advanced Search
Dubawa
7870
Ranar Isar da Sako: 2013/08/12
Takaitacciyar Tambaya
Shin a mazhabar ja'afariyya ana yin sujada a tsakiyar salla yayin da aka ji an karanta ayar Sujada?
SWALI
Shin a mazhabar ja'afariyya ana yin sujada a tsakiyar salla yayin da aka ji an karanta ayar Sujada?
Amsa a Dunkule

Bisa mahangar fikihun Shi'a wannan mas'alar ta zo ne kama haka: Idan mai salla ya karanta daya daga cikin surori hudu da suke da ayar da wajibi ne a yi sujada in an karanta su, kuma da gangan, to sallarsa ta bace[1]. Amma idan bisa rafkana ne ya shagaltu da karantawa, ta yadda kafin kaiwa ga ayar sujada sai ya fahimta, to dole ne ya bar wannan surar ya karanta wata surar[2], idan kuwa bayan ya karanta ayar sujadar ne ya fahimci hakan[3], to dole ne ya yi sujadar da nuni kawai a cikin sallar[4], kuma ya wadatu da karanta wannan surar ke nan. Amma idan ya ji karanta ayar sujada yana cikin salla, sai ya yi sujada da nuni, to sallarsa ta yi[5].  
 

[1]. Marja'o'I kamar Khu'I, Tabrizi, Bahjat (bisa ihtiyadi sallarsa ta bai). Sistani: (Wajibi ne ya yi sujada bayan karanta ayar sujada, sai dai sallarsa ta baci bisa ihtiyadi, kuma dole ne ya sake yin salla ke nan, sai dai idan bisa rafkanwa ne ya yi salla. Idan kuwa bai yi sujada ba, to zai iya ci gaba da sallarsa, duk da kuwa ya yi laifi saboda ya bar yin sujada). Janzani: (Bisa ihtiyadi wajibi ba a karanta ayoyin sujada a salla, kai har ma bisa ihtiyadi mustahabbi ko da farkonsu ne ka da a fara karantawa). Makarim: (Duk sa'adda aka karanta daya daga ckin sororin da suke da sujadar wajibi a salla da gangan, bisa ihtiyadi wajibi ne dole a yi sujada, sai kuma a ashi a karanta fatiha da wata surar, a kammala salla, sannan a sake wata). Taudhihul Masa'il: Imam Khomain; Bani Hashimi Khomaini, sayyid Muhammad Husain, j 1, sh 545, m 983, Daftare Intisharate Islami, Kum, Bugu na Takwas, 1424 H.K.
[2]. Ayatul-Lahi Makarim: (Idan ya wuce rabi, to ihtiyadi ne ya sake salla ..); Haka nan, sh 545, m 984.
[3].  Marja'ai masu Girma, Tabiriz: (ihtiyadi ne ya yi nuni da sujada ya kamala ta uku, bayan salla sai ya yi sujada); Gulfaigani Safi: (bisa ihtiyadi ya yi nuni da sujada wajbiba, ya kamala ta uku, bayan nan sai ya karanta wata surar da nufin samun ladan wurin Allah, sai ya yi ruku'u ya kammala sujada, bayan salla bisa ihtiyadi sai ya yi sujada); Sistani da Makarim: (dole ya yi kamar na da gangan ne); Nuri: (Ya wadatu da surar da ya karanta, bayan salla sai ya zo da sujadar); Bahjati: Dole ne bisa ihtiyadi ya karanta wata surar, bayan salla kuma sai ya yi sujadar ayar); haka nan.
[4].  Ayatul-Lahi Araki: (Sai ya kammala surar, ya yi wata surar da nufin ladan Allah, sannan sai bayan ya kammala ya sake yin salla).
[5].  Marja'ai: Khu'I, Tabrizi, Sistani: (Idan ya ji sujadar yana cikin salla, to sallarsa ta yi, bisa ihtiyadi ya yi nuni da sujadar, bayan salla sai ya yi sujadar); Bahjati: (Idan ya ji sujadar yana cikin salla, to bisa ihtiyadi sai ya yi sujadar bayan salla, kuma sallarsa ta yi).
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa