Please Wait
13375
- Shiriki
An samu ruwaya game da kallon mace wacce ba musulma ba ga mace musulma daga imam Sadik (a.s) yana cewa: Bai kamata ba ga mace musulma ta yaye lullubinta a gaban mace bayahudiya ko kirista, domin su suna ba wa mazajensa bayanin siffofin jikinta[1]. A wannan ruwayar dole ne mu lura da wasu muhimmai bayanai da zamu kawo su a takaice kamar haka:
1. Daga kalmar nan ta bai dace ba” zamu fahimci cewa wannan aikin makruhi ne, wato karahiya ne ga matan musulmi su yi hakan. Kuma manyan malaman mazhabar imamiyya su ma sun bayar da fatawar karhanci ne[2].
2. Abin da ake nufi da yaye lullubi yana nufin bayyanar da fuska da hannaye (zuwa wuyan hannaye) ne; domin bayyanar da wadannan wurare har ga maza ba shi da matsala a shar’ance. Sai dai kallon mata ga al’aura biyu na mace (musulmai ne ko ba musulmai ba) haramun ne. Don haka abin da ake nufi shi ne kallon dukkan jiki ban da al’aura biyu, da fuska da hannaye (zuwa wuyan hannaye).
3. Daga ambaton dalilin haka da ya zo a ruwayoyi zamu iya amfanuwa da cewa: Babu wani bambanci tsakanin matan da suke Ahlul-kitabi da wasunsu, don haka duk wata mata da zata iya yin bayanin siffofin mace musulma to ya hau kan mace musulma ta boye jikinta gareta.
4. Yankin karshen ruwayar yana bayanin dalilin hukunci ne; an yi bayanin dalilin hukunci shi ne tona sirrin bayanin jikin mace musulma da matan Ahlul-kitabi suek yi ne ga mazajensu, kuma wannan yana nuna mana cewa babu wani bambanci tsakanin miji da wanda ba miji ba. Wato; idan dai zata yi bayani ga wani mutum wanda ba mijinta ba, to wannan hukuncin na haramcin nuna mata jikin mace musulma yana nan dai.
Tambayar da ake kawowa a nan wacce ke ma kika kawo a nan: Idan kuma ba ta yin bayanin jikin musulma ga wasu mutane, to shin hakan dai cire lullubi gareta (da nuna mata jikin musulmar) ya halatta?.
Idan dai mace musulma ta samu tabbacin cewa wannan lamarin ba zai faru ba, kuma su ma wadancan matan zasu kiyaye lamarin sirrin jikinta kamar sauran matan musulmi to ba dole ba ne a yi mata lullubi da boye jikinta garesu, a irin wannan yanayin kamar yadda wasu manyan malamai suka bayar da fatawa ne cewa; ya halatta ta yi hakan[3].
Bayani mai alaka da wannan: Tambaya 1692 (shafin intanet: 1843) Bayani: Lullubin mata ga junansu.
[1] Kulaini, Muhammad bn Yakub, alKafi, j 5, babin suturta… shafi: 518.
[2] Najafi, Jawahirul Kalam fi sharhi shara’I’ul Islam, j 29, s: 63; Mausu’atul imam alKhu’I j 32, mas’ala: 28: Ya halatta ga kowanne namiji da mace duba zuwa ga wanin al’aurar… shafi: 28.
[3] Hakim, Sayyid Muhsin, Mustamsik al’Urwatul Wuthka, j 14 (mas’ala 28): Ya halatta ga kowanne namiji da mace duba zuwa ga wanin al’aurar… shafi: 22.