Please Wait
11441
- Shiriki
Amir ya bayyana tare da bayani wannan cikin huduba ta uku a nahj da aka sani da shakshakiyya, kamar yadda ya zo daga cikinta “amma wAllah (SW)i ya sanyata … inda a karshe yake cewa … faufaufau (haihata haihata) wancen tsanani ya faru kuma ya kare”
Amir ya bayyana tare da bayani wannan cikin huduba ta uku a nahj da aka sani da shakshakiyya, kamar yadda ya zo daga cikinta,
“amma wAllah (SW)i wane ya sanya rigar halifanci alhalin ya san cewa mjatsayina a kanta ya kai matsayin kudubi, ruwa mai ambaliya ya zubo daga gareni har zuwa tsayin da tsuntsu ba zai iya kaiwa ba, na sanya labule (shinge) tsakanina da kujerar halifanci alhali nine mafi cancanta da ita kuma wanda yafi kowa ganeta (saninta).
Sannan na fara tunanin zan barta ne kokuma na hakura da ita (sai naga hakuri yafi) na hakura alhali hakurin yana da kunci kamar misalin makanta cikin mafi duhun daren da mumini zai zamto na yunkurin fita daga cikinsa har zuwa komawarsa ga Allah (SW).
RINJAYAR DA HAKURI
Sai naga cewa hakuri shi ne mafi cancanta naga na zabi yin hakurin, duk da cewa yana da tsanai kai kace ana sokowa mutum allura a ido ko ace ya yi kama da kisa ta hanyar shakewa, sai nake kallo yadda ake yin watandar ganimar gadona (halifanci) har zuwa karshen na farkon, sannan kuma ya kara mikata zuwa hannun wani a bayansa (umar dan kattab), sai imam ya rero baitukan wakar alasha da ke fadin ‘kwanakina na wucewa a bayan rakumi (cikin wahala) alhali akwai ranaku masu dadi ranakun rayuwar dan uwana Jabir.
Akwai abin mamaki kn wannan abu na mikata ga wani can bayan mutuwarsa, koda yake babu mamaki hakan wadannan biyun sun tsara rabata ne a tsakaninsu, shi kuma wannan dayan ya sanya halifanci cikin karfin hali inda akwai matsaloli da kura kurai da yawa a zamaninsa cikinta kai kace rakumine da babu mai jansa kuma tare da shi akwai majanyi daurarre, idan yaja madaurin zai iya tsaga masa kofar hanci, idan ka duba ana jagorantar mutane bias rashin tsari ko rashin kula, hauka, duk kuma ta barauniyar hanya. Duk da haka naci gaba da hakuri tsawon lokaci cikin wannan yanayi mai tsauri har shima ya kama hanyarsa zuwa ga Allah (SW), shima kuma ya kara sanyata a hannun wasu jama’a da ya ce nima ina daga cikinsu duba irin wannan tufka da warwara amma zamu zabi mulkine ta hanyar shawara wato shura (me zanyi da wani abu wai shura) yaushene dayansu ya samu kokwanto kaina da har zan zama daya da wadancen duk da haka na hakura da waccen faduwa na kaskanta yayin da suka kaskanto na hau hayinda suka hau sama, daya daga cikinsu ya juyamin baya saboda kinsa da hassada a kaina.
Sauran kuma suka juya wani bari sabida surukantarsa ga wani da ma wasu abubuwan daban daban har sai da na ukun ya hau kanta (kujerar bhalifanci) tare da cakuda abincin dabbobi da kashinsu wuri daya. Ta danginsa kanne da yayye da yan uwa (wato banu umayya) ya zauna yana hadiyar dukiyar Allah (SW) kamar mayunwaci rakumin da ke cinye ganyayen da ke bakin idon ruwa ghar sai da idaniya bakina ta tsinke, aikinsa sai da ya halakashi hadamarsa ta kaishi faduwa kasa wanwar.
YI WA IMAM ALI(a.s) BAI’A
A wannan lokaci nayi mamaki da nayi mamaki da mutane masu yawa ke kokarin bubbugowa zuwa gareni, suka tunkaro uwa gareni ta kowane bangare kai kace wani garken kurayene (zuwaga kanshin nama) suka rufeni kamar sa bi takan Hassan da Husain (a.s) har sai da gefen kafaddna suka yage kai kace sun kewayeni kamar garken dabbobi (tumaki da akuyoyi) ne, a yayin da na kalli tsarin gwamnati wani bangare ya balle wani ya yi tawaye wasu kuma sun fara gudanar da abubuwa bisa kuskure, kamar basuji fadin allh cewa ba “wancen gida na lahira mun sanyashi ga wadanda ba su bukatar daukaka a nan duniya kuma basa son barna, kuma kyakyawar makoma nag a masu tsoron Allah (SW)” haka ne wAllah (SW)i sunjita kuma sun ganeta, duniyacu take bayyanar musu kyalkyali a idonsu kuma kayace kayacenta ya lalata su gashinan ai duk wanda ya shuka tsaba (domin ta futo ta girma) kuma ya (bar iska na gudanawa) kirkiri yanayi, idan da mutane ba su zo ba da tsayuwar hujja da samuwar mai taimako Allah (SW) ba zai karba daga malamai ba haresai sunki yarda da hadamar (zarin) azzalumi da na tsike igiyar hlifanci a kan kanta, kuma da na bawa dayan irin yadda nayiwa dayan (na farkon) da kunga cewa wannan duniyar taku tafi min nisanta daga atishawar akuya.[1]