Please Wait
12367
Ma’anar tayarwa a luga da kuma a ma’ana ta shari’a: A ma’ana ta luga taro yana nufin a tattara abu waje daya, amma a yaren shari’a, yana nufin Allah zai tattara halittu domin ya yi musu tambaya su ba da amsa. Hakika an zo da ra’ayoyi guda biyu a dunkule a game da yadda tara dabbobi zai zama a ranar alkiyama.
- Ba wani maganar tayar da dabbobi da tara su a ranar alkiyama, mutuwar dabbobin ita ce Kiyamar su da tara su, saboda ita dabba ba mukallafa ba, yin tambaya da hisabi ya kebanci Mukallafai ne kawai.
- A daura da ra’ayin farko kuma, wasu sun ce, lallai dabbobi sun ba da Kiyama da tara sun kamar yadda yake ga mutumi, cewa za a tara su ranar Alkiyama, domin dukkanin dabbobi suna da ji a jiki da fahimta irin tasu, to za a yi musu tambaya dai-dai da fahimtar.
ILIMIN DABBOBI DA SUKE JI A JIKIN SU:
Kari kan ayoyi da ruwayoyi masu yawa wadanda suke nuni a bisa ilimin dabbobi da abin da suke ji a jikin su, to sannan gwaje-gwajen da ilimomin zamani suna karfarar wannan abin da ake da’awa a kansa, daga cikin gungun ayoyin da suke nuni a kan haka zai iya yiwuwa mu kafa dalili a kan haka da zancen tururuwa da yadda ta nbemi guduwa daga rundunar Annabi Sulaiman amincin Allah su kara tabbata a gare shi haka nan kissar tafiyar Al-hudu-hudu zuwa ga nahiyar Saba’I a yaman, da kuma labarin Mai Tayar da hankali da abin mamaki wacce ya kawowa Annabi Suleiman amincin Allah su kara tabbata a gare shi, haka nan kuma tarayyar tsuntsaye a wajen tattaunawar da aka yi a fadar Annabi Sulaiman da Makamantan haka, dukkanin wannan za su iya yiwuwa a kafa dalkili a kancewa lallai dabbobi suna da abin da suke ji a jikinsu da ya karara halittar su kawai. Dangane da ruwayoyi kuma wadanda suke bayyana sashen wasu matakai da darajoji na dabbobin, idan ko bah aka ba, to babu wata ma’ana na ba su irin wadancan darajojin da matakan, misalign wannan shi ne ruwayar da ta zo daga Imam Assajad amincin Allah su kara tabbata a gare shi a maganar sa da take cewa: Tabbas Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya ce: Babu wani rukuni da ya tsaya a matsayar nan ta Arfa sau bakwai na aikin Hajji face Allah ya sanya shi a cikin ni’imar aljanna ya kuma yi albarka a tsatson sa”
Amma game da abin da ya kebanci gwaje-gwaje da ababan da aka lura na zamani to mu muna ganin cewa dukkanin dabbobi da su ko ya cuce su, dabba ta san makiyin ta ta kuma san abokin ta, sannan tana gujewa fadawa hatsari yayin da ya mamaye ta, kamar dai yadda take yin motsi zuwa ga abin da zai amfane ta, koko tana tanadar kan ta domin kayo da tsayawa ga sashenb wasu abubuwa masu muhimmanci da aka jingina mata, dukkanin abubuwan nan da suka gabata suna nuni ne zuwa ga mallakar da dabba take da shi na ji a jiki da kuma fahimtar da ta wuce haddin ta na dabi’a.
Idan mun ce ji a jiki a fahimta su ne abubuwan da suka ba mutum mallakar inganci na kiyama sa da tara shi da kuma komawar sa zuwa ga Allah, to haka nan ma fahimtar dabba da ji a jikin ta su ne suka ba su mallaka na kiyamar su da tara su da kuma komawar su zuwa ga Allah. Hakika masu cewa dabbobi ma za su fuskanci tsayawar kiyama da taron ta, sun yi riko da ayar nan madaukakiya ne na maganar Allah Madaukaki da ya ce “yayin da za a taro dabbobi”, suka ce: Abin da ake nufi da ayar shi ne tattara dabbobin da tara su waje daya a ranar alkiyama. Kuma wannan ra’ayin abin da ya zo a cikin aya Madaukakiya a maganar Allah Madaukaki tana karfafar sa inda ya ce: “Babu wata dabba da take kan doron kasa ko wani tsuntsu da yake tashi da fukafukan sa face su ma al’umma ce irinku, kuma ba a bin da muka yi sakacin zuwa da shi a cikin littafi, sannan zuwa ga Ubangiji su za a tashe su”.
A wannan ayar mai Gaskiya Madaukaki ya kamanta dabbar da mutum ne hakankuwa a’inda ya ce” “Al’umma ce irin ku”, idan mun bibiya ayar Madaukakiya za mu sake ganin maganar sa Madaukaki da ya ce: “Sannan zuwa ga Ubangijinsu za mu tashe su”. A nan ma akwai abin da yake nuni cewa dabbobi kamar mutane ne za su mutu daga baya kuma a tashe su a ja su zuwa ga Ubangijin su, a ranar taro, sannan ruwayoyin Musulunci sun karfafi wannan ma’ana, domin ruwaya ta zo daga bangare Sunna daga Annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi game da Tafsirin ayar da ta gabatar cewa: Lallai Allah Mai Tsarki da sannu zai tara dukanin wadannan dabbobi ya dauki fansar sashen su zuwa sashe, har ma an ce zai dau fansar dabbar da ba ta da kaho daga wacce ta buge ta da take da kaho, a wasu kuma ruwayoyi daban a wannan fage, daga cikin su akwai cewa: “Allah zai yi adalci ga akuyar da ba ta da kaho daga wacce take da kaho.”
Ma’ana ta Lugga da kuma ta Isdilahi game da kalmar “Hashar”
Taro[1] a ma’anarsa ta gargajiya, yana nufin tattaro abu, an yi amfani da wannan ma’anar a cikin maganar Allah Madaukaki da ya ce “Wannan taro ne wadda yake da sauki a gare mu”.[2] Amma a ma’anarsa ta shari’a, to ita wannan Kalmar ta zo da ma’anar taron da Allah mai tsarki zai yi ga halittunsa ya zo a fadin Allah Madaukaki: “Ku ji tsoron Allah ku sani cewa gare shi za a tara ku”.[3]
Dabbobin daji: Jama’ ne: Kwaya daya dagan su shi ne (dabobin daji) dabbar jeji akasin fa ita ce dabbar gida[4] da aka saba da ita, an yi amfani da lafazin jeji ne a kan dabbobin da ba su saba da mutum ba ta jin dadin ta zama kusa da shi.[5]
Sannan mas’alar Kiyamar dabbobi da tara su suna daga cikin mas’alolin da masu ilimin magana da masu fassara suke samun sabani a kan ta, wasu sashe kuma sun yi Imanin da cewa tsayuwar Kiyama da tambaya da amsa yana daga cikin abin da makallafai suka kebento da su, tun da dabbobi ba makallafai ba ne, to ba za a tayar da su a yi musu hisabi ba, Kiyamar kowacce dabba ita ce mutuwar ta, gefan haka kuma, mafi yawan malamai sun tafi a kan cewa dukkanin dabbobi suna da shirin (Ji a jiki) da fahimta kuma za a tara su ranar Alkiyama a yi musu hisabi da abin da ya dace da su, na wannan abin da suka mallaka na shu’uri da fahimta.
ILIMIN DABBOBI DA ABIN DA SUKE JI NA JIKIN SU
(SHU’URI)
An sami ayoyi da ruwayoyi masu yawa da suke nuni da cewa dabbobi sun mallaki ilimi da shu’uri kari a kan cewa gwaje-gwajen mutum da iliminsa na zamani ya karfafi wannan ma’ana, ya taka wa wannan abin da ake da’awa a kansa, zai iya yiwuwa a kafa dalili da gudanar da tururuwa ta yi daga gidan ta lokacin da ta ji wucewar rundunar Annabi Sulaiman[6] amincin Allah ya tabbata a gare shi, haka har kissar tafiyar Alhudu-hudu zuwa garin sa, da yake Yaman da kuma dawowar sa yana mai dauke da labarai masu ta da labarin mai jan hankali ga Annabi Suleiman[7] amincin Allah ya tabbata a gare shi, da kuma yadda tsuntsaye suka yi tarayya wajen tatttaunawar da aka gudanar da ita a gaban Annabi Sulaiman. Haka nan zancen tsuntsaye da suke yi da junansu da ma alfahrin da Annabi Sulaiman amincin Allah ya tabbata a gare shi, ya yin da cewa Allah ya sanar da shi[8] maganar tsuntsu dukkanin wadannan abubuwan da suka gabata suna nuni ne da cewa dabbobi ko tsutsaye[9] suna da shu’uri da fahimta da ta wuce dabi’ar su ta halitta domin ya zo a cikin Kur’ani Mai Girma cewa; dukkanin samammu “Babu wani abu face yana tsarkake Allah da yi masa godiya, sai dai ku ne ba kwa fahimtar hakan”.[10] Hakika wannan tasbihin na hakika ne, daukar sa a matsayin tasbihi bisa ba harshen na ishara ko nuni ba zai ba da wata ma’ana ba.[11]
Hakika ya zo a cikin wasu ruwayoyi cewa ita wannan ayar tana daga mafifitan dalilai na cewa wannan tasbihi yana fitowa ne bisa ilimi da zancen harshe ba na hali ba, domin da abin nufin shi ne tasbihi da harshen hali wanda yake nuni zuwa samuwar mai halitta, to babu ma’ana game da fadin Allah Madaukaki da ya cewe: “sai dai ku ne ba kwa gane tasbihin nasu” inda ya ce: magana ta Gaskiya ita ce: Tasbihin na hakika he da ka fada da baki babu ma’ana a dora fahimta a kan cewa tasbihi ne na hali.
Hakika ya zo a cikin wasu sashen ruwayoyi da suka tabbatar da darajoji da martabobi na wasu sashe.[12] Dabbobi kamar ruwayar da take cewa: tabbas rakumin da ya je Makka har sau uku dan aljanna ne, kamar yadda aka rawaito daga Imam Assajad fadinsa da ya ce: “Lallai Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya ce: Babau wani rakumi da ya tsaya a matsayan nan ta Arfa na hajji8 sau bakwai face Allah ya sa shi a cikin ni’imar aljanna, ya kuma yi albarka a cikin tsawonsa”.[13] Irin wadannan ruwayoyi suna nuni ne da cewa lallai dabbobi suna da fahimta da shu’uri idan ko ba haka ba, to ba ma’ana a ba wa dabbobi irin wadannan darajoji da matsayai. Amma ta fuskacin da gwaje-gwaje kuwa to mu mun ga cewa gaba dayan dabbobi suna san abin da yake amfanar su da kin abin da yake cutar da su, sannan suna san makiyansu da kawayen su kamar yadda suke gudu yayin da suka fuskanci hadari sannan kuma suke yunkuri zuwa ga abin da zai amfane su, kari a kan damar da suke da ita na karbar ilimi da ma iya tsayuwa da yin sashen wasu aikace-aikace da aka kifa zuwa gare su.
KAMANCECENIYA TSAKANIN TAYAR DA DABBOBI DA KUMA TASHIN DAN ADAM:
Abin da za a fa’idantu da shi daga ayoyi da ruwayoyi bisa yanayi bayyananne shi ne tabbas dabbobi kamar mutum ne game da matsalar rayuwa da komawa zuwa ga Allah kamar yadda mallakar fahimta da shu’uri su ne suka inganta tsayuwar kiyama da tara dan Adam, to dabbobi ma suna da wani gwargwado na fahimta da shu’uri da zai inganta kiyamar su da tara su, duk da yin hakan danganta da dai-dai samuwar sai daga cikin ayoyin da aka yi riko da su wajen tabbatar da haka fadin Allah Madaukaki a cikin ayar nan madaukakiya da ya ce: “Yayin da za a tayar da dabbobi”[14] yayin da suka ce: ita wannan ayar tana nuni ne a kan tayar da dabbobi a ranar kiyama, duk da sashen wasu mutanen sun ce tana nuni zuwa share fage na kiymar da kumna karewar duniya,[15] amma dai mafi yawan malaman tafsiri da suke magana a kan taron sun karfafi ra’ayin su bisa komawa zuwa ga ayar nan madaukakiya ta fadin Allah Madaukaki da ya ce: “Babu wata dabba da take a doron kasa ko wani tsuntsu da yake tashi da fukafukin sa biyu face su ma al’umma ce irin ku, sannan babu abin da muka yi sakaci ba mu kawo shi ba a cikin litattafi, sannan zuwa ga Ubangijin su za mu tashe su”.[16] Wannan ke nan mu duk da cewa wasu sashe sun yi imani da cewa abin da ake nufi da fadin Allah da ya ce: (Alummu ne irin ku) shi ne, su wadannan dabbobi halittar Allah ne kamar yadda kuke halittar Allah, kowane daya daga cikin ku dalili ne a kan girman mahaliccin wanda yake shi kadai da ilimi da ikon sa da hikimar sa,[17] imanin wasu sashe kuma abin da ake nufi da ayar wajen kamaceceniyar dabbobi da mutum shi ne a wasu al’amura ne daga cikin su akwai cin abinci da bacci ta ci daga baccin da bin hanyoyin yadda za a rayu da biyan bukatu da gudanar da al’amuran yayyen su, domin amintar musu da rayuwar tasu ta zama karbabbiya wadda za su dora su a kai domin dauwamar halin da suke a kai.[18]
Amma mafi yawan Malamai sun bayyanar da ra’ayin ta hanyar fadin Allah Madaukaki da ya ce: (sannan zuwa ga Ubangijin su za a tara su) da cewa abin da ake nufi shi ne dabbobi irin ku ne, za su mutu sannan a tayar da su daga nan kuma a tara su a gaban Ubangiji su a karshen al’amari[19] kuma tabbatattun ruwayoyi da labarrruka na Musulunci sun karfafi wannan ma’ana daga cikin ruwayoyin akwai wanda aka cirato daga Abuzar inda ya ce: Na kasance a wajen Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi, sai ga wasu jakunan dawa guda biyu suna karo da juna, sai Manzon Allah ya ce: shin kun san a kan me suke karo? Sai suka ce ba mu sani ba, sai ya ce Allah ya sani kuma zai yi hukunci a tsakanin su”.[20]
Akwai ruwaya daga Annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ta bangaren Ahlul Sunna cewa an cirato daga Annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi da suke fassrar ayar da ta gabata cewa: Lallai Allah Mai Tsarki da sannu zai tayar da dukkanin wadannan halittu a ranar alkiyama zai dauki fansar sashes zuwa sashe, ruwayoyin sun yi nuni zuwa haka a inda mai tsira da aminci ya ce: Tabbas Allah zai dauki fansar tsakanin dabba mai kaho da wacce ba ta da kahon,[21] haka nan an samu wasu ruwayoyin daban da ke magana a kan wani fage.[22]
[1] Sayyid ali akbar na alkurashi a cikin kamusul kur’ani j 2 shafi na 145.
[2] Suraru kaf aya ta 44.
[3] Surar bakara aya ta 203.
[4] Sayyid ali akbar na alkurashi a cikin kamusul kur’ani j 7 shafi na 189.
[5] Mufradatul ragi Kalmar (wahsh).
[6] Surar namlu aya ta 18.
[7] Surar namlu aya ta 21.
[8] Surar namlu aya ta 17.
[9] Surar namlu aya ta 16.
[10] Surar isra’i aya ta 44.
[11] Tafsirul mizan an allama daba-daba’I bugu na shekara 1363 h.s. j 13 shafi 110 - 112.
[12] Tafsiru nurus sakalain, gugu na hudu shekara 1373 h.s j. 1 shafi na 715 hadisi na 68.
[13] Tafsiru nurus sakalain, gugu na hudu shekara 1373 h.s j. 1 shafi na 715 hadisi na 68.
[14] Surar takwir aya ta 5.
[15] Tafsirul amsal na ayatullahi nasiru makarim sharazi j, 26 shafi 173-174.
[16] Surar an’ami aya ta 38.
[17] Tafsiru maj’amul bayan na dabrasi bugun darul ma’arifi bugu na 2 shekara 1408 h.k, j na uku (j. 3 da na 4) shafi na 174.
[18] Tafsiru maj’amul bayan na dabrasi bugun darul ma’arifi bugu na 2 shekara 1408 h.k, j na uku (j. 3 da na 4) shafi na 174.
[19] Tafsiru maj’amul bayan na dabrasi bugun darul ma’arifi bugu na 2 shekara 1408 h.k, j na uku (j. 3 da na 4) shafi na 174.
[20] Tafsiru maj’amul bayan na dabrasi bugun darul ma’arifi bugu na 2 shekara 1408 h.k, j na uku (j. 3 da na 4) shafi na 174. Da kuma tafsiru nurul sakalaini j. na 1 shafi na 715, hadisi na 69.
[21] Tafsirul manar na muhamma ridha shirazi j na 7 sshafi na 326.
[22] Biharu; anwari juzu’I na 7 shafi na 353 zuwa na 377.