Please Wait
9189
- Shiriki
Domin mu yi bayyanin madu’in, zamu yi zance kan mas’alar ta bangare uku:
- Shin abin da aka ruwaito dangane da gajertar Imam Ali (a.s) haka ne ko ba haka ba?
- Idan har ya ingata shin gajerta aibi ne ga mutum?
- Shin mene ne fassarar wasu siffofi na ma’asumai na zahiri da aka ambata a riwayoyi da a ke ginin aibu ne?
Yanzu zamu shiga bayanin wadannan mas’aloli bi-da-bi:
Da farko dai yana wajaba -kafin amsa wannan tambayar- sanin cewa wasu sifofi da wasu ke ganinsu a matsayin aibi to ba aibi ba ne. Alal misali an san cewa daga cikin sifofin Imam Ali (a.s) a kan ce “mai sanko mai tumbi” Shi sanko na nufin wanda ba shi da gashi a gaban kai. Shi kuwa tumbi na nufin girman ciki. To zamu ba da fassara da ta dace da matsayin Amirul muminina (a.s).
A bisa zahiri “mai sanko shi ne wanda babu gashi sosai a magabacin kansa, mai tumbi kuwa shi ne wanda cikinsa ya dan daga sama amma ba don yawan cin abinci ba, domin Amirul muminina ba mai yawan cin abinci ba ne, mai tattausar rayuwa ne”[1]
A wani zance da ya yi a Nahjul balaga yana cewa: “To ku saurara shi Imaminku (Ali) a duniyarsa ya wadatu da riga guda da abincinsa gusa daya”.[2]
Bayan wannan gabatarwar wajibi ne a san cewa a ruwayoyi da ke magana kan sifofin Imam Ali (a.s) da baye-bayensa akwai lafazin “rubu’in tsawo” kalmar “rubu’i a maza”[3] wanda wasu suka fassara ma’anarta da gajertarsa.
To wannan fassarar ba daidai ba ce kamar yadda littattafan luga suka nuna. Abin da ake nufi shi ne mai yalwan kafadu. Ku duba wannan zancen a Lisanul’arab:[4]
“Kibiya murabba’a na nufin tsakatsaki ba doguwa ko gajera ba”[5]
Littatafai da dama na luga sun tafi a kan wannan fassara”.[6]
Na biyu: Idan muka dauka gajertarsa ake nufi, ya dace mufahimci cewa ita gajerta ba aibi ba ce matukar ba ta wuce daidai kima ko dabi’a ba, ko kuma ya dadu da wata tawaya ta zahiri to a nan ne illar zata bayyana. Amma idan ba haka ba gajerta ba wani aibi ba ne. Domin Allah (s.w.t) Ya halicci mutane da siffofi mabambanta. Bisa dabi’a wadannan sifofin mutane su kan bambanta, sai dai bai kamata a aibata mutum bisa launin fatarsa ko gajertarsa ko muryarsa ba.
Na uku: Abin da aka ruwaito game da sifofin zahiri na ma’asumai (a.s) tilas su zamana ba masu sa jama’a su kyamace su ko su guje su ba. Domin su jagorori ne na jama’a, dole da’awarsu ta zama ta game komai, watau kiyaye haibarsu.
Wannan mas’alar da aka ambata a riwayoyin ba ta kebanta ga Imamai ma’asumai kadai ba (a.s), ta game kowane mutum mai hidima ga addini da ke da dangantaka ta kaitsaye da jama’a. Tilas su zamana sun kubuta daga kowace siffa da zata kai ga jama’a su guje su. A sifofin lmamu kamar yadda ya zo a hadisai ya wajaba ya zamanto ba mai kuturta ko kyazbi ko ire-irensu ba.”[7]
A karshe zamu yi nuni zuwa ga wani mahimmin bayani: Amirul muminina (a.s) kwamanda ne na sojan musulmi kana shi ne babban kwamanda a yakoki uku a zamaninsa. To bisa al’ada a dabi’a ta soja ya zamana sadauki; masamman idan muka yi la’akari a yaki a kan yi fito-na-fito. Kur’ani Mai girma ya yi nuni da tsokaci a kan sifofin soja. Wannan matsayin yana nuna dabi’a ta soja na bukatar mutum sadauki kakkarfa kamar yadda ya zo a kissar Daluta:
“Annabinsu ya ce da su “hakika Allah Ya nada muku Daluta sarki a gare ku” sai suka ce “Kaka mulki zai kasance a gare shi a kammu alhali mu ne mafiya cancantar mulki daga gare shi, ga shi ba shi da yelwar dukiya! Sai ya ce: “Hakika Allah ne Ya zabe shi da mulki a kanku Ya kuma kara masa yelwar dukiya da ta jiki, Allah kuma Yana ba da mulki ga wanda ya so Allah ma yelwacin baiwa ne masani.”[8]
Yana daga cikin sifofin kwamanda na soja yelwar jiki. To hakika Amirul muminina (a.s) yana da wannan siffa kamila.
[1] Atabrizi, Jawad, a Siradudun naja’at, j10, sh429 a baiti na 1197.
[2] Assayid Radi Abuhassan Muhammamad, Nahjul balaga, sh417, wasika ta 45, dabaa’in Darulhijra, 1414H, Kum.
[3] Almajlisi Muhammad Bakir , a Biharul’anwar, j35, sh86, dabaa’in Mu’assasatul wafa’a Berut 1404 H.
[4] A littafin da ya gabata J35, sh4.
[5] Ibin Manzur Muhammad bin Karam, Lisanul Arab j8, sh101, tailfin Adabulhauza Kum,1405 H.
[6] Ibin Asir Muhammad Aljazari, a Annihayaj2, sh190, Mu’assasar Isma’iliya,Kum, 1364 H.
[7] Biharul Anwar j16, sh408.
[8] Albakara 247.