Please Wait
9735
Duniyar zarra ko kuma duniyar alkawari, na nufin wani lokaci ko wata marhala ko mahalli ko kuma wata duniya ce wacce Allah ta’ala ya fitar da rayukan dukkanin mutane daga cikin tsatson Annabi Adam (amincin Allah ya tabbata a gare shi), a bisa kankanuwar sura sosai, kuma bayan da rayuka suka shiga cikin wannan dan karamin jikin sai Allah ta’ala ya riki alkawari da su a kan yin imani da ubangijintakarsa da annabtar manzanninsa da kuma yin biyayya ga imamai ma’asumai. Amincin Allah ta’ala ya kara tabbata a gare su.
Amma yin riko da wannan alkawarin, shin a wace duniya ya kasance kuma shin a wace marhala ya kasance kuma bisa wace ma’ana, ta yaya a ka yi shi, wannan abu ne da ba mu cimma wata amsa ta musamman a kansa a cikin a yoyin alkur’ani mai girma ba. Amma ruwayoyin da suka zo ta hanyar sunna da shi’a tare da cewa suna da yawa, sai dai ba su kai ga ba da gamsasshiyar amsa ta karshe kan wannan lamarin ba. Saboda haka ne ma a ka sami a ra’ayoyi mabanbanta wadanada suka nisanta da na juna, a tsaka-tsakin malamai da malaman akida da kuma mafassara (malaman tafsiri) daga cikin malaman musulunci dangane da bayanin yadda duniyar zarra take da kuma abin da ke tattare da ita na daga tambayoyi.
Hakika ayoyi da hadisan da suka zo kan bayanin wannan duniyar ta zarra - gami da abin da take kunshe da shi na daga alkawari da halittar bil’adama da kuma tabon da aka halicce shi da shi - sun bude faffadan fagen karatu da bincike faffadan gaske da kuma bada damar bayyana mahanga a kan lamarin, amma abin da za a iya kai wa ya zuwa gare shi ta hanyar wadannna ayoyin da hadisan shi ne kamar haka:-
Hakika zatin Allah madaukakin sarki ta horewa ko wane dan’adam dace na gane da sanin ubangijijntakar Allah, sai ya zama ko wane mutun na da wani nau’I na ilimi da sani wanda ake haifar sa da shi (shuhudi) dangane da mahalliccinsa, tare da cewa zai iya yiyuwa mutum ya gafala daga wannan masaniyar a yayain da ya nutse cikin shagulgulansa sai kaga ya fada cikin kogin mantuwa da gafala.
Kuma dalilan da ke tabbatar da samuwar duniyar zarra ko duniyoyin zarra, wani tari ne na ayoyi masu nagarta na daga ayoyi da ruwayoyi na hadisai wadanda ke bube sasanni da kofofi masu yawa ga masu tsananin so da shaukin zuwa ga Allah a lokacin da mutum ke nutsewa cikin tunani da tadabburi kuma ya kwakkoma duba a cikin su.