Please Wait
11248
Ana kiran wannan bakin kyalle da ake rufe Ka’aba da shi a wannan zamani da suna suturar Ka’aba ko rigar Ka’aba. A wannan zamani ne ake wa Ka’aba rika da bakin yadi, da aka yi masa zayyanar ayoyin Kur’ani da aka saka da launin ruwan gwal. Amma a zamunan baya rikar Ka’aba yadinta bai takaita da bakin launi ba, akan yi amfani da yaduka masu launi daban-daban.
Ibin Ishak yana cewa: Akan yi mata da farin yadi sannan sai a ka rika mata riga da yadi mai ratsin launuka sakar kasar Yema. Sannan a bayansa (s.a.w) Umar da Usman da Hajjaj da Ibin Zubairu su ke mata rigar da farin yadi a mata sutarar ta dibaji[1] (alhariri).
A wasu lokuta a kan yi da koren yadi da ja. A wasu lokuta akan garwaya launukan.
A farkon mulkin Nasiruddin al-Abbasi sun yi wa Ka’aban sutura mai koren launi. Amma a karshen zamanin halifancinsa sai suka yi mata da yadi mai bakin launi.
Bayan da sarakunan Masar suka kama ragama, sun yi wa Ka’aba sutura. Su kan aika sutura mai jan launi a duk shekara.[2]
A zamanin sarki Shah mai suna Sahuki sanda Iraniyawa suka albarkatu da dammar yiwa Ka’aba sutura, akan saka ne da launi mai rowan kwai. Ibin Batuta yana cewa littafin tarihin tafiye-tafiyensa: “Akan saka rikar ne da dibaji (alhariri) zalla a lardin Kurasana da ke kasar Iran, kana sai a aikata Ka’aba.
A shekaru tsakanin 1221-1229, mutanen Hijaz ne suka albarkatu da yin rigar. Su kan yi sakar ne da alhariri ja. Wadda daga baya suka musanya shi da bakin alhariri.[3]
A duk lokacin da aikin Hajji ya karato lokacin a ke canza suturar ta yadda ake fara yayeshi a hankalu kana sai ayi wa Ka’bar farar sutura. Kana bayan kare aikin Hajji sai a saka masa sabuwar suturansa.[4]
Wannan ya nuna ke nan babu wani takamaiman dalili dangane da suturar Ka’aba, sai dai ya dogare da zabin masu yin.
[1]. Asgarul Fa’idan, Tarikhun wa ‘Asar Makka Mukarrama wa Madina Munauwara sh 95.
[2]. Asgarul Fa’idan, Tarikhun wa ‘Asar Makka Mukarrama wa Madina Munauwara sh 96.
[3]. Sayyid Kibare Simaya Makka sh161,
[4]. Sayyid Kibare Simaya Makka sh162. Mahdi Multaji, Faharanke Danastanbahye Bish (a.s). Safare Khana Khuda, 2012 sh 97 cikin, kitabu akhbare Makka wama ja’a fiha minal ‘Asar, na Muhammad Ibin Abdullah Ibin Ahmad Azruki.