advanced Search
Dubawa
6315
Ranar Isar da Sako: 2015/05/18
Takaitacciyar Tambaya
Mene ne hukuncin sallar mamaci a fikihun Ja’afariyya? Kuma yaya ake yin ta?
SWALI
Mene ne hukuncin sallar mamaci a fikihun Ja’afariyya? Kuma yaya ake yin ta?
Amsa a Dunkule
Amsar malaman Shi'a game da wannan tambaya yana kamar haka ne:
1. Yin salla ga mamaci musulmi ko yaron da yake da hukuncin musulunci[1] da ya kai shekara shida, wajibi ce[2].
2. Sallar mamaci kabbarori biyar ce kuma akwai ambaton Allah tsakanin kowace kabbara da bayani hakan ya zo kamar haka:
Bayan niyya da fadin kabbara sai a ce: «اشْهَدُ انْ لٰا إِلٰهَ إِلَّا اللّٰهُ وَ انَّ مُحَمَّداً رَسُولُ اللّٰهِ صلى اللّٰه عليه و آله و سلم» wato; »Na shaida babu abin bauta sai Allah kuma hakika Muhammad manzon Allah (s.a.w) ne«.
Bayan kabbata ta biyu sai a ce: «اللّٰهُمَّ صَلِّ عَلىٰ مُحَمَّدٍ وَ آلِ مُحَمَّدٍ»  wato; »Aminci ya tabbata ga Muhammad da aalayen Muhammad«.
Bayan kabbara ta uku sai a ce: «اللّٰهُمَّ اغْفِرْ لِلْمُؤمِنينَ وَ الْمُؤمِناتِ» wato »Allah ka gafarta wa muminai maza da muminai mata «.
Bayan kabbara ta hudu idan mamacin namiji ne sai a ce: «اللّٰهُمَّ اغْفِرْ لِهٰذَا الْمَيِّتِ» wato; »Allah ka gafarta wa wannan mamaci«, idan kuma mace ce sai a ce: «اللّٰهُمَّ اغْفِرْ لِهٰذِهِ الْمَيِّتِ» wato; »»Allah ka gafarta wa wannan mamaciya«. Bayan kabbara ta biyar sai a fada, da an fade ta to salla ta kare ke nan.
Wannan abin da aka kawo ya isa a sallar mamaci. Sai dai yana da kyau a kawo ambaton Allah mai yawa fiye da haka, sai a yi ta kamar yadda zamu kawo a nan kasa:
Bayan kabbarar farko sai a ce:
«اشْهَدُ انْ لٰا إِلٰهَ إِلَّا اللّٰهُ وَحْدَهُ لٰا شَرِيكَ لَهُ وَ اشْهَدُ انَّ مُحَمَّداً عَبْدُهُ وَ رَسُولُهُ ارْسَلَهُ بِالْحَقِّ بَشيراً وَ نذِيراً بَيْنَ يَدَىِ السَّاعَةِ»
Wato; »Na shaida babu abin bauta sai Allah shi kadai ba shi da abokin tarayya gare shi, kuma na shaida cewa Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne da ya aiko shi da gaskiya yana mai albishir da gargadi game da tashin alkiyama «.
Bayan kabbata ta biyu:
 «اللّٰهُمَّ صَلِّ عَلىٰ مُحَمَّدٍ وَ آلِ مُحَمَّدٍ وَ بارِكْ عَلى مُحَمَّدٍ وَ آلِ مُحَمَّدٍ وَ ارْحَمْ مُحَمَّداً وَ آلَ مُحَمَّدٍ كَافْضَلِ ما صَلَّيْتَ وَ بٰارَكْتَ وَ تَرَحَّمْتَ عَلىٰ ابْراهِيمَ وَ آلِ إِبراهيمَ انَّكَ حَميدٌ مَجيدٌ وَ صَلِّ عَلىٰ جَميِع الأَنْبيٰاءِ وَ الْمُرسَلينَ وَ الشُّهَداءِ وَ الصِّدِّيقينَ وَ جَميِع عِبٰادِ اللّٰهِ الصّٰالِحينَ»
Wato; »Allah ka yi aminci ga Muhammad da aalayen Muhammad, ka yi albarka ga Muhammad da aalayen Muhammad ka yi rahama ga muhamma da aalayen Muhammad, fiye da yadda ka yi aminci kuma ka yi albarka kuma ka yi rahama ka Ibrahim da aalayen Ibrahim, hakika kai abin yabo ne da godewa, ka yi aminci ga dukkan annabawa da manzanni da shahidai da siddikai da dukkan bayin Allah na gari «.
Bayan kabbara ta Uku:
«اللّٰهُمَّ اغْفِرْ لِلْمُؤمِنينَ وَ الْمُؤمِنٰاتِ وَ الْمُسْلِمينَ وَ الْمُسلِمٰاتِ الْأَحْيٰاءِ مِنْهُمْ وَ الْأَمْوٰاتِ تابِعْ بَيْنَنٰا وَ بَيْنَهُمْ بِالخَيْراتِ انَّكَ مُجيبُ الدَّعَواتِ انَّكَ عَلىٰ كُلِّ شَيْ‌ءٍ قَدِيرٌ».
Wato; »Ubangiji ka gafarta wa muminai maza da muminai mata da musulmi maza da musulmi mata rayayyu daga cikinsu da matattu, ka kuma bi tsakaninmu da tsakaninsu da alherai domin kai ne mai amsa kira, kai mai iko ne a kan komai «.
Bayan kabbara ta hudu: Idan mamacin namiji ne sai a ce:
«اللّٰهُمَّ إِنَّ هَذٰا عَبْدُكَ وَ ابْنُ عَبْدِكَ وَ ابْنُ امَتِكَ نَزَلَ بِكَ وَ انْتَ خَيْرُ مَنْزولٍ بِهِ اللّٰهُمَّ إِنّا لٰا نَعْلَمُ مِنْهُ الّا خَيْراً وَ انْتَ اعْلَمُ بِهِ مِنّا اللّٰهُمَّ انْ كٰانَ مُحْسِناً فَزِدْ فِى احسٰانِهِ وَ انْ كٰان مُسِيئاً فَتَجٰاوَزْ عَنْهُ وَ اغْفِرْ لَهُ اللّٰهُمَّ اجْعَلْهُ عِنْدَكَ فى اعْلٰى عِلِّيّينَ وَ اخْلُفْ عَلىٰ اهْلِهِ فِى الْغابِرِينَ وَ ارْحَمْهُ بِرَحْمَتِكَ يا ارْحَمَ الرَّاحِمينَ»
Wato; »Ubangiji wannan dai bawanka ne dan bawanka, dan baiwarka, ya sauka gun ka, kuma kai ne mai fiyayyen masauki gare shi. Ubangiji mu ba mu san komai ba gare shi sai alheri, kuma kai ne ka fi mu sanin sa fiye da mu. Ubangiji idan ya kasance mai kyautatawa to ka kara masa cikin kyautatawarsa, kuma idan ya kasance mai munanawa to ka ketare masa ka yi masa afuwa ka gafarta masa. Ubangiji ka sanya shi gun ka daga cikin mafi daukakar masu daukaka, ka sanya wasu daga masu nagarta masu mayewa ga ahlinsa, ka yi masa rahama da rahamarka ya kai mafi tausayin masu tausayi «. Haka nan ma a fada bayan kabbara ta biyar, sai dai idan mamacin mace ce bayan kabbara ta hudu sai a ce:
«اللّٰهُمَّ إِنَّ هٰذِهِ امَتُكَ و ابْنَةُ عَبْدِكَ وَ ابْنَةُ امَتِكَ نَزَلَتْ بِكَ وَ انْتَ خَيْرُ مَنْزُولٍ بِهِ اللّٰهُمَّ انَّا لٰا نَعْلَمُ مِنهٰا الّٰا خَيْراً وَ انْتَ اعْلَمُ بِهَا مِنَّا اللّٰهُمَّ انْ كانَتْ مُحْسِنَةً فَزِدْ فِى احسٰانِهٰا و انْ كانَتْ مُسِيئةً فَتَجاوَزْ عَنْهٰا وَ اغْفِرْ لَهٰا اللّٰهُمَّ اجْعَلْهٰا عِنْدَكَ فِى اعْلىٰ عِلِّيِّينَ وَ اخْلُفْ عَلى اهْلِهٰا فى الْغٰابِرينَ وَ ارْحَمْهٰا بِرَحْمَتِكَ يا ارْحَمَ الرَّاحِمينَ».
»Ubangiji wannan dai baiwarka ce ‘yar bawanka, ‘yar baiwarka, ta sauka gun ka, kuma kai ne mai fiyayyen masauki gare tai. Ubangiji mu ba mu san komai ba gare ta sai alheri, kuma kai ne ka fi mu sanin ta fiye da mu. Ubangiji idan ta kasance mai kyautatawa to ka kara mata cikin kyautatawarta, kuma idan ta kasance mai munanawa to ka ketare mata ka yi mata afuwa ka gafarta mata. Ubangiji ka sanya ta gun ka daga cikin mafi daukakar masu daukaka, ka sanya wasu daga masu nagarta masu mayewa ga ahlinta, ka yi mata rahama da rahamarka ya kai mafi tausayin masu tausayi«[3].
 
 

[1].  Wato uba da uwar yaron ko daya daga cikinsu ya kasace musulmi ne.
[2]. Taudhihul masa’il (hashiyar Imam khomain), j 1, s 333, m 594.
[3]. Abin da ya rigaya, s 337, m 608.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa