Please Wait
11435
Dangane da yadda ake karanta ziyarar Ashura ga wanda baya da lokacin karanta gaisuwa ko tsinuwa daya-bayan-daya, to zai iya karanta ziyarar ta wata fuska kuma ya samu ladan. An ruwaito daga Imam Hadi (a.s) ya ce: “Mai karantawa a ziyarar Ashura la’ana dari a jumla daya zai ce (Ya Allah Ka tsine wa farkon azzalumi da ya fara zaluntar…) Sannan ya sake cewa: “Ya Allah Ka tsine musu sau 99, to a hakan tamkar ya yi sau 100 ne”. Kana wanda ya karanta gaisuwa cikakkiya sau guda sannan ya ce, sau 99 a kalma daya (Assalamu Alal Husein Wa Ala Aliyub Nul Husein Wa Ala Auladil Husein Wa Ala As’habil Husein), to kamar ya karanta sau darin ne”[1]
[1] . Shifa’us sudur fi sharhi ziyaratul ashura’a, alh. Mirza abul fadal, Teheran (1273-1316 k) tahakikin sayyid Aliyu al-abdahi al-asfahani, Kum, madba’ar shuhada 1368 h sh, j 2.