Please Wait
12161
Akwai Littattafan Hadisi masu yawa Wadanda suka kawo wannan Bayanin, An ruwaito daga Annabi mafi girma (s. a. w. a. ) yace: Kuyi Taka Tsantsan da fitsari, domin mafi yawan Azabar Kabari, shi yake Jawowa (sabbabawa)”[1] An Ruwaito daga Imam As sadik (as) cewa’mafi yawan azabar kabari, yana daga fitsari ne” (wanda ba’a bi ka’ida wajen kiyaye shiba) [2] Amma game da hikimar wannan hukunci abinda zamu ce shine: mas’ala ce tabbatacciya cewa dukkan hukunce -hukunce sun Tsayu ne akan Asasin maslaha da barna wadanda suke kunshe a cikinsu.
ko wani hukunci yana da hikima da dalili na musamman, Amma ba abu ne mai sauki a iya sanin dukkan wadannan dalilai, da iyakance su ba a mafi yawan lokuta”[3]kuma babu shakka cewa shi hankali yana iya fahimtar , rashin yin Taka Tsan-tsan acikin Mas’alar Fitsari Yana da Alaka da Al’amarin Tsarki, kuma Rushewar Sharadin Tsarki yana Jawo Rushewar wasu Ibadu ciki kuwa har da Ibada Mafi Girma kamar Sallah, A saboda haka yana iya Jawo Bacin Wannan Ibadar.
To amma Hankali ba zai iya Fahimtar Alaka a Bayyane da ke Tsakanin Azabar Kabari da Rashin Bin Ka’ida na Dokokin yin Fitsari ba . ko da yake a Dunkule yana iya Fahimtar cewa lalle, Ayyukan Mutum suna da Tasiri mai Muni ko Mai Kyau, Wadanda Sukan Shafi Rayuwar sa ta Jiki ko ta Ruh[4]i.
[1] Biharul an-war juzu’I na-4-shafi na-275babi na 8 ahwalul barzakh wal kabr a azabih.
[2] Wasa’ilush’shi’a juzu’I -1-shafi 340
[3] An cirone daga tambaya mai lamba 1360 (lambar dandali2073)