingantacce ba ne.[3]
  2. Wannan ruwaya ibin Dawus ya kawo ta ne a babin cewa Sayyida Zahara (a.s) ta bai wa salmanu wata addu’a ne don kariya daga zazzabi[4] ana kiransa da sunan (hirzun Sayyida fatima)[5]
  3. Batun cewa Fatima ta yi shaukin ganin salmanul farisi, ba ta da wata matsala da ma’asumancinta da kamewarta; saboda idan da ka lura da farkon hadisin da karshensa zaka fuskanci cewa lallai wannan haduwa ta faru bayan kwanaki goma da wafatin manzon Allah (s.a.w) sannan Imam Ali da Sayyida Zahara (a.s) sakamakon wannan babban rashi da bakin ciki zuciyarsu ta shiga kadaici sai ya zama suna begen ganin Salmanu, wanda ya kasance abin girmama da kauna a wajen manzon Allah (s.a.w) da yadda ya samu kusanci dasu wanda ya kai ga cewa suna kirga shi daya daga cikin danginsu har ta kai ga manzon Allah yana ce masa (Salmanu daya daga cikinmu yake Ahlilbaiti).
Sai ya yi sauri ya tafi ganinsu domin ya yi tarayya da su cikin bakin cikinsu da kadaicinsu, ta wannan fuska a lokacin da Imam Ali (a.s) ya ga Salmanu sai ya soki lamirinsa ya ce masa ya Salmanu bayan wafatin manzon Allah (s.a.w) ka yi mana jafa’i ne? Sai Salmanu daga wannan lokaci ya fadaka cewa Fatima (a.s) ma tana begen ganinsa ta na kuma son ba shi wata tsaraba da aka kawo mata daga aljanna, saboda haka shi wannan shauki da begen ta fuskar shari’a ba shi da wata matsala.
 
Na hudu: Idan ka yi duba tare da lura zaka ga an nakalto a cikin tarihi da sira kan tsari da shakalin hijabi da tufafin Sayyida Fatima (a.s) zaka iya kai wa ga wanna sakamakon cewa ita a kowanne lokaci tare da wanda ba muharraminta ba tana cikakken kiyaye hijabi da tufafinta, sai dai cewa tana kiyaye matsakaicin haddi wanda hakan wani abin koyi ne ga sauran matan musulmai. Bisa la’akari da wannan nukuda ko matashiya daga bangaren da ya zo a ruwayar da cewa (sai kwatsaham na same ta zaune kanta akwai wani kyalle daga abaya wacce idan ta lullube kanta kwaurinta zai yaye idan kuma ta rufe kwaurunta kanta zai yaye) ya kamata a ce Salmanu kadai dai yana bayanin kaya ne wanda hakan yake nuna saukin kan Sayyida Fatima (a.s), ba wai hakika kwaurin kafarta ya kasance tsirara ba ne, Allah ya tsare mu daga wannan tunani. Kari kan wannan bayani ya zo a ruwayoyi da dama cewa mataye gama gari a wancan zamani suna sanya dogon wando a kasan abayarsu manzon Allah (s.a.w) yana cewa: (Allah ya yi rahama ga macen da take rufe kafafuwanta take sanya wandon kirki)[6] da wannan siffantawa ta kaka za ace Sayyida Zahara (a.s) wacce take da mukamin isma da kamewa da jin kunya a ce ba zata sanya wannan dogon wando kasan abayarta da take gajeriya ba? Saboda haka tabbas a kasan wannan abayar tana sanye da wani tufafin.
Bisa la’akari da wadannan nukdodi cikin sauki zamu iya banbancewa tsakanin shauki da koyar da addu’a cikin abin da ya zo a cikin tambayar, sannan ya kamata mu san cewa wasu sun yi wa wannan hadisin mummunar fahimta da ganin cewa ba sa kiyaye hukunce- hukuncen shari’a ba a tsakaninsu, dangane da muharrami da wanda ba muharraminsu ba, tabbas wannan kiyasin da suke yi gurbatacce ne.    
 
 
 

Dubawa da gyara kermani [1]   Muhujud da’awat . minhajul; ibadat: sh 5-6 wallafar ibn dawus Aliyu bn musa
[2] Muhujud da’awat. Minhajul ibadat wallafar ibn dawus Ali bn musa sh 5-6. Biharul anwar juz 43 sh 66 manakib sh 297-298
 
[4] Tambaya mai lamba 28424
[5] Muhujud da’awat: 5 hirzu maulatina fatima alaihas salam
[6] Manla yahaduruhl fakihu juz na 3 sh 467
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa