Please Wait
Dubawa
11587
11587
Ranar Isar da Sako:
2016/08/10
Lambar Shafin
fa1970
Lambar Bayani
50045
- Shiriki
Takaitacciyar Tambaya
Da”awar shi”a kan riddar sahabban mazon Allah {s.a.aw} bayan wafatinsa da wacce ma”ana sahabban su ka yi riddar? Shin wannan da”awa za ta iya karbuwa kuwa?.
SWALI
Yan Shi”a na da”awar cewa bayan wafatin manzon Allah {s.aw} sahabbai sun yi ridda sun koma addininsu na baya,( Biharul anwar : juz 22 sh 352 h 80) Tambayar Ita Ce shin sahabbai gabanin wafatin manzon Allah {s.a.w} sun kasance Shi”a isna-ashariyya, sai ya zamanto bayan wafatin annabi sun koma kan fahimta sunna? ko kuma dai gabanin wafatin yan sunna ne sai bayan wafatin suka canja zuwa shi”a, saboda juya baya da komawa na nufin canjawa daga wani hali zuwa wani hali daban…
Amsa a Dunkule
samuwar karkata daga nau”in bidi”a da ridda tsakankanin sashen sahabban manzon Allah {s.a.w} bayan wafatinsa.
Na farko: daga mahangar littafai na tushe na al”ummar musulmi faruwar hakan wani abu ne da aka sallamawa da babu kokwanto ko shakka ciki sannan kuma sam bai kebantu da littafan shi”a ba. Akwai tarin riwayoyi mutawatirai daga manzon Allah {s.a.w} wadanda akwai su cikin ingantattun littafan hadisai guda shida na sunna da ragowar karbabbun littafan sunna da ingantattun sanadai masu tarin yawa da suke nuni da cewa sashen sahabban manzon Allah {s.a.w} bayan wafatinsa sun yi watsi da hanyarsa da koyarwarsa sun koma kan hanyarsu da suka bari a baya, wannan shi ne ainahin abin da muke nufi da karkacewar sahabbai wanda zai jawo a kore su daga shan ruwan alkausar ranar kiyama sannan mala”ikun azaba su korasu zuwa wutar jahannama kamar yadda ya zo a hadisi.
Na biyu: ridda kamar yadda ya zo a riwayoyi ba ya nufin riddar isdilahi wacce ke kaiwa ga kafircewarsu, kadai dai na nufin komawarsu hanyarsu ta jahiliya da al”adarsu da kau da kai daga hanyar manzon Allah da koyarwarsa.
Saboda haka ba ma nufin cewa a da sahabbai yan shi”a ne sai suka canja suka koma sunna bayan wafatin manzon Allah {s.a.w} duk da cewa a mahangar tarihi da hadisi wannan abu tabbatacce ne kuma farko sunan da aka fara ji daga manzon Allah {s.a.w} shi ne shi”a, sannan farkon wanda ya radawa mabiya Ali {as} wannan suna na shi”a shi ne manzon Allah {s.a.w} kuma farkon wadanda aka fara sani da amsa sunan yan Shi”a wasu adadine daga sahabban manzon Allah {s.a.w}.

Amsa Dalla-dalla
Don samun gamsashshiyyar amsa ya zama tilas mu bibiyi riwayoyin da su ka yi Magana kan tafkin alkausar.
Tabbas imani da tafkin alkausar na daga cikin sallamammun abubuwa wajen dukkanin mazhabobin musulmai dukkaninsu sun yi tarayya kan imani da shi, akwai Tarin riwayoyi mutawatirai[1] daga annabi {s.a.w} cikin littafan shi”a da sunna da ke nuni da cewa sahabban manzon Allah {s.a.w} ranar kiyama zasu kwarara zuwa ga manzon Allah {s.a.w} don su sha daga atfkin alkausar, sai dai cewa yan kadanne daga cikinsu za a ba wa izin shan wannan ruwa, sannan kaso mai yawa daga cikinsu za a kore su daga shan wannan ruwa na kausara mala”ikun azaba su korasu zuwa wutar jahannama, yayin da suka tsinci kawukansu cikin wannan hali sai su nemi taimako daga manzon Allah {s.a.w} sai annabin rahama ya tambayi dalilin korar sahabbansa daga tafkin kausara, sai take ubangiji ya ba shi amsa da cewa wadannan mutanen bayan wafatinka sun kirkiri bidi”a wadda takaisu ga ridda.
Bayan jin wannan sako daga ubangiji sai annabi ya la”ancesu ya nemi nisanta daga garesu.
Misali daga shahin wadannan hadisai, kamar haka:
1 An karbo daga sahal dan sa”ad daga manzon Allah {s.a.w}: lalle zan rigaye ku kwarara tafkin kausara, sai wasu jama”a wadanda na sansu suma sun sanni su gangaro zuwa gareni amma sai a katangeni ga barinsu a hanasu gangarawa kausara, sai na ce su fa mutanena ne sai a ce mini hakika kai ba ka san abin da suka aikata bayanka ba, sai ince nesa nesa daga wadanda suka canja bayana[2].
2 An karbo daga Abu hurairatu daga manzon Allah {s.a.w}: ranar kiyama wasu ayari daga sahabbaina zasu gangaro zuwa gare ni amma sai a kore su daga kausara, sai ya ce: ya ubangiji sahabbaina? sai ubangiji ya ce: kai ba ka san bidi”ar da suka kirkira ba bayanka, hakika sun yi ridda sun juya baya[3] sun koma abin da suka bari baya.[4]
3 An karbo daga abu huraira daga manzon Allah {s.a.w}: yayin da na ke tsaye a tafkin kausara sai ga wasu ayari wadanda na sansu, sai ga wani ya zo ya na cewa ku taho mu tafi sai ince zuwa ina? Sai ya ce: zuwa jahannama, sai na ce: me suka yi? Sai ya ce: sun canja bayanka sun koma kan abin da suka bari baya. Ba na zaton wasu daga cikinsu za su samu ceto face gwargwadon adadin rakuman da suka bata daga cikin garken makiyayinsu,[5] (Karin Magana ce dake nuna cewa ba masu tsira sai `yan tsiraru)
4 An karbo daga ummu salama daga manzon Allah {s.a.w}: zan gaba ce ku gangara tafkin kausara, saboda haka ku yi taka tsantsan game da ni, babu wanda zai gangaro face an kore shi kamar yadda ake korar bataccen rakumi, sai ince: me su ka yi, sai ace mini, ba kasan irin bidi”ar da suka kirkira ba bayanka, sai nace: a nesantasu[6]
5 An karbo daga abu sa”id kuduri daga manzon Allah {s.a.w}: ya ku taron mutanena lalle ni ranar kiyama zan rigayeku gangara tafkin kausara; za a nuna mini wasu jama”a daga sahabbaina yayin da ake korasu zuwa ga jahannama sai daya daga cikinsu ya daga murya ya ce: ya Muhammad ni ne wane dan wane, sai manzon Allah {s.a.w} ya ce masa tabbas nasan nasabarka kwarai da gaske sai dai cewa kai ka kirkiri bidi”a bayana, ka koma kan al”adun jahilya.[7]
6 An karbo daga umar Dan khaddabi daga manzon Allah {s.a.w}: zanyi bakin kokarina wajen kare ku daga shiga wuta sai dai cewa ku za ku yi galaba kai na ku yi hujumi ku afka cikin wuta kamar yadda kwaron fara da malam buda mana littafi ke hujumi ya afka, sannan ya yi kusa kusa in yi bankwana da ku, lalle zan riga ku gangara tafkin kausara, sannan za ku gangaro zuwa gareni jama”a jama”a za kuma ku gangaro a warwatse, hakika na san sunayenku da fusakenku kamar yadda makiyayi ke banbance bakon rakumi cikin garkensa. Sai a damkeku zuwa wuta, sai in roki ubangijina ince masa mutanena al”ummata? Sai a ce mini ba ka san bidi”ar da suka kirkira ba bayanka, lalle su sunyi ridda sun koma kan abin da suka bari baya.[8]
Ya zo cikin sashen masadir na shi”a imamiya daga wasu daga cikin imamai {as} daga littafin biharul anwar na allama bakirul majalisi {rd} daga abu basir ya tambayi imam sadik {as} shin bayan wafatin manzon Allah [S.A.W] dukkanin mutane sun yi ridda in banda abu zarr da mikdad da salmanu? sai imam sadik {s.a.w} ya cewa abu basir to ina abu sasan ina abu amratul Ansari?[9]
Cikin wannan riwaya ta bihar da ta gabata za mu fuskanci cewa imam ya yi watsi da tunanin da abu basir yake na cewa in ban da mutane uku dukkanin mutane sun yi ridda bayan wafatin annabin rahama ta yadda ya Ambato masa wasu daga cikin salihai da suka wanzu kan tafarkin shiriya.
Saboda haka dangane da hadisin da ambatonsa ya gabata zamu fuskanci abubuwa kamar haka:
Na farko: hadisin bai zo daga masadir mu”utabari ba na shi”a.
Na biyu: Kalmar mutane cikin hadisin na nufin sahabbai dalili kan haka kuwa shine mutanen da imam sadik {a.s] ya tunatar da abu basir kan cewa suma suna kan shiriya dukkaninsu daga sahabbai su ke saboda haka wadanda abu basir ya ambace su da Kalmar mutane na nufin sahabbai kenan kamar wadanda ambatonsu ya zo daga baya.
Na uku: zahirin riwayar da ke sama da ragowar riwayoyi na nuni da cewa adadin wadanda suka wanzu kan shiriya daga sahabbai ya wuce adadin da riwayar da ke sama ta zo da shi, a bayyane zamu gane cewa imamai {as} cikin wadannan hadisai basu kokarin iyakance adadin wadanda suka wanzu kan shiriya daga sahabbai ba ne, a a kadai suna son yin bayani kan cewa kadanne daga mutane suka wanzu kan koyarwar manzon Allah {s.a.w} bayansa, galibin mutane sun juya daga riko da koyarwar sun komawa al”adunsu na jahiliya kamar yadda muka yi nuni kan haka a baya game da ridda, wanda ba ya nufin ridda ta isdilahi ba, kadai dai wannan na nufin watsi da riko da muslunci da komawa ga al”adun jahiliya.
Sakamakon Da Zamu Samu:-
Gaga wadannan riwayoyi zamu fahimci shi ne cewa: Kalmar haddasawa wadda ta zo da ma”anar kirkirar bidi”a cikin wadancan riwayoyi wadanda ambatonsu ya gabata, sannan ita bidi”a na nufin kawo wani tunani ko wasu akidu da ba su da samuwa cikin littafin Allah da sunnar manzonsa. Ita kuma bidi”a na daga sabo wanda hadisi ya yi bayanin cewa aikata ta na bata dukkanin ayyukan ma”abocinta sannan ta kautar da shi daga hanyar shiriya da koyarwar muslunci.
Na biyu: a bayyane ya ke daga hadisan da muka ambata a sama cewa wasu jama”a daga sahabbai bayan wafatin manzon Allah {s.a.w} sun kirkiri bidi”o”iwadanda bas u da tushe daga littafin Allah Ta’ala da kuma sannur mazonsa[10] kuma kirkirar bidi’a na daga cikin babba zunibin da ke shafe ayyukan na gari da mutum ya aikata a baya kuma tana kautar da mutum daga hanya madaidaiciya.[11]
Na biyu; ruwayoyi sun bayyana bayan wafatin ma’aiko (saw) sun faran da bidi’o’I, (hakika baka dan abin da suka farar ba a bayanka)[12] kuma laifin sa suka na farar da bidi’o’i ya gimamam har ya kai suu ga matsayin da aka haramta musu shan ruwan tafkin kausara da kuma amfanuwa da shi tare da nisantarsu daga Allah da manzonsa.
Na uku: hadisan da suka gabata a sama bai yiwuwa a fassara su da ma”anar wadanda suka yi ridda karshe karshen rayuwar manzon rahama da bayan wafatinsa, saboda mafi ingancin bayanin hakikanin waye sahabi bai haduwa da wadanda su ka yi ridda.
Ibn hajar askalani na cewa: sahabi shi ne wanda ya hadu da annabi ya na mai imani da shi ya kuma bar duniya kan wannan imani.[13]
Saboda haka su wadanda suka yi ridda ba su siffantu da wadannan siffofi ba saboda su ba su mutu suna masu imani da muslunci ba, saboda haka ba su shiga cikin bayanin sahabbai a dai dai lokacin hadisan manzon Allah {s.aw} na Magana da sahabbai ne kadai.
Bayanin waye sahabi a mahangar mutane: wadanda su ka yi ridda ba su shiga cikin sahabbai sakamakon malaman sunna sun ce kadai wadanda za a kidaya su daga sahabbai su ne wadanda suka zauna tare da da annabi lokaci mai dan tsaho.[14] A wajen tabi”i malam sa”idu dan musayyab ya bayyana wannan lokaci da cewa: mafi karanci dole ya kasance shekara daya zuwa shekara biyu.[15] Sai dai cewa wadanda suka yi ridda ba su riski annabi ba kuma ba su zauna gwargwadon wannan lokaci da malam sa”id dan musayyab ya ambata ba, malam ibn asir yana cewa: ahlul ridda ba sa cikin sahabban manzon Allah {s.a.w}.[16]
Sannan kuma kalmomi sun zo cikin hadisan tafkin kausara kamar haka: wasu mazaje daga cikinku,[17] na sansu sarai nima sun sanni,[18] a wani lafazin kuma mutane daga sahabbaina[19] na san sunayenku da fuskokinku.[20]
Bayanan da suka gabata ba yadda za a yi a jingina sun kan wadanda suka yo ridda ta kowace fuska, ballantama su ‘yan riddan basa daga cikin manyan sahabbai kuma manzo bai san fusakunsu ba kuma bai san sunayensu da nasabarsu ba. Ballantana ma sani abu da ya kamata mu ambata anan shi ne wasu daga cikin manyan sahabbai sun yiikrari da bakinsu cewa: bayan wafatin manzo (was) sun farar da bdi’o’i.[21] don haka wannan na nuni a sarari cewa wadanda aka ambata a hadisin tafki da cewa sun yi ridda kuma sun kirkiri bidi’a ba wasu mutane ne da suke sababbin shiga musulunci kamar `yan ridda ba. (hakika sahabbai ake nufi).
Na hudu: sannan abu mai kara jan hankali da kara karfafar maganar mu shi ne riwayar sahabi zaidu dan arkam wanda na daga cikin manakaltan wannan hadisin tafkin kausara, yayin da zaidu dan arkam ya nakalto riwayar daga manzon Allah {s.a.w} mutane sun tambaye shi cewa lokacin da manzon Allah {s.a.w} ke muku bayanin wannan hadisi ku nawane a wajen? Sai zaidu ya ce mun kai mu 800 zuwa 900.[22]
Na biyar: kari kan bahasin da ya gabata, idan ya zamanto maganar riddar sababbun muslunta bayan wafatin manzon {s.a.w} ta inganta sakamakon ba shirye suke ba da su ba da zakkarsu ga hukumar abubakar dan abi kuhafa ba, sai hukumar abubakar ta tuhume su da yin ridda da kafircewa saboda sun ki ba ta zakkarsu, saboda haka su wadannan mutane da ake tuhuma da ridda ba sa cikin wanda hadisin tafkin kausara ke Magana kansu. Saboda a hadisin kausara akwai maganar haddasa bidi”a su kuma alhul ridda babu wata bidi”a da a ka zargesu da aikatawa in banda ridda sannan akwai banbanci a bayyane tsakanin ridda da haddasa bidi”a, saboda ita bidi”a na nufin shi ne shigar da wani abu cikin addini wanda ba cikinsa yake ba, su kuma ahlul ridda ba su shigar da wani abu cikin addini wanda ba cikinsa ya ke ba[23], kadai dai sun yi watsi da hanya da koyarwar manzon Allah {s.a.w} sun koma abin da suka bari a baya, sannan sunan wannan aiki da suka aikata ridda ba bidi”a ba.
A ridda mutum na barin dukkanin addini ne ya koma kan tsohuwar akidarsa da tunanisa na jahiliya, amma a bidi”a mutum bai barin addini ya na zamansa cikin addinin sai zai dinga yin addinin ne bisa son zuciyarsa ya dinga sanya abin da ba addini ya ke ba cikin addini, saboda haka riddar da ta zo cikin hadisin kausara ridda ce da ta bubbugo daga bidi”a ma”ana da farko su ba ridda suka fara ba, a a bidi”a suka dinga aikatawa har takaisu ga ridda, sannan ma”anar wannan ridda shi ne komawa kan al”adunsu na jahiliya ba ridda ta isdilahi ba, a a suna nan a musulminsu illa dai suna bin al”adun jahiliyya.
Na shida: cikin hadisin kausara an kawo maganar canjawa da sauyawa kamar haka: “nesa nesa ga wadanda suka canja (gayyara) bayana”[24] “nesa nesa ga wadanda suka sauya (baddala) bayana[25]”
Wannan hadisi na sama ya bayyana cewa wasu jama”a daga cikin sahabbai bayan wafati sun caccanja abubuwa masu muhimmanci daga muslunci, wanda wannan aiki nasu ya jawo fushin Allah da annabinsa sannan manzon Allah {s.a.w} ya la”ance su ya nemi nesanta shi daga garesu cikin fadinsa: ayi nesa da su a yi nesa da su.
Wani adadi daga malaman sunnsun fassara fadin mazon Allah {s.a.w} kan sahabbansa matsayin fita dag koyarwar muslunci.
Malam ibn kasdalani daya daga cikin wanda suka yi sharhin littafin sahihul buhari ya rubuta cewa: kalmomin da aka ambata cikin hadisin tafkin kausara na nuni da cewa wasu daga cikin sahabbai sun canja addininsu, saboda wani laifi daban suka aikata wanda bai kai ga jirkita addini ba da bai zai taba yiwuwa annabi furta Kalmar nesa nesa a kansu ba, ballantana ma da zai zamanto ya maida hankali wajen ya ga ya ceto su[26]
Na bakwai: ya zo cikin hadisn kausara cewa sun dinga ja da baya har sai da suka koma kan abin da suka bari baya.[27] Kuma ya zo cewa na rantse da allah ba za su gushe ba suna komawa kan abin da suka bari baya.[28]
Wannan jumloli da suka zo a sama na nuni da cewa sahabbai sun yi watsi da koyarwar muslunci sun koma jahiliya.
Malam ibn hajar askalani na cewa: fadin manzon Allah {s.a.w}: ba za su gushe ba suna juya bayansu, ma”ana suna ridda.[29]
Na takwas: kamar yadda ya gabata cikin lafazin daya daga hadisan tafkin kausara cikin fadin manzon Allah {s.a.w}: bana tsammanin wasu zasu tsira daga cikin face gwargwadon batattun rakuma[30]
Wannan hadisi na kausara ya yi bayani karara kan cewa cikin sahabban da za su gangara zuwa tafikin kausara kadann ne cikinsu ahalin rabauta da samun tsira[31]
Kamar yadda muka gani shi batun ridddar wani sashe daga sahabbai bayan wafatin annabi {as} ba abu ne da ya zo cikin littafan shi”a ba kadai, bari madai ya zo cikin mafi ingancin littafai wajen sunna.
Haka kuma kamar yadda mu ka yi bayani a baya ita riddar sahabbai ba ya nufin wai da suna kan shi”anci sai suka canja bayan wafatin manzo ko kuma da sunna ne sai suka koma shi”a. kadai dai riddarsu na nufin sakin hanya da tsarin da manzon Allah {s.a.w} ya barsu akai da komawa kan al”adusnu na jahilya.
duk da cewa kiran wasu da sunan yan shi”a wani tabbataccen lamari ne idan muka koma tarihi da riwayoyi kamar yadda ya ke tabbace cewa farkon wanda ya fara radawa mabiya Ali dan abu dalibi daga cikin sahabbai shi ne manzon rahama da kankin kansa.[32]
Abu hatim razi ya rubuta cewa: farkon suna da ya fara samuwa a muslunci a zamanin manzon Allah {s.a.w} shi ne sunan shi”a wannan suna ya kasance lakabi ga mutane daga sahabbai sune: abu zarr salmanu ammar da mikdadu[33]

[1] Sharhin sahihu muslin niri j15-16, da umdatul kari’I j23 shafi135 da shirhi sahihul buhari kirmani 23/63. Sai Al-Tamhid na Ibn Abdulbarri 2/291.
[2] sharh Sahihu bukhari na Mustafa dib buga juz 5 h 2407
[3] Sharhi sahihul buhari na Mustafa dib albaga j5 shafi 2407
[4] Sahihul bukhari kitabul rikak babi 53 h 6213
[5]Sahihu bukhari kitabu rikak babi 53 h 2115, lisanul arab juz 15 sh 135, nihayatul garibul hadis juz 5 sh 274
[6] Sahihu muslim kitabu fada”il h 2295
[7] Musnad ahmad juz 4 sh 79, attamheed na ibn abdur barr juz 2 sh 299.
[8] Attamheed na ibn abdur barr juz 2 sh 301
[9] Biharul anwar juz 23 sh 352 Na ce da Abu Jafar (as) shin dukkanin mutane sun yi ridda in banda mutum uku, Au Zarri da Salman da Mikdad? Sai abu Abdullani y ace to ina Abu Sasanda Abu Umrata ba’ansare? J23 shafi 352
[10] Al nihaya fi garibil hadis na ibni ashir j1 shafi 351.
[11]Sunani ibni majah a gabatarwa babi na 7 shafi 49
[12] Sahihul buhari shafin bauta babi na 23 da sahihu muslim babin falaloli babi na 9.
[13]Al”isaba fi tamyizil sahaba juz 1 sh 4
[14] Mu”ujamul alfazul kur”an sh 382, usdul gaba juz 1 sh 26
[15] Usdul gaba juz 1 sh 25
[16] Nihayatu fi garibul hadis wal”asar juz 2 sh 214
[17] Sahihul buhari littafin bayi shafi 53. Da sahihu muslami , falaloli babi na 9
[18] Wanda ya gabata
[19] Wanda ya gabata
[20] Zan gane ku da sunayen ku da kamanninku …altamhid na ibni abdulbarri 2/301.
[21] Ma’arif na ibni kutaiba 134.da buhari littafin yakoki 33.
[22] Mustadarak hakeem juz 1 sh 7677. Talkis Almustadarak zahabi juz 1 sh 77. Masabihul sunna juz sh 551
[23] Mu’ujamu mufradatul kur’an na ragib ba’esfahane.
[24] Sahihu bukhari kitabul rikak babi 53. Sahihu muslim kitabul fada”il babi 9
[25]Wanda ya gabata
[26] Irshadul sari juz 9 sh 340
[27] Sahihu bukhari ktabu rikak babi 53
[28] Shin ka san abin da suka aikata a bayanka? Wallahi basu gusheba suna komawa baya. Sahihul buhari, babin bayi 23 da na fitonu 1. Sahihu muslim littafin falaloli.
[29] Fatahul bari juz 11 sh 476. Annihaya fi garibul hadis wal”asar juz 4 129
[30] Sahihu bukhari kitabu rikak babi 53 h 2115
[31] Irshadul sari juz 9 sh 342. Umdatul kari juz 23 sh 142
[32] Durrur Mansur juz 8 sh 589. Tazkiratul kuwas sh 52. Hilyatul auliya”I juz 4 sh 329. Tarik bagdad juz 12 sh 289.
[33] Kudadu sham na mohd karrad ali juz 6 sh 245
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga