Please Wait
Dubawa
5607
5607
Ranar Isar da Sako:
2012/05/05
Takaitacciyar Tambaya
don me ake kiran annabi Muhammad (s.a.w) amintacce?
SWALI
don me ake kiran annabi Muhammad (s.a.w) da Muhammad amintacce?
Amsa a Dunkule
Amintacce shi ne kishiyan mayaudari, watau ana nufin mutumin da ba ya yaudarar jama’a, kuma kowa ya natsu da shi ya dogara da shi bisa kyawun dabi’unsa. Idan muka waiga zuwa ga halayen Annabi (s.a.w) ta mu’amala da daidaku da al’umma tun a samartakarsa, zamu ga amana wata dabi’a ce da ta samu gindin zama a gun sa saboda ya Shahara da gaskiya da amana a tsakanin mutane kana kowa ya natsu da shi, wannan ya sa ake kiran sa da “Al’amin”.
Abin da yake da muhimmanci mu fadi a nan shi ne bayan kasantuwar Annabi (s.a.w) aminin wahayin Allah ne, abin dogaro ne a gun Allah (s.a.w) kamar yadda ya kasance a gun jama’a.
A addu’o’i na ziyarar Annabi (s.a.w) kamar yadda aka ruwaito daga Ma’asumai (a.s) sun zo da lafuza Kalmar “Aminullahi” a gurare da dama. Kana dimbin ruwayoyi da suka zo da wannan lakabi suna da damar gaske, wadda hakan zai kara tabbatar da abin da muke zance a kai.

Amsa Dalla-dalla
Amintacce shi ne kishiyan mayaudari, watau ana nufin mutumin da ba ya yaudarar jama’a, kana kowa ya natsu da shi ya dogara da shi bisa kyan dabi’unsa[1]. Idan muka waiga zuwa ga halayen Annabi (s.a.w) wajen mu’amala da daidaku da kuma al’umma tun a samartakarsa,1 zamu ga wata dabi’a ce da ta samu gindin zama a gun sa saboda ya Shahara da gaskiya da amana a tsakanin mutane kana kowa ya natsu da shi, shi ya sa a ke kiransa da “Al’amin”.
An ruwaito cewa wani ayari na fatake da ya bar Makka ya tafi Basara da ke kasar Sham don yin kasuwanci, sun tadda wani fasto na jiran ayarin. Suna isa sai ya tambaye su; A cikin masu aikin hajji na wannan shekara akwai mutanen Makka? Sai suka ce: “Akwai”. Sai ya ce: “To ku tambaya Ahmad bin Abdulmudallib ya bayyana? Domin a wannan watan zai bayyana, kuma shi ne Annabin karshe”. Mai ruwayar ya ce: “Da na dawo Makka sai na tambaya me ya faru”? Sai suka ce: “Muhammad bin Abdullah Al’amin[2] ya yi da’awar Annabta”[3].
Abin da yake da mahimmanci mu fadi a nan shi ne bayan kasantuwar Annabi (s.a.w) aminin wahyin Allah ne, abin dogaro gun Allah (s.a.w) kamar yadda ya kasance a gun jama’a. Wannan shi ne dalilin kiransa da “Al’amin” kamar yadda ya zo a Kur’an da kuma hadisai. Kana Annabi ba ya da bambanci da sauran annabawa, domin duka annabawa amintattu ne na wahayin Allah (s.w.t). Shi ya sa Allah ke fada a kissar Annabi Hudu (a.s) Ya ke cewa: “Isar muku nake da sakonnin Ubangijina kuma ina mai muku nasiha ne amintacce. ”3. Kamar yadda Kur’ani Mai Girma ya kawo a bisa harshen Annabi Nuhu da Annabi Ludu da Annabi Salihu da Annabi Shu’aibu (a.s) kowanne sai da ya cewa jama’arsa: “Hakika ni, manzo ne amintacce”[4].
Akwai gurare da dama a addu’o’in ziyarar Annabi (s.a.w) da Ma’asumai suka ruwaito mukan kira Annabi da Kalmar “Aminulallah”. Daga cikinsu akwai inda muke zantawa da shi a wasu ziyzrce-ziyarce muna cewa “Assalumu alaika ya rasulallah (s.a.w) Muhammadu Aminullahi wa ala rusuliHi wa aza’imi amriHi…”[5]. Ruwayoyi sun yawaita zuwa da wannan a gurare da dama, zamu kawo guri daya don ba da misali:
An karbo daga Abdullahi bin Jundub yana cewa: Imamu Rida (a.s) ya rubuta wasika zuwa gare ni ya ce: “Bayan haka, hakika Allah Ya aiko Muhammadu (s.a.w) ya kasance Aminin Allah a halittarSa, bayan kauransa sai mu Ahlul baiti muka gaje shi mu ne amintattu na Allah a bayan kasarSa”[6].

[1] Almuhaiyir, Rida, Almu’ajam Al’abajadi (Arabi-Farisi) sh4.
[2] Arruwandi, Kudubuddin, Alkhara’ij j1, sh125-126, wal Jawarih, Mu’assatul Imamu ul Mahdi (AJ) Kum, 1409 K.
[3] Al’a’raf: 68.
[4] Ashu’ara: 107,125’143’ 162’ 178.
[5] Ibinkulkwaih Alkummi, Kamiluzziyara’at, sh 201. dabaa’in IntiShara’at murtadyah, Najafui Ashraf,1365,H.
[6] Alkulaini, Muhammad bin yakub, Alkafi, j1, sh223, Darulkutub Al-islamiyah,Tehran, 1365, H.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga