Please Wait
Dubawa
4849
4849
Ranar Isar da Sako:
2016/08/29
Takaitacciyar Tambaya
Akwai wani mutum da Manzon Allah (s.a.w) ya taho da shi daga Kasar roma, shin wannan mutumin shi ne dai Yasir baban Ammaru?
SWALI
Akwai wani mutum da Manzon Allah (s.a.w) ya taho da shi daga Kasar roma, shin wannan mutunim shi ne dai Yasir baban Ammar ko kuma wani mutumin ne daban ba shi ba, ina fatan zaku yi mini bayani.
Amsa a Dunkule
Baban Ammar sunansa Yasir Dan Aamiru Anasi, ya kasance mutumin Yeman ne[1] daga yankin muzhij, daga Kabilar “Anas”[2] har lokacin da ya isa samartaka ya kasance ya na rayuwa a Yeman, yana da Yan’uwa guda uku sai aka rasa Daya daga cikin su (ya Bata) don haka shi da ‘yan’uwansa guda biyu waDanda ake kira da Malik da Haris suka haDu suka biyo sahun Dan’uwansu da ya Bata har suka iso makka suka fara bincike suna nemansa, amma kash har suka Debe tsammani daga samunsa. Sai Malik da Haris suka koma Yeman, amma Yasir, sai ya zauna a maka kuma ya Kudurci zama na dindindin a nan.[3]
Amma mutumin nan mai suna Yasir wanda Manzon Allah (s.a.w) ya taho da shi daga kasar roma a zahiri wannan mutumin ba shi da samuwa a sarari, kamar yanda, a lokacin da inbi Hajar AsKalani yake jero sunayen sahabban Manzo (s.a.w) da ya zo kan masu suna Yasir, sunan mutum uku kaDai ya jero: Yasir Dan Aamir Anasi, da Yasir Dan suwaidul Juhaini da kuma Yasir Abul Rabda’ul Balawi, [4] wanda ba Daya daga cikin su da ya fito daga kasar Yeman.
Tabbat akwai wani mutum mai suna “Suhaibu” wanda ya kasance daga cikin sahabban Manzon Allah (s.a.w) wanda asalinsa balarabe ne amma da yake ya zauna tsahon lokaci a kasar rum, sai ya zamana ya shahara da sunan “Suhaibur Rumi” (Suhaibu Dan rum).

[1] Ibni hajar al-asKalani, ahmad Dan Ali, al-isaba fi tamyizis sahaba, j 6 sh 500, bairut darul kutubul ilmiyya bugu na Daya, shekara ta 1415.
[2] Ibni sa’ad, kitabul waKidi, Muhammad Dan sa’ad, alDanaKatul kubra, j 4 sh 101, Beirut, darul kurubul ilmiyya bugu na Daya shekara ta 1410.
[3] Adreshin da ya gabata.
[4] Ka koma Al-isaba fi tamyizis sahaba, j 6 sh 500 – 501.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga