advanced Search
Dubawa
28193
Ranar Isar da Sako: 2007/10/27
Takaitacciyar Tambaya
ta ya ya annabi Sulaiman (a.s) bayan mutuwar dan shi ya zamanto ya na rokon mulki da shugabanci, amma imam Husain (a.s) bayan mutuwar dan shi sai ya ce: ya Ali bayan ka wannan duniyar ba ta da wani amfani?
SWALI
ya zo cewa annabi Sulaiman (a.s) bayan mutur dansa a lokacin da ya shiga cikin musiba amma sai ya yi wannan adu'ar kamar haka {ya Allah ka gafarta man kuma ka yi mani mulki irin wanda bayana ba za ka yi ma wani ba domin kai mai yawan baiwa ne} ba tare da nuna rashin guri ga duniya ba sai ya bukaci mulkin duniyar. Amma a waki'ar karbala mun ga imam Husain (a.s) wanda shi abin koyi ne wajen hakuri da dauriya kuma ga shi da matsayin da ya fi na annabawa har da ulul'azam, a lokacin da yake tsaye kan jana'izar dansa Ali akbar (a.s) sai ya ce: {ya Ali bayan ka duniya ba ta da wani amfani}. Idan a Kur’ani abin da annabi Sulaiman ya ce da kuma aikin da ya aikata {wato rokon mulki} falalace to ya zamu yi da maganar da kuma aikin imam Husain {na nuna rashin matsayin duniya bayan rashin dansa} shi kuma mai za a fassara shi? A ba da amsa da kakkarfan dalili na hankali da ruwaya.
Amsa a Dunkule

Duk da cewa zancen annabi Sulaiman (a.s) ya na hikaya ne na daukakar matsayi da kuma yakini da Sulaiman ya ke da shi zuwa ga rahamar Allah marar karshe wanda ba za ka hada da sauran mutane ba, amma ba zaka hada da halin da imam Husain ya samu kansa ba. Saboda wannan ayar: na daya; ta na nuni da cewa annabi Sulaiman ya girgiza a lokaci guda {amma ba ya nufin ya aikata sabo ba ne} saboda mutuwa nau'I ne na musiba. Na biyu: dan da annabi Sulaiman ya rasa tun daga haihuwarsa ya na da nakasa, mafi yawan lokaci rashi ko mutuwar irin wadannan yara {na kasasu} bai tada hankali mutum so sai. Amma imam Husain a ranar ashura a lokacin da ya ke wannan bayani na daya: ya kai kololuwar sani da son ubangiji. Na biyu: dan da ya rasa wato a ranar ashura ya yi kama da manzon Allah ta hanyar magana, halaye, da jiki. Kuka da nuna damuwa a kan rashin irin wannan da ke da kama da manzon Allah dole ne komin nauyin zuciya ta sosu kuma ta yi sanyi, da farko wannan wani abu ne nau’in halitta, na biyu: ya na nuni da girman samuwar imam ne wanda a lokaci guda jarimi ne mai karfin zuciya wurin dagewa a cikin gwagwarmaya, amma kuma ya na da zuciya cike da tausai da rahama. Na uku: wannan jumlar na nuni da sadaukarwa ta imam wanda ya ba da fiyayyen abin da ya ke so ga ta farkin Allah.

Saboda haka: wannan bayani na imam bayana nufin yanke kauna da guri ga rahamar ubangiji ba ne sai dai nuni da karfin imani da guri mai yawa ga rayuwa mafificiya wato lahira.

Amsa a bayanai:

A kan dalilin sakamakon saukar wadannan ayoyi biyu 34 da 35 [1]na suratul {sad} hikayoyi da ruwayoyi masu yawa a cikin litafan tafsir da na tarihi an rawaito {in a ka kula da matsayin isma na annabi Sulaiman} kamar haka[2]:

Annabi Sulaiman yana da gurin samun da jarumi wanda zai taimaka mashi wurin tafiyar da kasa da kuma yaki da makiya, ya na da mataye masu yawa sai ya ce ma kansa: zan sadu da su baki daya domin mu samu ‘ya’ya masu yawa da za su kai ni ga hadafi na wato tafiyar da kasa da kuma yaki, amma sai ya gafala bai ce insha Allah ba wanda fadin wannan Kalmar shi ne ke nuna dogaron mutum ga Allah, a cikin wannan yanayi bai samu koda da daya ba daga matan, sai dai da nakasashe wanda ke da jiki kamar ba ruhi sai dai a dora kan kujera, saboda haka Sulaiman ya shiga tunani mai zurfi cewa ya aka yi na manta da Allah lokaci guda na kuma dogara da kai na, saboda haka sai ya tuba ga Allah[3].

Wannan ayar da farko na hikaya da cewa annabi Sulaiman ya samu girgiza a lokaci guda {ba da ma'anar sabo da} saboda rashi nau’i ne na musiba, na biyu: dan da ya rasa nakasashe ne tun da aka haifai shi, saboda haka ra sa irin wannan dan bai cika damun mutum ba. Amma imam Husain ranar ashura lokacin da ya ke wannan maganar da farko: yana cike da kamal da sani da kuma son Allah. na biyu: dan da ya ba daga tafarkin Allah yafi kowa kama da manzo Allah ta hanyar jiki, hali, magana. Wanda ya ba da kansa sakamakon kare imamin zamaninsa lokaci da ya ke shiga filin yaki sai ya ce: ni ne Ali dan Husain dan Ali, ina cikin jikokin manzon musulunci. Ina rantsuwa da Allah cewa dan zina ba zai mulke mu ba. Zan doki ku da mashi na har sai ya koma bai da kaifi. Kuma zan yake ku da takobina domin in kare babana. Zan yake ku kamar yadda matashin hashimi da alawi yake yaki[4].

Kuka da nuna rashin jindadi saboda rasa irin wannan dan da ke da wadannan siffofin komai nauyin zuciya zatayi sanyi da kuma damuwa; da farko dabi a ce, na biyu: yana nuni da girman samuwar imam ne a lokaci guda da ya ke jarumi da karfin zuciya wurin gwagwarmaya, amma zuciyarsa cike da tausai da so da kauna saboda imam tushe ne na dukkan kamala ta dan Adam so da kauna suna daya daga cikin kamalolin mutum. Manzon rahama lokacin da ya rasa Ibrahim dan sa ya yi kuka alokacin da yake amsa tambayar dalilin kukan shi sai ya ce ba kuka ba ne tausai ne dukkan wanda bai da jinkai ba zai samu jinkai ba[5].

Fatimatu Zahra (a.s) lokacin da ta zaya kan kabarin babanta manzo Allah da damuwa mai tsanani ta ce: ya baba ka tafi tafiyar ka ta sa hasken da ke cike da duniya ya tafi kuma ni'imar ta tayi jinkiri, duniya tayi haskene da hasken ka, amma yanzu ranarta mai haske ta zamo duhu mai bushewa kamar dare marar haske[6].

Na uku; wannan jimlar ta imam Husain a lokacin da ya ke kan Ali akbar wanda jikinsa ke cike da rauni da rai hannun Allah ya ce: ya Ali duniya bayan ba kai, ba ta da wani amfani; yana nuni da matsayin mai girma da Ali akbar ke dashi ga imam wanda samuwarsa ya na dai dai da rayuwar imam ne.

Na hudu: wannan na nuni da sadaukarwa irin ta imam ne saboda ya yi kyauta da abu mai daraja kuma abin da yafi so ta hanyar Allah madaukaki.

Shin wanda yake cikin koshin lafiya dansa ma haka, amma saboda neman yarda Allah ya kauda kansa ga komai shin wannan shi yafi guri zuwa ga rahamar ubangiji ko ko wanda ya rasa nakasashen dansa kuma a lokaci guda yana mai bugatar Allah ya malaka masa duniya? Ko da yake maganar annabi Sulaiman na hikaya da girman ruhinsa da daukakar matsayi, yakini, ga rahamar ubangiji marar iyaka wanda ba zaka hada shi da sauran mutane ba. Amma ba abin aunawa ba ne da halin na musamman wanda imam Husain ya samu kansa. Don haka maganar imam ba wai kadai tana nuna yanke kauna ne ba ga rahamar Allah ba sai ma dai tana nuni da guri da imani mai yawa da kuma zabar rayuwar lahira dawwamama a kan ta duniya.

Ko da yake jimlolin imam na nuna yanayi marar kyau na wancan zamanin, zamu iya fahimtar miyasa imam ya kuji duniya, imam a hanyarsa ta zuwa karbala yana cewa: duniya ta canza fuska yanda sanin ta zai wuya kyawonta na cikin gushewa, babu abin da ya yi saura cikin alkhari ga duniyar nan sai dai kamar saura rowan da aka wanke kwano kuma kamar kona ce wadda in ba tsirre masu cutarwa ba ba abin da ke fitowa cikin ta, shin ba ku luraba ba a aiki dagaskiya kuma ba su barin aiki da karya, har takai ga cewa mumini na gurin mutuwa, mutane sun koma bautama duniya addini ya zamo kan harsuna kawai[7].

A karbala ta bayyana dalilin gujema duniya da imam ya yi keta mutunci da kuma shahadantar da bayin Allah.

Imam zainul'abidin (a.s) ya ce: duk wuri ko gidan da muka sauka babana a kan shahadar yahaya dan zakariya (a.s) ya ke magana; wata rana ya ce: kaskanci duniya a wurin Allah madaukaki shi ne yanke kan annabi yahaya da kuma ba da shi ga wata mace mazinaciya daga bani isra'il a matsayin kyauta[8], haka nan ma lokacin shahadar Ali akbar imam ya ce: ta ya wadannan mutane ba su ji tsoro ba wajen keta hakin Allah da manzonsa da keta mutuncin manzon Allah[9].

 


[1] Binciken da mu kayi na jarabawar da akayima Sulaiman , sad,35.

[2] Almizan arabi ,jildi na 17 shafi na 204; tafsir namune jildi na 19, shafi na 282 rah rahshinasi,ustad misbah yazdi,shafi na 174.

[3] Tafsir namune jildi na 19,shafi na 281.

[4] Biharulanwar,jildi na 45,shafi na 43.

[5] Wasa'ilshi'a, jildi na 2,abwab dafan,babi na 17,shafi na 922,ruwaya ta 8.

[6] Biharulanwarjildi na 43,shafi na 174-18.

[7] Biharulanwar jildi na 45, shafi na 299.

[8] Biharulanwar jildi na 45, shafi na 299.

[9] Biharulanwar jildi na 45,shafi na 44.

 

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa