advanced Search
Dubawa
11307
Ranar Isar da Sako: 2014/11/04
Takaitacciyar Tambaya
Su waye “Tabi’ai” kuma meye matsayin tafsirin sahabbai da abin da ya fifita da shi
SWALI
Suwa ake kira Tabi’ai kuma menene mihimman mafifitan siffofin tafsiri a lokacin Tabi’ai?
Amsa a Dunkule
Khadibul bagdadi yana cewa: Tabi’i shi ne wanda ya abokanci sahabi. Amma a cikin maganar da Hakim ya fadi akwai nuni kan saki ba kaidi kan tabi’i da cewa shi ne wanda ya hadu da sahabi kuma ya rawaito daga gare shi ko da kuwa bai abokance shi ba. Sannan akwai wadanda ba su isu da saki ba kaidin da aka yi ba kan tabi’ai da cewa shi ne wanda ya ga sahabi! La’akari da cewa ana kiran an yi ta’arifi sahabi da cewa shi ne wanda ya ga Manzo (s.a.w) domin akwai banbanci, saboda matsayi da daukakar ganinsa (s.a.w), wanda su sahabbai ba su da wannan matsayin. Wasu kuma sun shardanta cewa ya isar idan Tabi’i ya yi imani a kokacin da ya hadu da sahabi.
Hakika maganar masu binceke ta sassaba kan daraja da matsayin tafsiri a lokacin tabi’ai, tsakanin yin saki ba kaidi kan kin karbar abin da tabi’ai suka fitar (kin karbar abin da tabi’ai suka fitar kwata-kwata) na daga baiwar tafsiri da kuma tsakanin yin saki ba kaidi kan karbar dukkanin abin da mafassaran wannan lokacin suka fitar. Sai dai idan aka kalli abin da kallo managarci kuma aka yi masa hukuncin da ya dace bisa la’akari da sakamakon da tafsirin wannan lokacin ya bayar hakan zai sa mu rarrabe a cikin hukunci kuma ba zamu yi wa wadannan tafsirai hukunci guda ba, me kyau ko mara kyau ba, ballantana ma kallon ko wane tafsiri shi kadai a wata marhala zai sa mu fita daga kiyaye ka’idar bin diddigin wannan marhalar, bisa la’akari da sakamakon da za mu kai zuwa gare shi, idan muka karbi komai ko kuma muka kore komai daga abin da ya zo na daga wadannan tafisrai tabbas hakan zai kai mu ga watsar da da yawa daga cikin sakamakon bincike na ilimi idan har muka kore komai, da kuma fadawa cikin matsalar karbar mahangar tafsiri wacce aka tabbata ta saba da Kur'ani mai girma da kuma lafiyayyen hankali ta daya bangaren.
Kuma za’a iya lissafa mihimman mafifitan siffofin tafsirin tabi’ai kamar haka:- Na daya: fadadawa a cikin tafsiri, hakika tabi’ai sun tabo bangarorin tafsiri mabanbanta. Na biyu: tsara shi da tabbatar da shi sannan suka dawwana shi cikin takardu da alluna bayan da ya kasance a lokacin sahabbai a daidaice a cikin bakunan mutane. Na uku: konkomawa da yin Ijtihadi, wannan ita ce siffa mafi girma da mihimmanci, wacce zamanin tabi’ai ya rabauta da ita, ta yanda da yawa daga cikin malaman wannan zamanin sun taka rawa kan hakan sai suka sake yin duba da kokkomawa a cikin mas’alolin addini, wanda daga cikin akwa mas’alolin Kur'ani. Na hudu: yaduwar isra’iliyanci a wannan zamanin.
A wannan lokacin ne aka shigar da ruwayoyin isra’iliyanci masu yawa cikin tasfiri wannan kuma a sakamakon yawan ma’abota littafi da suka shiga musulunci a daidai wannan lokacin.
Amsa Dalla-dalla
Khadibul bagdadi ya ce: Tabi’i shi ne wanda ya abokanci sahabi. Amma a cikin maganar Hakim akwai nuni kan saki ba kaidi kan tabi’i bisa cewa shi ne wanda ya hadu da sahabi kuma ya rawaito daga gare shi ko da kuwa be abokance shi ba. Sannan akwai wadanda ba su isu da saki ba kaidin ganin sahabi ba kadai, kamar yanda suka iso wanjen kiran sahabi da cewa shi sahabi shi ne wanda ya ga Manzo (s.a.w) saboda matsayi da daukakar ganinsa (s.a.w), kai wasu ma sun shardanta cewa ya isar idan Tabi’i ya yi imani a kokacin da ya hadu da sahabi.[1]
Tafsirin ko ma’anar Tabi’ai
Bukatuwa zuwa tafsirin Kur'ani mai girma ta karu sosai bayan wafatin Manzo (s.a.w) lokaci bayan lokaci saboda nisanta daga lokacin da wahayi ya sauka da kuma fadadar daular musulunci ta hanyar bude kasashe, da kuma bayyanar sam’aloli na ilimi sababbi sai wani adadi daga sahabbai suka yadu zuwa wasu biranai, sai Abdullahi dan Abbas a makka shi kuma Abdullahi dan mas’udu a kufa Ubayyu dan ka’abu kuma a madina Abu Musal Ash’ari kuma a basara abuldarda’i kuma a sham, kuma suka yi ta bada darasin tafsirin Kur'ani mai girma kuma suka taka rawar gani a wannan tafarki, sai hakan ya haifar da da mai ido ta hanyar wani adadi mara yawa na tabi’ai, kuma ya kai ga bayyanar makarantun tafsirai mabanbanta, ta haka ne wannan abin gado mai tsada na tafsirin Kur'ani ya ciratu daga tabi’ai zuwa tabi’it tabi’ina kuma kiraza zuka hardace shi harasa kuma suka yi ta nakalto shi[2] . hakika wannan fadadawar (warwatsuwar sahabbai dss) ta taka babbar rawar gani wajen bayyanar makarantun tafsiri mabanbanta, kamar makarantar makka da ta madina da ta Iraki, kuma ililin tafsira na daga cikin ilimin musulunci wanda ya fara bayyana a matattarori (mahadodi na karatu) na koyarwar musulunci. [3]
Fitattun masana tafsiri daga ta’biai.  
Hakika da waya daga cikin manema ilimi sun kasance sun zabura babbar zaburowa kuma sun ci gaba a fagen neman sani da kai wa ga sanin hakika koyarwar musulunci ta hakika madaidaiciya, kuma duk da sun sami cikas na cirato koyarwar addinin daga hasken annabta kai tsaye, sai suka fake a wajen sahabbai masu girma don neman sani. Sai suka cirato ilimi daga gare su kuma suka yadi shi cikin mutane sun kasance su ne mahadar zare tsakanin rushen ilimi na farko da al’umma baki daya kai tsaye, ba kawai a wannan zamanin ba, bari dai a kowane lokaci da zamani sai suka wayi gari su ne madauka tutar shiriya ta musulunci zuwa dukkanin talikai.
Kuma wadannan bayin Allah Ta'ala gungu ne na mutane marasa adadi tamkar dai taurarin sararin samaniya a cikin dare mai duhu, kuma sun daidaitu a bayan kasa sun yadu cikin yankuna da garuruwa, manya- manya daga cikinsu sun hada da:-
  1. sa’idu dan Jubairu: 2. Sa’idu dan musayyibi; 3. Mujahid dab Taglib 4. Dawus dan kaisan; 5. Ikramata yaron dan Abbas; 6. Ada’u dan rabahi; 7. Ada’u dan Sa’ib; 8. Ibbani bin Taglib; 9. Hasanul basari; 10. Alkamaru dan kaisu; 11. Muhammad  dan Ka’abul kurzi; 12; abu Abdurrahaman Asalmi; 13. Masruku dan Azda’I; 14. Al’aswad dan yazidun nahk’I; 15. Murratal Hmadani; 16. Amirush Saibani; 17. Umar dan sharhabilu; 18. Zaidu dan wahabu; 19. Abu Sha’asa’al kufi; 20. Abu Sha’asa’al azdi; 21. Asbagu dan Nabatata; 22. Zurri dan Habishu; 23. Abu laila; 34. Ubaidu dan kaisu; 25. Rabi’u dan anasa; 26. Harisu dan kaisu; 27. Katadata dan Di’amata; 28. Zaidu dan Aslama; 29. Abul Alayata; 30. Jabirul ja’afi. [4]  
matsayin tafsirin tabi’ai
maganganun masu bincike sun sassaba kan matsayi da martabar tafsiri a lokacin tabi’ai, a tsakaninsu akwai masu kore dukkanin abin da suka fitar baki daya akwai kuma masu inganta duk abin da alkaluman mafassaran wannan lokacin su suka zana baki daya. [5]  
sai dai idan kuma kalli lamarin kallo bisa mahangar jigon ilimi kuma muka yi hukuncin da ya dace kan sakamakon da tafsiri ya fitar a wannan lokacin zamu tuke zuwa ga rarrabe wa wajen yin hukuncin kuma ba za mu yiwa sakamakon hukun kala daya ba muce ko mai mai kyau ne ko mara kyau ne ba. ballantana ma bibiyar kyawawan abin da tafsiri yake dauke da shi kadai fita ne daga fagen bincike na ilimi a cikin yin tsokaci da kalo bale na tafsirin wannan zamanin sado da abin da zai biyu bayan karbar dukkanin hadisan da kuma kore dakkanin abin da ke cikinsu na daga abin da ilimi ke kyamar sa na zabur da da yawa daga cikin sakamakon bincike na ilimi idan muka kure ingancin tafsirin baki daya, da kuma fadawa cikin matsalar lazimtawa kai karbar mahangar tafsiri ta kuskure wacce tabbas ta saba wa Alkuk’ani mai girma ta wani bangaren kuma ta saba wa hankali lafiyayye da daya bangaren. [6]
kari kan cewa hakika marhalar tafisiri a lokacin tabi’a ta gamu da jarrabawar shigowar labaran isra’iliyyanci mai yawa a cikin ilimin kalam da taffsiri da ra’ayi da bayyanar mazhabobi mabanbanta al’amarin da ya sa ya za ma abu ne mai wahalar gaske a ce tafsiri ya tsarkaka daga dukkanin gurbatattun ruwayoyin wannan lokacin ko kuma ya zama ya rushe dukkanin wadannna munannan tunaninnika musammam da yako akwai makarantu na tafsiri daban-daban a ko wacce daga madina da makka da Iraki kuma ko wacce taga cikin su ta yi riko da tata mahangar ta daban.
Madogarar tafsiri a lokacin tabi’ai
Saurare it ace hanyar farko wajen isar da tafsiri, kuma Kurani shi ne mafficin kayan aiki a wajensu a wannan lokacin wajen fahimtar fassarar littafin Allah Ta'ala domin tabi’ai sun kasance suna tafiya kan tafarkin sahabbai kuma su ne suka tarbiyantar da su kuma bisa ala’ada sai suka zama sun bi tafarkinsu duk da cewa su sun yalwata wajen bude sababbin kofofi masu fadi bisa gwargodon yalwatuwar daular musulunci da kuma shigowar al’ummu cikinsa jama’a jama’a, alhali suna dauke da ilmominsu da ladubbansu da wayewarsu, sai mahanga da budewar ido da wayewar ilimi ta kara fadada kuma fagen neman sani kan abubuwa masu zurfi ya kara fadada.
Kuma zamu iya karkasa makomar da tabi’a suka dogara da ita kan fahimtar ma’anonin zance Allah Ta'ala da bayyana manufarsa da tsikayar majefarsa zuwa madogarori masu zuwa:-
Na daya: komawa zuwa shi kansa kur’anin. Na biyu: komawa zuwa ga abin da suka cirato daga sahabbai na daga hadisan Manzo (s.a.w) kan fassarar Kur'ani. Na uku: la’akari da sababan saukar ayoyi da kuma abin da ya faru a lokutan da ayoyi ko aya ko kuma surar ta sauka da makamancin haka. Na hudu: komawa zuwa (lugga) yaran laranci shi a kan kansa musamman ma wakokin larabawa wadanda ake kira da (diwaninsu). Na biyar: nau’o’in ilimomi da kuma masaniyar da musulmai suka kai zuwa gare su albarkacin fadadar kasar musulunci da yaduwar musulumnci da dafifin da aka samu na ladubba da ci gaban da suka zo wa musulmai. [7]   
Tafsirin tabi’ai a ma’auni
Tafsirin tabi’ai ya kebanta daga tafsirin sahabbai da wasu kebance-kebance ta fuskoki kamar haka:-
Na data: fadadawa a cikinsa
Hakika tabi’a sun shiga bangarorin daban-daban na tafsiri kuma sun kutsa cikin ma’anonin Kur'ani ta bangarori da dama masu nisa a daidai lokacin da tafsirin sahabbai ya kasance ya takaitu cikin bangarori iyakakku a cikin lugga, da sha’anin saukar aya da wasu ilimomi na shari’a don kawar da abin da ya shige wa mutane duhu ta wannan bangaren kawai hakika tafsiran tabi’ai sun yi tattaki zuwa gaba a bangarori masu yawa.
Don haka hakika tafsiri a wancen lokacin ya tattaro bangaren adabi da ligga tattara wa fafada sosai haka ma tarihin ai’ummun da suka gabata da al’ummun zamanin wadanda suke makwabtaka da tsibirin larabawa, na daga tarihin garururwansu da rayuwar su daidai da abin da ya zo musu na labara, kai har ma da harasnasu da al’adunsu da daga bangaren da ya shafi Kur'ani mai girma, haka ma a wannan lokacin suka shigar da binciken ililmi akida ko kalam da ya samo asali a wannann lokacin a cikin bangaren tafsiri, kuma suka alakanta shi da da yawa daga cikin ayoyin Kur'ani kamar irin su ayoyin siffofin Allah da mafara da kiyama da makamancin haka.
Hakika wannan fadadawar ta dauki sabon salon a ciki yalwatuwa tare da tsayuwa cikin sabonin mahangogi da suke budewa a kullum duk lokacin da ilimomi da masaniyar dan adam ta fadada, kuma haka ya kawo kara masaniya kan adabobin da al’ummun da suka shiga musulunci suke da su kafin shigarsu, wdanda suka shiga musulunci jam’a-jama’a suna dauke da iliminsu da masaniyarsu kuma suka yi amfani da su wajen hidamtawa musulmai da musulunci, kuma wadannan tarin cigaban nasu sun kasance suna kara yaduwa da yaduwar sasannin musulunci.
Kuma tafsiri bai gushe ba yana kara yado da girba mutukar ilimi ya kara yawa da fadada kuma masaniyar dan adam ta kara sama. Kuma hakika yalwatuwar masaniyar biladama ta dauki kaso mai tsoka wajen iya warware murdaddun mas’alolin da suke kimshe cikin halittu da samuwa ko kuma ta zamo mai nusar da bil’adama kan wani boyayyen sirri ko sirrikan samuwa, kuma lalle ilimi da falsafa sun taka rawa mafi girma da dukkanin iyawarsu a wannan fagen.
Na biyu: tsara shi da buwauta shi da kuma maida shi a matsayin littafi.  
Tafsiri a lakacin sahabbai ya kasance kamar yanda yake a lokacin Manzo (s.a.w) ya daidaita a bakunan mutane ya yadu tsakaninsu, abin kiyaye wa cikin kirjinansu saboda takaituwar yawansa da kusancin fadinsa kuma abin takaitawa cikin ‘yan kalmomi masu buyayyon manuniya ko mai wankan jirwayen ma’ana a wancen lokacin.
Amma kasancewar sa tsararre a jere rubutacce mai shakali wanda aka maida shi litttafi wannan ya faru ne a lokacin tabi’ai da tabi’ut tabi’ina dayan su ta kasance yana bijiro da kur’ani tun daga farkon sa har karshe yana karantawa a gaban malami, yana tsayawa kan ko wace aya yana tambayarsa kanta yana mai neman sanin ma’anarta ko yana neman sanin manufarta a wajensa ko yana neman ya sanar da shi a bin da take nufe da abin da take jifa zuwa gare shi. Kuma baya wuce wa har sau ya dawwana ta cikin littafi ko ya rubuta ta a littafin rubutu ko allon da yakance yana dauke da shi, ta haka ne suka dauki ilimin tafsiri suka tsara shi suka rubuta shi a wancen lokacin,[8] bari mu yi nuni zuwa ga wasu ‘yan misalsali kan wannan:-
Mujahid ya ce: Na bijiro da Kur'ani sau uku ga Abdullahi dan Abbas ina tsayawa kan kowace aya ina tambayarsa kan abin da ta sauka kuma ta yaya ta sauka [9].
Ibni malikata ya ce: Na ga mujahid yana tambayar dan Abbas kan tafsirin Kur'ani tare da shi a kwai wani sai ibni Abbas ya ce da shi: ka rubuta har sai da ya tambaye shi kan tafsirin Kur'ani baki dayan sa [10] .
Kuma Katada yana da littafin tafsiri kuma ta yiyu ya zama yana da tubu babba ne kuma hakika Khadibul Bagdadi ya yi amfani da shi a sama da waje dubu uku.
Jabiru dan yazidu ja’afi ma yana yana da tafsiri, haka ma Hasanul Basari da Ibbanu bini Taglig da Zaidu dan Aslam da wasunsu wadanda ke da litattafai sanannu na tafsiri da ilimomin Kur'ani [11].
Na uku: nazari da ijtihadi 
Wannan ce mafi girma kima da tantantuwar da tafsirin tabi’ai ya rabauta da ita, domin wani adadi daga malaman wannan zamanin sun yi aiki tukuru suka yi nazari kan da yawa daga mas’alolin addini wanda daga ciki akwai mas’alolin Kur'ani mai girma da suke komawa zuwa mas’alar siffofi da sirrikan halitta da halayen Annabawa da Manzanni da makamancin haka sun kasance suna bijiro da su su kwatanta su da shari’a ta hankali kuma su tsage ta kan hukuncin sa mai shiryarwa, kuma idan ta kama sai su yi tawilinsa daidai da yanda zai dace da dabi’a madaidaiciya.[12]
Kuma tabi’ai ba su taba dakatawa (gazawa) ba a cikin wasu ayoyin da wan abu daga sahabbai be zo musu a kanta ba face sai sun yi  ijtihadi sun zage dantse kanta sun bayyana abin da ake nufi da ita a cikin tasfiransu. [13]
Na hudu yaduwar hadisan isra’iliyanci a wannan lokacin
A wannan lokacin ne da yawa daga cikin (hdisan isra’iliyanci) ruwayoyin yahudawa na kokarin bata musulunci suka shiga cikin tafsiri, wannan kuma ya faru ne saboda yawan wadanda suka shiga musulunci daga ma’abota littafi a daidai wannan lokaci alhali kissoshin malamam coci da uskifai ba su gushe ba suna cuke a kwakwalensu na daga abin da yake komawa zuwa lokacin da aka fara yin halittta da sirrikan samuwa, da asalin samar da samammu da labaran[14] al’ummun da suka gabata da hadisan annabawan baya da da yawa daga cikin labaran manyan magabata da masu bi musu baya na daga abin da ya zo a Attaura da da sauran litattafai da suka gabata.   
 
 
 

[1] Khadibul bagdadi, Ahmad dan Ali a cikin kifaya fi ilmid diraya shafi 22 madina, maktabatul a lamiyya, ta tare da tarihin bugawa ba. Ibni Kasir badamashke, imsa’il dan umar a cikin ikhtisari ulumul Kur'ani shafi 91 bairul darul kutubul ilmiyya bugu na biyu na tarihi; Suyudi jalalddin , a cikin tadwinur wawi fi sharhi takribun nawawi wanda farabi abu kutaiba nazr Muhammad  ya yi wa tahkiki j 2 shafi 699 ba tarihi, darul daiba; Tahawani, zafr, kawa’id fil ulumul hadis sh 48 arriiyadh, sharikatul abikan. 1404.
[2] Muhammad  hadi ma’arifa, al-tafsirul wal mufassirun, mukaddimar mai yadawa . ka duba shahrudi, abdulwahab, argon aasimani, Jastari dar kur’an, irfan wa tafasiri irfan, risht, alkitabul mubini bugu na farko 1832. Shakir Muhammad  kazim, mabani  wa wawishahai tafsiri, shafi 274. Almarkazil alami lilulumil islamiyya bugu na daya . 1382. Marwati shaharab, fajuhishi kan tarihin tafsirin Kur'ani shafi 176, Tehran bugu na daya 1381.
[3] Ka duba zahabi, Muhammad  Husain, al-tafsir wal mufassirun, j1 shafi 100-127 bairut, daru ihya’i yturasil arabi ba tarihi. 
[4]  Ma’arifa, Muhammad  hadi al-tafsir wal mufassirun fi saubihil jadidi, j1 sha 132 mashhad aljami’atul ridhawi lil ulum al-islamiyya buguna daya 1418. Assabuni Muhammad  dan Ali a cikin tibyan fi uluml Kur'ani shafi 77 bairut, alamul kitab bugu na farko 1405.
[5]  Ka duba al-tafsir wal mufassirun fi saubihil jadidi j 1 sh 423 – 432 al-tafsir wal mufassirun j 1 sh 128.
[6] Mu’addib sayyid Ridha roshahri tafsirul kur’an shafi 130 – 146 kom isharak bugu na farko  1380.
[7] al-tafsir wal mufassirun fi saubihil jadidi j 1 sh 447 – 451.
[8]  Masdarin daya gabata shafi na 432 – 433.
[9] Albalkhi mukatil dai salaiman tafsiru mukatil j 5 shaf 65 bairut dari ihya’I turas bugu na daya 1423. Suyudi, jalaluddin alitkan fi ulumil Kur’an j2 sh 473. Bairut darul kutub arabi bugu na farko  1421.
[10]  Dabari, muhamma dan juraihi, jami’ul bayan fi tafsiril Kur'ani j 1 sh 31 bairut darul ma’rifa bugu na daya 1412.
[11] al-tafsir wal mufassirun fi saubihil kashib j 1 sh 434.
[12] Masdarin daya gabata j 1shafi na 435.
[13] Fajuhishi firamuni tarihi tafsirul Kur'ani  shafi 178 – 179. al-tafsir wal mufassirun fi saubihil kashib j 1 sh 435.
[14] Ka duba al-tafsir wal mufassirun fi saubihil kashib j 1 sh 446. Argun asimani, jastari dar kur’an, irfar wa tafasiriirfani sh 100, Fajuhishi firamuni tarihi tafsirul Kur'ani  shafi 161.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa