advanced Search
Dubawa
6879
Ranar Isar da Sako: 2006/05/22
Takaitacciyar Tambaya
mece ce alakar jagorancin malami da jam'iyyu?
SWALI
mece ce alakar jagorancin malami da jam'iyyu?
Amsa a Dunkule

Kungiyoyin siyasa, da ma'anar wasu jam'iyyu masu iri-iri akwai su a cikin kowace al'umma tun zamanin da. A yanzu ana ganin jam'iyyun siyasa a matsayin wani abu na tarayyar mutane da 'yancin zabe ne. bisa wannan asasin ne ya zama dole mu kalli wannan lamari a matsayin wani abu mai canjawa wanda yake yana da alaka da sharadin zamantakewar al'umma, siyasa, da al'adu.

Idan samuwar jam'iyyu ya zama kamar sauran abubuwa ne da suka shafi dokokin da matukar akwai maslaha da ta wanzu da karfinta kuma babu wani canji da zai faru cikin dokokin asasi da bisa sabuwar maslaha, to zasu ci gaba da karfinsu.

Jam'iyyun da ake da su suna wakiltar ra'ayoyin mutane ne, kuma suna da hadafin ci gaban hukumar musulunci ne, don haka kungiyoyin jam'iyyu suna da alaka ne kamar irin ta mutane da jagora malami.

Kuma daya daga cikin aibin yin kungiyoyin jam'iyyu shi ne mayar da amfanin al'umma ya koma kasan na jam'iyyun siyasa, don haka ne sai a rusa amfanin al'umma saboda na jam'iyya, wannan lamarin kuwa ba a yarda da shi ba a tsarin musulunci haka ma duk wani tsari na hankali ba zai yarda da wannan ba.

Amsa Dalla-dalla

Kungiyoyin siyasa da ma'anar da aka kawo masu jama'u daban-daban a kowace al'umma tun da can akwai su. Amma kungiyoyin siyasa da wannan sabowar ma'anar ta yanzu, babu makawa, sun faru ne sakamakon tsarin dokokin zabe na majalisu ne[1]. Don haka da wannan ma'anar ne aka samu abin da ake kira ci gabban zamni tun daga zamani sabuwar haihuwa da aka fi sani da juyin juya halin turai, daga nan kuma sai wannan ma'anar ta mamaye duniya ta kuma fadada.

Yanzu samuwar kungiyoyin siyasa wani abu ne da yake nufin tarayyar mutane da 'yancin siyasa ne. Bisa wannan asasin ne ya zama dole mu kalli wannan lamari a matsayin wani abu mai canjawa wanda yake yana da alaka da sharadin zamantakewar al'umma, siyasa, da al'adu.

Idan samuwar jam'iyyu ya zama kamar sauran abubuwa ne da suka shafi dokokin da matukar akwai maslaha da ta wanzu da karfinta kuma babu wani canji da zai faru cikin dokokin asasi da bisa sabuwar maslaha, to zasu ci gaba da karfinsu.

Jam'iyyun da ake da su suna wakiltar ra'ayoyin mutane ne, kuma suna da hadafin ci gaban hukumar musulunci ne, don haka kungiyoyin jam'iyyu suna da alaka ne kamar irin ta mutane da jagora malami.

Ko da yake tarihin kasashe daban-daban daga cikin hatta da Iran yana nuna cewa ra'ayoyin mutane a gudanarwa a fagage daban-daban suna tare da taron jama'a ne, sau da yawa kadan ne akan same shi da yanayin kungiyancin jam'iyyun siyasa.

Ta wani bangaren kuwa zuwa yau a cikin kasar nan ta Iran sau da yawa ba kasafai ake samun ma'anar jam'iyyu ba da ma'anar hakika, wannan kuwa yana nuna mana cewa yawancin akwai kungiyoyi ne na cikin da suke da hadafofi daban-daban ba tare da an samu wanta ma'ana ta daban ta mas'alolin siyasa ba, da wannan ne aka samu cewa jam'iyyu ba su samu karbuwa ba cikin mutane, kuma abin da ya faru a Iran ba sunan shi jam'iyya ba.

Kuma daya daga cikin aibin yin kungiyoyin jam'iyyu shi ne mayar da amfanin al'umma ya koma kasan na jam'iyyun siyasa, don haka ne sai a rusa amfanin al'umma saboda na jam'iyya, wannan lamarin kuwa ba a yarda da shi ba a tsarin musulunci haka ma duk wani tsari na hankali ba zai yarda da wannan ba.

Karin bayani:

1. Mahdi Hadawi Tehrani, Wilayat wa Diyanat, Mu'assar Al'adun Khaneye Khirad, Kum, bugu na biyu, 1380.

[1] Abul fadhl kadi, Hukuke asasi ba na hadhoye siyasi, s: 721, Intisharate danishgahe Tehran, espand 1373.

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa