Please Wait
Dubawa
5382
5382
Ranar Isar da Sako:
2014/10/30
Lambar Shafin
fa11206
Lambar Bayani
25041
- Shiriki
Takaitacciyar Tambaya
Akwai wasu Hadisai har a cikin Littattafan Shi’a da suke hana a yi Gini a kan Kaburbura, shin duk da samuwar wadan nan Ruwayoyin ta yaya zamu iya Halatta gina Kabari, da da Kubbobi a kan Makwantan Imamai?
SWALI
Na ga wasu hadisai da suke hana a gina makwantai da kubbobi a kan kabari. Ina neman karin bayanin wannan al’amarin
An ruwaito a cikin littafin (Manla yahadhuruhul Fakih) da littafin (wasa\'ilush shi’a) daga Imamus Sadik (a) ya ce: “Manzon Allah (s.a.w) ya hana a yi salla a kan kabari, ko a zauna a kai, ko a yi gini a kansa…”. kuma an karbo daga gare shi (s.a.w): “Kar ku mayar da kabarina ya zamo alkibla ko masallaci, domin Allah ya tsine wa Yahudawa a saboda sun dauki kaburburan Annabawan su a matsayin masallatai, ” kuma a cikin littafin (Furu\'ul kafi da Man la yahdhuruhul fakih da wasa\'ilush shi\'a) daga samma\'ah dan Maharan cewa ya tambayi Abu Abdullahi (a.s) game da ziyarar kabarbura da gina masallatai a cikinsu, sai ya ce "Game da ziyarasu ba laifi, ba za a gina masallatai a cikinsu ba) haka nan ya zo a cikin littafin (Man la yahdhuruhul fakih) daga Imamus Sadik (a.s): ”dukkan abin da aka dora a kan kabari wanda ba kasar kabarin bane to nauyi ne a kan mamaci” kuma a cikin littafin (furu\'ul kafiy da littafin wasa\'ilush shi\'a) daga Abu Abdullahi (a.s): ”Annabi (s.a.w) ya hana a kara wata kasa a kan kabari wacce bata fito daga cikinta ba ne, kuma akwai wata ruwaya a cikin littafin (Manla Yahdhuruhul fakih) daga Ali Amirul muminin, daga littafin wasa\'ilush shi\'ah) daga Ali Amirul Muminin (a.s) ya fadi abin da yake da ma\'anar cewa: "wanda yayi gini a kan kabari ko ya dora mutum mutumi a kai, to ya fita daga musulunci” a cikin (littafin wasa\'ilush shi\'a kuma) daga Abu Abdullahi ya ce Amirul Muminin (a.s) ya ce: “Manzon Allah ya aike ni zuwa Madina, ya ce kada ka bar wani hoto sai ka shafe shi, kada ka bar wani kabari sai ka daidaita shi.” kuma a cikin littafin (al istibsar da littafin wasa\'ilush shi\'a daga Aliyyu dan Ja\'afar (a.s) ya ce: "Na tambayi Abul Hassan Musa (a.s) game da hukuncin gini a kan kabari da zama a kai, shin ya inganta? Sai ya ce: ”bai inganta ba a yi gini a kai, ko zama, ko a fente shi, ko a sumunte shi”.
Amsa a Dunkule
Alkur'ani mai girma ya ambata a fili sosai, game da mas'alar gina masallaci a kan kaburburan As- habul Kahafi, a inda ya ambaci labarinsu, kuma ya halatta shi ne, bai hana ba, a'a sai dai ma, ya ambace shi ne, yana mai karfafa shi, a matsayin wani al-amari ne mai kyau.
Akwai kuma ruwayoyi masu yawa, wadanda ba wai kawai suna nuna halaccin yin ibada a kusa da kabari ne kawai ba, a'a, suna ma nuna cewa yin ibadar tana da lada ninkin ba ninkin, a wani bangare na uku kuma akwai ruwayoyin da a dubi na farko za a ga kamar sun saba daga ita wannan ayar mai girma da gungun ruwayoyi na farko, sai dai kuma dole ne a fahimci cewa abubuwan da suke faruwa, da wasu al'amura na zaman takewa, kamar yin ridda zuwa ga shirka, da fankamar yawa, da alfahari, da rashin hakuri da juriya, da wasu tunanunnuka na bata wadanda ba su dace da addinin musulunci ba, da wadanda suke barazana ga al'ummar musulmi suna daga cikin jimillar dalilan da suke sa wa a hana mutane, su nuna tsananin karkata ta wajen muhimmantar da kaburbura daga imamai ma’asumai, (a.s)
kari a kan haka kuma shi ne cewa idan muka duba gamammiyar al’adar musulmi, da kuma na Ahlul baiti (a.s) a kebance zamu gan su suna gani da idanuwansu yanda aka yi gini a kan kabarin Manzo mafi girma (Sallal lahu alaihi wa alihi) da imamai na farko kamar Imam Husaini (a.s) amma ba su hana ba, kuma matafiya da malaman tarihi sun labarta mana labarin kubbobi da yin gini a kan kaburbura, a kan idon malaman musulunci gaba dayansu, a nan ga kabarin da ake darajantawa na Abu Hanifah, a can kuma akwai kabarin Abdul Kadir, na uku kuma ga na Malam Wane, ….
kuma dadin da dawa a kan hakan, wannan dabi’ar ta watsu a cikin dukkan kasashen duniyar musulunci, tun daga arewacin Afurka har zuwa kasar Indiya, da kasashen da suka yi makwabtaka da su.
Ba a taba hanawa ba, sai a shekaru dari biyu da suka wuce, daga wasu da suke daukar kansu a matsayin masu kare tauhidi, kai kace dukkan Malaman Musulunci, a tsawon shekaru darurruka, ba su fahimci abin da wahabiyawa suka fahimta ba!!.
Kuma wannan yana nuna kasancewar dukkan Malaman mazhabobi, suna fahimtar ruwayoyin hanin nan da wata fassara ce ta daban, wacce ba ta kore halaccin gina kubbobi a kai ba.

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga