Please Wait
7988
- Shiriki
Rana na daya daga masu tsarkakewa kamar yadda ya zo a fikhu, yadda rana ke tsarkake gini da kasa kuwa; ka da a samu tazara tsarkakakkiya tsakanin zahirin (doron) kasa da bayanta (cikinta) ko kuma ginin da hasken ranar zai sauka a kansa kamar iska ko wani jikin (object) daban misali;
- Kamar bulon da aka yi da siminti zaka samu cikinsa bai hade duka ba zaka samu tazara da iska za ta iya bi ta cikinsa wanda ba kamar bulon kasa ba wanda yake hadadde
- Ko Kamar kasar da take da hawa-hawa a tsakaninta kamar wani abu irin katako ko itace ta yadda tsakaninsa akwai tazara;
A cikin wani abu makamancin wannan idan akwai najasa a ciki da wajen kasar rana kan busar da bangaren saman ne kawai shi kuma bangaren cikin ba ya tsarkaka saboda tsarkakar na saman da kuma wanda iska kan iya bi ta ciki, a wannan maganar wasu daga malamai ba su sa wannan sharadin na karshe a cikin mas’alolin tsarkakewar rana ga kasa da gini ba.
Wanna bisa fatawar IMAM KHUMAINY (KS)
Domin karin bayanai duba
1- (Rana da tsarkakar kaya, kaya da shimfidu masu najasa) tambaya ta 4805 (mauki’iy: 5249)
2- (sharadin tsarkakar bango mai najasa ta hanyar rana) tambaya ta 5002 (mauki’iy: 5259)