advanced Search
Dubawa
9583
Ranar Isar da Sako: 2010/08/25
Takaitacciyar Tambaya
Mene ne Hukuncin Karanta Zikirin da a ka Samo Daga Abu-basir a Yayin Tashahud na Salla?
SWALI
Shin karanta zikirin Abu-basir wanda ya samo daga imam Sadiq (a.s) {Bissimillahi wa billahi walhamdulillahi wa khairal asma\' Lillah ashhadu an la\'ilaha illallah wahdahu la sharikalah, wa ashhadu anna muhammadan abduhu wa rasuluh, arsalahu bil-haq bashiran wa naziran baina yadaiyis sa\'a, ashhadu anna rabbi ni\'imal rabbi, wa anna muhammadan ni\'imal rasul, wa anna aliyyan ni\'imal wasiy wa nimal Imam. Allahumma salli ala Muhammad wa aali Muhammad wa taqabbal shafa\'atahu fi ummatihi war fa\'a darajatahu}. Shin fadin hakan yana bata salla ?
Amsa a Dunkule
Ya zo a cikin muhimman litattafan fiqihu {hukunci} cewa mustahabbi ne a cikin tashahud na biyu karanta wannan zikiri kamar haka: {Bissimillahi wa billahi walhamdulillahi wa khairul asma' lilLah, ashhadu an la'ilaha illallah wahdahu la sharikalah, wa ash'hadu anna muhammadan abduhu wa rasuluh, arsalahu bil-haq bashiran wa naziran baina yadaiyis sa'a, ash'hadu annaka nii'mal rabbi wa anna muhammadan ni'imal rasul, attahiyatulilLah wa salawatu tahiratun tayyibatun zakiyyatun gadiyatun ra'ihatun sabigatun na'amatun, ma taba, wa zakiya, wa tahura, wa khalus, wa safa, falilLah. Ashhadu an la'ilaha illallah wahdahu la sharika lah, wa ashhadu anna muhammadan abduhu wa rasuluh, arsalahu bilhak bashiran}. Amma a matsayin mustahabbi ba wai a matsayin bangare daga bangaren tashahud ba, to ba laifi yin hakan.
 
Amsa Dalla-dalla
Ya zo a cikin litattafai muhimmai na hukunce-hukuncen addini cewa daya daga cikin mustahabban tashahud shi ne yayin da mai salla a cikin tashahud na daya da na biyu ya karanta kalmomin da Abu-basir ya rawaito gada imam Sadiq (a.s). Wadannan kalmomin su ne kamar haka; {bissimillahi wa billahi walhamdulillahi wa khairal asma'Allah ashahadu an lailaha illallah wahadahu la sharikalahu, wa ashahadu anna muhammadan abduhu wa rasulahu, arsalahu bilhak bashiran wa naziran baina yadayyes sa'a, ash'hadu anna rabi ni'imal rabbi wa anna muhammadan ni'imalrasul wa anna aliyyan ni'imal wasi wa ni'imal Imam, allahuma salli ala Muhammad wa aali Muhammad wa taqabbal shafa'atahu fi ummatihi war fa'a darajatah. Sai ya yi godiya ga Allah sau biyu ko kuma sau uku sai ya tashi a cikin tashahhud na biyu {wato raka'a ta uku ko ta hudu} sai ka karanta wannan {bissimillahi wa billahi walhamdulillahi wa khairal asma' Lillah, ashhadu an la'ilaha illallah wah'dahu la sharikalah, wa ash'hadu anna muhammadan abduhu wa rasuluh, arsalahu bil'haq bashiran wa naziran baina ya daiy assa'a, ash'hadu annaka ni'imalrabbi wa anna muhammadan ni'imal rasul, altahiyatulil'Lah wa salawatu dahiratu dayibatu zakiyatu gadiyatu ra'ihatu sabigatu na'amatu ma taba wa zakiya wa tahara wa khallasa wa safaya falahu, ash'hadu an la'ilaha illallah wahdahu la sharika lah, wa ash'hadu anna muhammadan abduhu wa rasuluh, arsalahu bil'haq bashiran}[1].
Marigayi ayatullahi gulfaigani a cikin amsar da ya bayar dangane da wannan tambayar sai ya ce: "Tashahud na Abu-basir da ya zo a cikin (Urwatul wusqa) ka karanta shi kamar yadda ya zo saboda ba mas'ala ce ta tushe ba dole ne muqallidi {mai koyi} ya karanta kamar yadda ya zo rubuce ba kari ba ragi[2].
Abun tuni a nan shi ne bangaren ''wa anna aliyyan ni'imal wasiy wa ni'imal imam'' bai zo a cikin ruwaya ba {Urwatul Wusqa}.
Saboda haka karanta bangaren da ya zo a cikin (Urwatul Wusqa) kamar yadda ya zo ba kari ba ragi a kuma matsayin mustahabbi ba a matsayin bangare na tashahhud ba, ba laifi kuma bai bata salla, amma in mai salla ya karanta da niyyar cewa wani sashe ne na tashahhud to sallarsa ta baci.
Hazrat Ayatullahi Hadawi Tehrani, ya ce: Tashahhud wajibi shi ne shaidawa da kadaita Allah da kuma shaidawa da sakon manzon Allah (s.a.w), Saboda haka irin zikirin Abu-basir a matsayinsa ba zai bata salla ba.
 

[1] Alyazadi , sayyid Muhammad kazim bin abdulazim taba taba'i al'urwatul wuska{ almahshi} , jildi na 2 , shafi na 591, alnashir; mu'assasa yada musuluncin taba'at lijama'at mudarisin , tarihin bugawa 1419: k, taba'at; ula, makan taba'a; qom mukadasa , muhakki , almushah; ahmad muhsin sabzwari, tare da hawashi na fukaha, jildai na biyar.
[2] Majma'ul masa'il { gulphaigani } ,jildi na daya , shafi na 177 , yadawa ,darulkur'an , tarihi bugu 1409 k: bugu na biyu : adadin jildin 3; wurin bugawa qom mugadasa.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa