advanced Search
Dubawa
9234
Ranar Isar da Sako: 2012/05/05
Takaitacciyar Tambaya
Me ye matsayi da girman da ke qarqashin xabi’u a fagagen wassanin motsa jiki?
SWALI
Me ye matsayi da girman da ke qarkashin xabi’u a fagagen wassanin motsa jiki?
Amsa a Dunkule

Musulunci bai bar kowanne vangare daga cikin vangarorin rayuwa kara zube ba saboda kasancewarsa gamammen addini ga dukkan duniya, matuqar wannan vangaren zai taimaka ma xan Adam a yunkurinsa na samun kamalar da zata masa jagora zuwa ga rabautar duniya da lahira.

Kamar yanda ya ba da muhimmanci sosai a vangaren kiwon lafiya (jiki da ruhi ) da kuma vangaren motsa jiki domin yana taimakawa don ganin an cimma manufa mai muhimmanci.

Wajibi ne a kan ‘yan wasan motsa jiki su tabbatar cewa sun yi amfani da dukkan salon da ya dace wanda yake kunshe da kyakkyawan yanayi, domin amfani da shi a fagagen motsa jiki da farfajiyoyinta a duk sanda dama ta samu.

Akwai wasu sashin ayyuka da kyawan halaye da ya kamata xan wasa ya siffantu da su a fagen wasa kamar: Yaki da zuciya mai yawan ingiza mutum, Yafiya da rangwame, saukar bako bisa mutumci da kuma girmama abokan karawa d.s.

Amsa Dalla-dalla

Daga cikin jerin abin da xan Adam yake ta qoqarin samu ko da yaushe shi ne; lafiyar jiki da ta ruhi. Addinin musulunci kuma bai qasa a gwuiwa ba wajen kula da kowane irin vangare daga ckin vangarorin da zasu kai mutum ga kamala don cin nasarar duniya da lahira. Saboda gamewarsa da kuma kasancewarsa adddini na dukkan duniya. Kamar yanda ya ba da muhimmaci sosai don kare lafiyar al’umma da kuma muhalli. Ba shakka musulunci ya kula da sashin motsa jiki matsayin shimfida don kare lafiyar jiki da inganta shi.

Haqiqa harkar motsa jiki ta bunqasa a wannan zamanin ta yanda ta sami ikon tattaro miliyoyin yan wasa koma fiye da haka, na matasa goggagu a fannoni dabam-dabam. Kai bama haka ba, ita harkar wasannan tana da wata rawa da take takawa mai matuqar tasiri wajen xinke varakar qasa da qasa. Da kuma inganta alaqar makwaftaka ta kasa da kasa.

Haka nan kuma wasan motsa jiki na fayyace (mana) al’adu da xabiun mutanen qasashe da al’ummu, kyawawansu da kuma munana. Kuma ita kamar mudubi ta ke ta hango mana kyawawa da munanan xabiun mutane a cikin qasa. (1)

Al’adun wasanni suna shiga qarqashin al’adun nan take kai tsaye wacce take taka rawa babba wajen kimanta matsaya, aiki da xabiun qwarewa; tsara dokoki; tsayar da da hukunci; da sauransu (2)

Akwai wani tsokaci game da harkar nan ta motsa jiki, kan cewa ita wasu taron nishaxoxi na jiki da kuma nuna gwaninta ta ala’adar jiki wacce take qarqashin dokoki gamammu da nufin jin daxi da shakatawa da gasa. Da kuma nishaxi motsa jiki na xai-xaiku da samun gogewa a fagen wassani da samun wasu sashin sifofi ko kuma tabbatuwar dukkan waxannan abubawa. A fili yake cewa shi wannan batu na wasanni yana vangaren ta’arifin motsa jiki ta vangaren munufofin da ake son cimmawa.

Sai dai fa akwai wanda ya zurfafa bincike game da muhimman abubuwan da bamu fada ba, shi kuma ya yi tsokaci ne ta janibin xabi’u a harkar motsa jiki, kamar haka;

Kuruciya, gasa, taimakekeniya, dattako, yaudara, amfani da abubuwan nishaxi, halayen masu gwaninta, Dangantaka tsakanin mai horar da yan wasa da yan wasa da sauransu (3).

Sannan kuma babu shakka ita qimar kyawawan xabi’u tafi qimar abin duniya nesa ba kusa ba! Wannan ma shi yasa zaka ga kowa yana fatan samunta, kuma zaka ga yana runsuna mata gami da yaba mata ko ba a datar dashi tsayuwa da it aba. Abin da muke cewa a nan shi ne wajibi ne a tabbatar da dukkan sakon gama gari wanda ke kunshe da kyakkyawan yanayi wacce za a iya aiwatarwa a fagagen wasan motsa jiki da farfajiyoyinta duk lokacin da dama ta samu. Ko kuma muna iya cewa: ya kamata ga masu wasan motsa jiki da su yan wasan kansu su ba da muhimmanci a vangaren ‘’ruhi’’ da kuma ma’anar mutum ta haqiqa.

 Kar kuma a taqaita a vangaren gangan jiki kawai. Saboda akwai kakkarfan alaqa Tsakanin jiki da ruhi, shi yasa musulunci ya kula da wannan ta mahanga tabbatacciya, bai kevance jiki shi kadai ba, ya bar rai. Ko kuma ya damu da rai ya bar jiki ba. A’a kamar yanda ya ba da muhimmanci ta bangaren zahirin jiki da gavovi to ya kuma qarfafa vangaren ruhi, akasin haka ya inganta. Yayin da ya tsara ka’idodi da dokoki wanda zasu kai ga cimma waxannan manufofi a hade. Kamar azumi da salla da addu’a d.s. in ko ba haka ba to kulawa da gangar jiki da gavovi baya cancantar dukkan wannan kulawar. Ba kuma zai fitar da mutum daga bangaren zahirinsa na gangan jiki ba.

Haqiqa imam khomaini (ks) ya qarfafa waxannan janibobi biyu na asali a lokacin da ya haxu da matasa yan wasan motsa jiki lokacin yana raye, har ma yake cewa: ‘wajibi ga matashi gwargwadon yanda ya kula da jikinsa da qarfafa gavovinsa, to haka nan ma janibin ruhinsa da baxininsa. Sannan ya kuma tunatar da matasan abin da yan wasa Iran suka kasance suna aikatawa a zamanin baya, na buxewa da Bismihi ta’ala da ambaton tawassuli da Imam Ali (as) har ya zama an san su da wannan sifa xin a wancen lokacin.4

Abu muhimmi a nan shi ne ya zama ga cibiyoyin wasannin motsa jiki da kuma wuraren wasanni su tantance nauyin da ya hau kansu na vangaren kyautata xabi’u, sannan kuma a bunqasa su, a kuma watsa su cikin ruhin matasan da kuma tunaninsu. Saboda su waxannan cibiyoyin na wasanni idan ya zama su da kansu ba su da qa’idoji da dokoki na kyayatata xabi’u wanda zai rinka masu jagoranci to fa matashi ba zai iya tantance matsayin sa ba ta vangaren halaye a wannan fagen daga me haxari, ka ga ke nan matashi zai shiga filin wasa ba tare da guzurin komai ba a fagen wasan.

Zamu yi qoqari mu yi nuni zuwa ga sashin wasu ayyuka da nauyin da suka kamata xan wasa ya siffatu da su a xabi’unsa, musamman ma a fagen wasa. Su ne na farko:

  1. Yaqi da rai mai yawan tunzurawa; wannan na nufin cewa matashi xan wasa yana da qaqqarfar vuqata ya zama ya yi rinjaye ga ransa, ta hanyar dankwafe ta a kan abin da take so da sha’awowi masu tunkuxa ta ta fuskar da ba ta dace ba. Domin takan angiza mai ita ya faxa cikin tarkon savo da mummunan aiki, to wannan al’amari ko da bai kevanta ga ‘yan wasa kawai ba ya game kowa da kowa, sai dai yan wasa sun fi vuqatarsa saboda yanayi na musamman da suke samun kansu kuma ga abubuwan rudu barkatai, sai sun dage sun yaki zuciyarsu fiye da waninsu.

Akwai ruwayoyi da yawa a wannan fagen waxanda suka zo daga wajen ma’asumai (as) zamu ambato qaxan daga cikinsu.

  1. An ruwaito daga annabi (saw) ya ce: ‘’Qaqqarfa ba shi ne wanda ya yi kaye ba, amma qaqqarfa shi ne wanda yake mallakar zuciyarsa lokacin fushi’’
  2. An ruwaito cewa manzon Allah ya wake wasu mutane a cikinsu akwai wani mutum yana xaga dutse, ana kiransa Dutsen Gwaraza alhalin su kuma suna ta mamakinsa, sai Annabi (saw) ya ce; mene ne wannan? Sai suka ce wani mutum ne yake daga dutse, Sunansa Dutsen Karfafa’’. Sai ya ce; Shin ba na ba ku labari da abin da ya fi qarfi ba? Wani mutum ne sai wani ya zage shi, sai ya haqura ya rinjayi zuciyarsa, ya yi galaba a kan shaixaninsa da na abokin faxansa.’’6
  3. Sarkin Muminai (as) ya ce: ‘’Kada ka yi rangwame ga zuciyarka wajen biyayya ga son rai, da fifita jin daxin duniya, sai addininka ya vaci ba kuma zai gyaru ba.’’7
  4. An ruwaito daga Abi Abdallah (as) cewa: Manzon Allah ya aika da bataliyar yaqi, yayin da suka dawo sai ya ce, ‘’Maraba da mutanen da suka gama qaramin jihadi kuma ya rage akansu babban jihadi’’ Sai aka ce ‘’ Ya Ma’aikin Allah mene ne babban jihadi? Sai ya ce; ‘’shi ne yaki da zuciya’’8

Na biyu: Rangwame da Yafiya: daga cikin abubuwan da suka zama wajibi ga matashi xan wasa ya yi ado da su, su ne mallakar qarfin halin rangwame da yafe laifi, lokacin da ya zama maxaukaki mai rinjaye a kan abokin karawarsa, ka da ya musguna masa har ya zama ya takura shi fiye da qima, saboda hakan na iya kai shi ga cutar da shi, amma ya yi rangwame, domin nuna godiya ga Allah Maxaukaki a kan rinjayen da ya ba shi a kan abokin karawarsa, kada ya musguna masa har ya zama ya takura shi fiye da kima, saboda hakan na iya kai ga cutar da shi, amma ya yi rangwame, domin nuna godiya ga Allah maxaukakin sarki.

An ruwaito daga Sarkin Muminai (as) yana cewa ‘’Kka haxiye fushinka, kayi rangwame lokacin da ka sami iko, ka yi hakuri yayin fushi, ka kuma kauda kai tare da rinjaye sai ka zama mai kyakkyawan karshe’’ (9).

Na uku: Nisantar girman kai: bai kamata xan wasa don ganin cewa yana da karfin jiki ya rinqa yin girman kai da xagawa a kan wasu ba, da kuma ruxuwa da karfinsa na jiki: ba haka ba! Ya wajaba ya sani fa cewa wannan ni’imar mayalwaciya a gare shi ta Allah ce ya bashi kyauta, ke nan ya kamata ya yi tunaninta ya kuma nemi qarin wata daga wajen Allah tare da qasqan da kai (tawali’u) ya kuma yawaita faxin ‘’Bihaulillahi wa kuwwatihi aqumu wa aqudu’’ a cikin sallar sa.

Tarihi na gaya mana cewa, Imamu Hussain (as) ya kasance yana yawaita fadin wannan kalmar ‘’La haula wala quwwata illa billah’’ (10) idan zai kai hari ga dandazon makiya.

Kuma haqiqa kur’ani ya tunatar game da wannan al’amarin a cikin fadarsa maxaukaki ‘’haqiqa dukkan karfi ya tabbata ga Allah baki daya’’ (11) don haka babu dalilin da zai sa xan wasa ya ruxi kansa da abin da yake dashi na karfin jiki da gavovi har ma ya manta da ubangijin da ya bashi wannan ni’imar lallei wajibi ne bisa hali na kwarai ya sarrafa wannan qarfin a hanyar da ta dace.

A kan haka ya zama tilas gare shi ya nesanci ruxu domin karshensa rushewa da tavarvarewa, haqiqa Amirul muminin (as) ya yi nuni zuwa ga wannan batun a cikin sashin wasu hikimominsa yayin da yake cewa ‘’Illar jarumi shi ne tozarta niyya. (12) an karvo daga gare shi kuma ‘’illar qaqqarfa takurawa abokin husuma’’ (13).

Na hudu: samartaka da tsare gida bisa mutumci yana daga cikin sannannun al’amura, a fagagen wasanni kowa vurinsa ya yi rinjaye a kan abokin karawarsa. Wannan kuma wani al’amari da yanayin wasanni da gasa ke farlantashi, yana da rawar da yake takawa wajen bunqasa da kuma cin ribar harkar wasa. A vangaren jiki da ruhi. Amma sai dai ya kamata gasar ta kasance cikin mutumci da gujewa duk abin da zai tava mutumcin sana’a) kuma ya wajaba ga xan wasa ya yi gwagwarmaya da abokin karawarsa bisa la’akari da dokoki da sharuddan da aka tsara ga mai masauki.

Bugu da qari kuma ba makawa gare shi ya rinqa kallon abokin karawa kallon qauna da girmamawa, kar ya tsane shi ko ya qullace shi a cikin zuciya. Ka da ya xinga tunanin cin nasara ko ta yaya, ko da kuwa za a keta alfarma da zub da mutunci.

  1. Duba littafin (majmu’atun-min-albahasin) al akhlaqul-amaliya- (akhlaq karbardiy)sh-429.
  2. Masdarin da ya gabata sh-32
  3. Masdarin da ya gabata sh-80 da kuma sh-417-420.
  4. Sahifat-al-imam, juz-18, sh-151.
  5. Almajlisiy. Muhammad Baqir. Bihar-al-anwar juz 74 sh-153 Mu’assasat al wafa, Beirut, 1404 Hij, kamari; alharraniy alhassan bn Shuubat, Tuhuf-al-uqul, sh47 nashr Jamaatul mudarrisin, qum, 1404 hij kamari abi farras warram, mujmuat warram, juz-1, sh122 nashr maktabat al-faqech, qum.
  6. Majmuat warram juz-2 sh10.
  7. Altamimy al’amudiy, Abdul Waheed bn Muhammad, Gurar-al hikam wa durat-al-alkalim. Sh306, nashr daftar-al tablig-al-islamiy –qum 1409 hijra kamari.
  8. Nahjul balagah. Sh159 intisharat darul hijrah, qum.
  9. Alsayyid bn tawus, alluhuf-ala-alqala-al-tufuf sh 119. Nashr jehan tehran bugu na farko 1348 shamsi.
  10. Sura baqara-165.
  11. Gurar al hikam-wa durar-al-kalim, shafi259
  12. Gurar al hikam-wa durar-al-kalim, shafi347

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa