advanced Search
Dubawa
6370
Ranar Isar da Sako: 2011/04/11
Takaitacciyar Tambaya
shin Allama Majlisi na daga cikin wadanda suka habaka Daular Safawiyawa, kana mai yaba wa mahukuntanta?
SWALI
Shin Allama Majlisi na daga cikin wadanda suka habaka daular safawiyawa kana mai yaba wa mahukuntanta?
Amsa a Dunkule

Dangantaka tsakanin malaman Shi’a da mahukuntan daular Safawiya da ma mahukunta na wasu dauloli da nufin raunana Shari’a ba ne. Dalilan yin hakan su ne samar da mamora da kyakkyawan manufa ga al’umma da yin wannan alakar kan haifar don taimakon jama’a da yada Mazhabar Shi’a da al’umma, kana akwai manufar yada ilimi da fahimtar Addini bisa dogara da cewa ikon fada aji da hukuma take da shi.

Daga cikin zarge-zargen da ake dangane da alkar Allama Majlisi ta siyasa har da zuwansa fada tare da tawagar mahuntan Safawiyawa da kuma taimakawa sarakuna na zamaninsa. Babu Shakka malami kan bada kai ga yanayi da suka samu kansu a ciki. Irin alakar Allama Majlisi ba ita ce farau a gun malamai ba. Tabbas irin wadannan malamai na Shi’a suna tafi da harkokinsu ne bisa tafarki na Imamai Ma’asumai  (a.s) wadda –wani lokaci- takan ginu bisa turbar amfani da sarakuna ‘yan-kama-karya da halifofi azzalumai ta hanyar duba na sanaki ga yanayin da ake ciki musamman a bagaren mahimman lamura da matsaloli da suka Shafi duniyar musulmi da zamantakewa da ilmatarwa, ta hanyar amfani da wannan alakar da nufin aiki tukuru don samar da fa’ida da nufin amfanar da al’umma da shiryar da mutane da samar da gyara a al’umma, musamman a gefen yada Addini da yada Mazhaba ta gaskiya da kokarin samar da adalci na rayuwa. To a nan zamu iya ganin dalilai da suka sa Allama Majlisi ya yi wannan hubbasar bisa wannan manufar, watau bai yi hakan don wata manufa tasa ta kashin kai ba. Wannan hubbasar tasa ta samu ne bisa yanayi da ya samu kai a ciki da nufin cimma wancan manufar da hadafi na siyasa. Ko da yake akwai malamai da suke da ra’ayi da ya saba nasa na katse duk wata alaka da mahukuntan Safawiyawa da ma wasunsu.

Amsa Dalla-dalla

Dangantaka tsakanin malaman Shi’a da mahukuntan daular Safawiya dama wasu mahukunta na wasu dauloli ba da nufin raunana Shari’a ba ne. Dalilan yin hakan su ne samar da alfanu da kyakkyawan manufa ga al’umma da yin wannan alakar kan haifar don taimakon jama’a da yada Mazhabar Shi’a da taimkon al’umma, kana akwai manufar yada ilimi da fahimtar Addini bisa dogara da cewa  ikon fada-aji da hukuma ke da shi. Kare malamai daga shiga hadari, samun damar  bayyana musa mutanen kirki don ba da kariya ga gurare masu albarka yayata hukunce-hukuncen Shari’a a tsakanin al’umma duk wannan kan samu ne ta hanyar kyautata alaka tsakanin malamai da sarakunan Safawiyawa. Bisa gaskiya manufarsu ba bishe Shari’a ba ne, manufa ce ta yada karantarwa da ilimi. Abin lura a nan shi ne wannan alakar da kyatata fahimtar juna wata dama ce a wani zamani ta sanin Ubangiji. Abin lura a nan shi ne wancan alakar da fahimtar juna wata mahimmiyar dama ce a tarihance kana gaba ce ta samun kyakkyawar dama ga Shi’a a wannan lokacin.

MaSharhanta game da daular Safawiyawa a wannan zamani sun yi amannar cewa “Tushen daular Safawiyawa ya faro ne a matsayin kungiya ta wannan hanyar ce daular ta samu shimfida ikonta da kafuwa da tabbatar dokokinta. Tsarinta na masarauta ya kunshi sassan bangaren soja, wadda kowane sashi na da nasa aikin, kana akwai bagaren tafiyar da mulki mai kare dokoki da tsara bukukuwa na Addini da ke karkashin malaman musulmi da yadawa da bunkasa harkokin Mazhabobi, karfafawa a kan batun wilaya da bara’a, da tsattsara bukukuwa na farin ciki da na takaici da idudduka na Addini da…, duk wadannan ababe sun yi matukar taka rawa wajen habaka siyasar Iraniyawa a daular Safawiyawa.”[1]

Dangantaka Tsakanin Allama Majlisa Da Mahukuntan Daular Safawiya

Daga cikin zarge-zargen da ake yi dangane da alakar Allama Majlisi ta siyasa har da zuwansa fada tare da tawagar mahukuntan Safawiyawa da kuma taimakawa sarakuna na zamaninsa. Kafin shiga wannan batun muna ganin ya zama tilas mu yi nuni zuwa ga wani muhimmin zance shi ne:   Hakika malaman Shi’a a karkashin daular Safawiyawa a zamanin sarki Sha kafin kafuwar daular Musulunci sun rayu ne a hali na takaici da shiga tasku da nisanta su a fagen siyasa da harkar zamantakewa ta yadda aka nisanta malaman Shi’a da wakilansu daga kowane irin mukami na harka da  jama’a. Wannan ke nan! A daya gefen su kuwa talakawa sun sallama wa wadannan mahukuntan. Tambaya a nan ita ce, wane mataki za’a dauka  idan aka tsinci kai cikin wannan yanayi? Shin ya dace a tunkari wannan hukumar ta hanyar fadanci da bambadanci da amfani da addini? Ko fito-na-fito da fafatawa da yanke hulda da rashin bada kai ga mahukunta?  Shin zai yi kokarin wayar da kan jama’a don kau da matsalar?  Ko ya wajaba ya shelanta jahidi don kau da ita da nufin kafa halattacciyar gwamnati da rusa ta baya? Ko kuma kyakkyawar mafita a irn wannan yanayi shi ne bude kofar tattaunawa da hada kai da mahukunta don samar da fa’ida da maslaha ga Addini da Mazhaba da ma al’umma?.

Babu Shakka malamai kan bada kai ga yanayi da suka samu kansu a ciki. Irin alakar Allama Majlisi ba ita ce farau a gun malamai ba. Tabbas irin wadannan malamai na Shi’a suna tafi da harkokinsu ne bisa tafarki na Imamai Ma’asumai  (a.s) wanda –wani lokaci- takan ginu bisa turbar amfani da sarakuna ‘yan kama-karya da halifofi azzalumai ta hanyar duba na tsanaki ga yanayin da ake ciki musamman a bagaren mahimman lamura da matsaloli da suka shafi duniyar musulmi da zamantakewa da ilmantarwa,  ta hanyar amfani da wannan alakar da nufin aiki tukuru don samar da fa’ida da nufin amfanar al’umma da shiryar da mutane da samar da gyara a al’umma, musamman a fagen yada Addini da yada Mazhabar  gaskiya da kokarin samar da adalci a cikin rayuwa. A irin wannan halin malaman Shi’a kan yi kokarin samar da kyakkyawar yanayi da nufin haifar da fa’ida ga jama’a ta hanyar wannan alakar. Wannan salon zamu gan shi a tsarin rayuwar Amirul muminina (a.s) haka kuma a rayuwa ta Imamai (a.s) na bayansa. Ga misalai:

- Taimakon da Amirul muminina (a.s) ya yi ga daulolin halifofin nan uku, da karbar mukamin gwamnan Ahawa’az da almajirin Imamu Sadik (a.s) watau Abdullahi Annajashi ya yi, Aliyyu bin Yakdin ya rike ministan kudi a gwamnatin Harunarrashid bisa umurnin Imamu  Kazim  (a.s), Imamu  Rida  (a.s) ya karbi makamin wilayatul ahad (yarima) a gwamnatin Ma’amun  Abbasi, Alkawaja Nasiruddin Dusi ya yi aiki a gwamnatin Holako da sauran su. Kazalika manyan malamai na Shi’a shigarsu gwamnatin Safawiyawa ya  taimaka a bangaren siyasa, malaman sun hada da gogaggen masani Alkarki, sheikh Baha’i, Allama Majlisi babba da Majlisi karami da sauran su, sun riki wasu mukamai na siyasa a fannin Addini. Abin lura a nan shi ne shigarsu gwamnatin Safawiyawa ba ya nufin sun shiga ne don bukata ta kashin kai ko samun matsayi ko mukami don tara dukiya ko kudi ba. Sun yi kokarin ne da nufin kare daula ta Shi’anci ta wani gefen. Wajabcin kulla wannan kyakkyawar alaka kan iya bayyana karara idan aka dubi wariya da a kan yi wa malaman Shi’a a tsawon tarihi. A bisa dabi’a kulla kyakkyawar alaka tsakanin mahukunta takan tsayu ne da nufin samar da wata dama ga malamai na sauke wani muhimmin nauyi da ke wuyansu da nufin kare Addini da Mazhaba da yada ta don ida sako na ilmantarwa da kare gundarin Mazhabar Shi’a da  kakkafa makarantun Hauza da ilimi da sauran su.

Domin karin bayani za’a iya duba gurare kamar haka:

  1. Marwi Baradanshiya siyasi Allama Majlisi; izalatu mazhab siyasi inda Allama Majlisi.
  2. Mujallat Hukuma Islamiya, daba’i na 20,suldan muhammadi, Abulfadal; <mururu bar’andake siyasia=Allama Muhammad Bakir Majlisi>

 


[1] . Nahram Nazad Muhusin safawiyah darkastara tarikh Iran zamin sh99, (makalar siyasar kan daujjlar Safawiyawa), daba’in IntiShara’at sanwidah,  jami’ar Tehran 1383 HK.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa