Please Wait
24076
Manzo (s.a.w) ya fada cikin mustahabbai da makaruhan jima’i cikin hadisi mai tsayi, ga Imam Ali (a.s) cewa: “ … ya Ali ka da ka tara da iyalinka cikin daren babbar salla domin idan Allah yai nufinku da samun da a wannan dare zai zamo mai yatsu shida ko hudu”[1] wannan hadisin an kara kawo shi cikin jami’ul akhbar wallafar tajuddeenish sha’iry da mukarimul akhlak, radhiyyuddeen Hassan dan fadhl attabrisy sadai hadisin ta bangarin tushensa mursali ne, amma ba za mu yi amfani da wannan hadisan ba wajan hukunta cewa duk wani ko wata daga mutane masu yatsu hudu ko shida cewa maniyyin haihuwarsu ya kyan kyasu ne a daren babbar salla, duk da cewa hadisin tushensa ya dangane, amma tare da yin ihtiyadi zamu dauke shi tsoratarwa domin hana shiga hadari, wanda zai zama riga kafi, inda a hankalce aikine mai kyau.
[1] Ash shairy, tajuddeen jamiul akhbar page 103 fasali na sittiin, cikin abin da ya kamata bayan shigar amarya dakin mijinta (gidanta), haka nan cikin bayanini kyawawa da makaruhai (a babin ki) yayin saduwa, manshuratush shareef urady Kum 1363 HS, adt dtabrisy radhiyyuddeen Hassaindan fadhl mukarimul akhlak page 209 minshiratush shareefr radhy KUM 1413 HS