Please Wait
7126
- Shiriki
Mafi dadewar madogara game da wilaya ko jagoaranicn malami da muke da ita sun hada da littafin Mukni'a na sheikh mufid ne, ya kawo wannan bahasi a babin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna a matsayin daya daga cikin abubuwan da suka hau kan malami.
a- babbar daraja ita ce umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna
b- Tsayar da haddodi
c- Gudanarwa da zartar da hukunce-hukunce
d- Jihadi da yaki da kafirai
e- Tsayar da salloli kamar juma'a, sallar idi, sallar rokon ruwa, sallar dimuwa
f- yin hukunci da alkalanci
Haka nan a bahasin Anfal, ya kawo cewa; tasarrufi a cikinsu ba ya halatta sai da umarnin imami adali.
Mafi dadewar sanadi da madogara da muke da ita kan jagorancin hukuma karkashin malami shi ne littafin nan na Mukni'a na sheikh Mufid (333 ko 338 – 413) wanda yake daga malaman karni na hudu ko na biyar hijira.
Shi ne ya kawo wannan bahasin a babin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna a littafinsa na Mukni'a
Bayan ya kawo martabobi da matakan yin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna tun daga mafi girman mataki na kashe mutum zuwa ga haifar masa da rauni sai ya kawo wannan bayani yana mai cewa:
Mai umarni da kyakkyawa ko hani ga mummuna ba shi da hakkin kisa ko jikkatawa, sai dai idan shugaba ne ya ba shi damar wannan aikin ya dora masa wannan matsayin. Sannan sai ya ci gaba da cewa: Amma mas'alar gudanar da haddodin Allah, suna kan sarki kuma shugaba ne jagoran musulunci wanda aka kafa shi ta bangaren Allah. Wadannan kuwa su ne imamai na shiriya daga alayen manzon Allah (s.a.w), ko kuma wadanda imamai suka nada su a matsayin shugabannin al'umma wanda wannan yana komawa zuwa ga malamai ne masana daga masu biyayya garesu[1].
A wannan jumlolin zamu ga akwai tsoron cewa kada a samu hukumar zalunci wacce ba ta komawa zua ahlul-baiti (a.s) a cikin maganar sheikh mufid, don haka da farko sai ya fara magana kan sarki kuma jagora da aka kafa shi ta fuskancin Allah madaukaki a matsayin makoma da zartar da kisa ko raunatawa domin tsayar da umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna, sannan sai mas'alar tsayar da haddodin Allah da ya kawo a matsayin babban misalin tsayar da umarni da kyakkayawa da hani ga mummuna[2].
Kuma da maimaita wannan lamari na cewa nauyin hakan yana kan jagoran musulunci ne wanda aka kafa daga wurin Allah madaukaki muna iya nuni da wannan kamar haka ke nan:
1- Imamai ma'asumai wadanda kai tsaye aka kafa su daga wurin Allah madaukaki domin gudanar da tafiyar da lamarin al'umma kai tsaye.
2- Jagororin da imamai masu tsarki suka ayyana su suka kafa su domin tafiyar da lamarin al'umma da jagarancin siyasa, da tsayar da haddodin Allah (s.w.t).
3- Malamai na shi'a da imamai masu daraja (a.s) suka kafa su domin jagorantar lamarin al'umma da tsayar da haddodin Allah (s.w.t).
Da wannan ne zamu ga sheikh mufid bayan ya yi bayanin lamarin hukumar jagoranci da tafiyarwar imamai ma'asumai (a.s) wanda lamari ne sallamamme gun shi'a, sai ya kawo bayanin da yake nuni ga abin da ya hada da wakilai na musamman na imamai da suke kafawa domin tafiyar da lamurran al'umma kamar irin su; Malik Ashtar, a lokacin imam Ali (a.s) ko kuma wakilai hudu a lokacin imam Mahadi (a.s), ko kuma wakilai na gaba daya wato malamai a lokacin fakuwar imamai (a.s) da boyuwar imam Mahadi (a.s).
Ko da yake shi sheikh Allah ya yi masa rahama da shi da malamai masu yawa ba su samu damar gudanar da hukuncin Allah ba (saboda yanayi bai ba su wannan damar ba), don haka ne zamu yi nuni da wasu lamurra a nan kamar haka:
Idan da malamai ya san cewa zai iya tsayar da haddi kan yaransa da ‘ya’yansa kuma yana ganin akwai rashin tsoron zaluncin masu mulki a kansa, to ya zama dole ya yi hakan[3].
Wannan maganar tana iya sanya kwararar hawaye a fuskar mutum saboda tana nuni zuwa ga zaluncin da shi’a suka fuskanta a tsawon tarihin musulunci, kuma wannan mas’ala a fili tana nuni da cewa mas’alar jagorancin malami ta kasance a fikirar mazhabin Ahlul-baiti (a.s).
Hakan nan sheikh Mufid yana kawowa cewa: Lamarin gudanar da dokokin Allah wajibi ne ga dukkan malamin da ya samu ikon gudanar da hukunci da wani mai hukunci ya kafa shi a kai, ko kuma aka ba shi kula da lamarin wasu jama’a.
To ya zama wajibi a kansa ya tsayar da hukuncin Allah, da gudanar da hukuncin shari’a, da umarni da kyakkyawa, da hani ga mummuna, da jihadi da kafirai[4].
Wato da wani sarki azzalumi zai ba shi matsayi da zai iya amfani da shi wurin gudanar da hukuncin Allah to ya zama masa wajibi ya karbi wannan matsayin domin ya tsayar da hukuncin Allah, wannan kuwa yana nuni da wadannan abubuwa hudu ke nan da suka hada da:
1- Tsayar da haddin Allah
2- Zartar da hukuncin shari’a da gudanar ita
3- Umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna
4- Jihadi da Kafirai da kare daula[5].
Kamar yadda zamu ga sheikh mufid yana mai karawa da cewa: Idan Malamai zasu kubuta daga sharrin ma’abota fasadi, to sai su yi sallar jam’I tare da ‘yan’uwansu (‘yan mazhabar Sunna) a sallar juma’a, da idodi, da neman ruwa, da kisfewa, kuma su yi sulhu da gaskiya tsakanin sauran musulmi da suke da sabani idan babu wani sheda a kai, kuma duk abin da aka dora wa alkalai na hakkin hukunci to ya hau kansu. Domin imamai (a.s) sun fawwala wa malamai wadannan lamurran matukar zasu iya gwargwadon ikon da suka samu kamar yadda ya zo a ruwayoyi masu inganci[6].
A bahasin “Amfal” wacce take ta manzon Allah (s.a.w) da wasiyyasa (a.s) ce, zamu ga cewa sheikh mufid yana kawo cewa wannan lamari ne na manzon Allah (s.a.w) da kuma masu maye gurbinsa, sai yake cewa: Babu wani wanda zai iya tasarrufi cikin amfal sai da izinin imami adali[7].
Daga wannan ne zamu iya fahimtar cewa abin da ya zo a babin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna sheikh mufid shi ma kamar sauran malaman shi’a ya yarda da cewa “malami adili” shi ne wanda hukumarsa take karbabbiyya yardajjiya a wurin Allah, wato yana nufin ko dai Allah ya kafa shi kan wannan matsayin kai tsaye, ko kuma wadanda Allah ya kafa ne su ma suka kafa shi.
A shi’anci ma’anar azzalumin jagora ko azzalumin sarki da sauran kalmomi irin wadannan suna nufin jagoran da hukumarsa ba ta da wata madafa daga umarnin Allah madaukaki, don haka biyayya ga irin wannan jagora ba ta halatta ba a shar’ance. Bisa wannan ne ma kalmar jagora adali ba kawai tana nufin jagora mai adalci ba ne, sai dai ma ta hada duk wata hukuma da take da madogara yardajjiya daga shari’a[8].
Karin Bayani:
1. Mahadi Hadawi Tehrani, Wilayat wa Diyanat, Cibiyar Al’adu ta Khaneyye Khirad, Kum, Bugu na biyu, 1380.
[1] Sheikh Mufid, Al’Mukni’a, shafi: 810.
[2] Wasu suna ganin gudanar da dokoki sun shafin hukuncin kotu a hukumar musulunci ne kawai, sai dai a fikihu ya shafi duk wani warware matsala da sulhuntawa da hukunci tsakanin mutane.
[3] Sheikh Mufid, Al’Mukni’a, shafi: 810.
[4] Sheikh Mufid, Al’Mukni’a, shafi: 810.
[5] Wannan yana nuna ya hada har da fara jihadi ke nan.
[6] Sheikh Mufid, Al’Mukni’a, shafi: 811.
[7]Sheikh Mufid, Al’Mukni’a, shafi: 279.
[8] Duk da suna daga sharuddan jagora adali.