Please Wait
9956
Sau da yawa mukan sami kawunan mu baki a rayiwa kuma makadaita, sai ka ga mun samu kan mu a hanyar da ba makawa dole sai mun tafi a kanta, wannan ita ce tabbatacciyar hanyar rayuwar mu ta tuntuni, kuma hakan ya hada da wasu al'amura kamar tsatson da muka fito daga gare shi, kabila, iyalin da aka haife mu a cikin su, abin cin da muke ci, yanayin yadda muka kasance, yare, da wasun wadannan. A daya bangaren kuma sau da yawa mukan sami kawukan mu kusa da wasu hanyoyi, shin za mu bi wadannan hanyoyin? Ko wasu za mu bi mu bar wadancan? Sanadiyyar haka sai ka ga mun dimauce mu yi ta kai kawo muna bata lokacin mu. Tambayar farko wace ke shigowa kwakwalen mu a cikin wannan halin ita ce: me zamu yi? Wacce hanya zamu bi?
Haka ne, hakika lafazi kamar "wacce", "don me" "ko wanne abu" suna yin nuni a kan zabi.
Amma dangane da abin da ya shafi zabin mutum ba makawar cewa: ba mu ne masu samar da ayyukan mu na zabi ba kawai, kuma ba a tilasta mana yin aikin ba ba tare da taka rawar mu ba, mu dai mu ne muke yin aikin tare da taimakon wasu masu share fage kamar sharudda mukaddimat (masu yin shinfida). Idan har ba a sami wannan tauyayyiyar illar (sababi) ba, wacce ita ce zabin mu da nufin aiwatar da aiki, to aiki ba zai yiwu ba har abada.
Aikin da mutum yake yi yana nuna alama daga cikin alamomin cewa duniya halittatta aka yi, hakika ayyukan da mutum yake aikatawa yakan zama talker manuniya a bisa samuwar ababan halitta a wannan duniyar, ma’ana abin yana da alaka cikakkiya da sababai (mai samarwa).[1] Shi mutum wani bangare ne daga bangarorin wannan duniya, kuma yana da dangantakar ta samuwa daga duniyar lahira, don haka ba zai yiwu wasu bangarorin su zama marasa tasiri a cikin ayyukan sa ba, misali 'yar gurasa wacce mutum ya kan ci, tana bukatawa ya zuwa wasu abubuwa da mutum zai iya amfanuwa da ita kamar ilimi, nufi, iko samuwar baki da kafa da wasun wannan, kamar kasancewar gurasar gata, da yiwuwar daukanta, da rashin samuwar abin da zai hana hakan, da dai sauran wasu abubuwa da wasu sharudda na waje har ma da na zamani duk suna da tasiri cikin samar da aikin. A lokacin da daya daga cikin abubuwan ko wani daga cikin sharadai bai tabbata ba to aikin ba zai kasance ba, ba za a sami damar yin gurasar ba, duk lokacin da abubuwan suka samu (samuwar duk abubuwan nan shi ne sababi cikakke) to aikin dole zai tabbata[2] (illa cikakkiya tana nufin tabbatuwar baki dayan sabubba da abubuwan da ke bada gudunmawa wajen yin aikin ko kuma samar da shi).
Hakika Allah shi ne ya mallake mu, nufinsa ya rataya da cewar mutum yana da manufa a cikin ayyukan sa da ya zaba, kamar shi ne mafarin wadannan sababan, misali idan kana neman tabbatuwar wani cikin ta hanyar abubuwa biyar to daya daga cikin wadannan abubuwa shi ne manufa da zabin mutum. Da za mu ce hasken wutar lantarki yana bukatar abubuwa da dama kamar: makunni, waya, fitilar, mita, transformer, shigar lantarkin cikin waya, hakika dayan daga cikin wadannan sabubba shi ne kunna mukunnin wutar, a cikin wannan misalin zai yiwu a ce idan duk wadannan sabubban da sharuddan suke tasbata to kunna fitilar yana nuni akan zabin mu da nufin mu, hakika Allah madaukakin sarki ya yi nufin cewa da mutum bai danna mukunnin fitilar ba da zabin sa, da fitilar ba ta ba da hasken ba. Hakika wajibcin danganta aikin gabaki dayan bangarorin a matsayin sababi ne cikakke, kuma wannan baya sa a ki danganta aiki ga mutum a matsayin sa na wani bangare daga bangarorin sababi cikakke.
Misalin da ya gabata dai-dai ne idan duk sabubban sun tabbata tabbas fitila za ta ba da haske, sai dai wai shin danna mukunnin fitilar dole ne ko ba dole bane?
Jawabin wannan tambayar shi ne: Lokacin da mutum ya tafi dannan mukunnin fitilar, to baki dayan sabubba sun cika, dole lantarki za ta bada haske. Tabbas yunkurin mutum ko rashin sa yana bada ma'anar yiwuwa wato zai iya yi ko ya bari, a fili hakan yake.
Saboda haka ikon mutum ne ya yi ko ya bari wannan yana nuni a kan zabi, kuma wajabcin danganta aikin ga baki dayan bangarorin nan na sababi baya wajabta danganta aikin zuwa ga wani bangare daga bangarorin sababi, - wanda shi ne mutum - irin dangantawar nan ta ba makawa ba.
Hakika fahimta da ganewar mutum - ta hanyar `yar karamar waiwayar sa ga wani abu - na karfafa wannan maganar, kuma abin a fili yake domin kuwa yana iya gane hakan. Mutane suna banbance kyautar Allah iri biyu, hakika mahangar ba daya b ace, misali, ci da sha, tafiya da dawowa ta wani bangaren, tafiya da rashin tafiya, girma da yaranta, tsaho da gajarta ta wani bangaren. Suna gane banbanci tsa kanin irin abubuwannan guda biyu, bangare na farko yana da dangantak da nufin mutum nan take, hakika yana cikin da'irar zabin sa, kuma an ba shi umarni da hani da tambaya, har ma da yabo da zargi. Sabanin bangare na biyu, ba wani nauyi ko aiki ko taklifanci a cikin sa game da mutum (ba a dorawa mutum yin wannan aikin ba).
Hakika mazahabobi biyu mashahurai sun bayyana a farkon Musulunci wadanda ke da alaka da Ahlussunna, sun yi magana dangane da ayyukan mutum. Wasu sun kudurce cewa ayyukan mutum sun rataya ne da manufar Allah wacce ba zai yiwu ya saba da hakan ba, saboda haka mutum a wajen su an dora shi a kan ayyukan sa (wato an tilasta shi haka zai yi ba shi da zabi kwata-kwata) ba sa ganin yiwuwar zabin mutum da nufinsa. Alhalin daya bangaren sun tafi a kan cewa mutum shi kadai yake ayyukansa (yana cin gashin kansa) ayyukansa ba su da alaka da nufin Allah, ayyukan sa sun fita daga cikin kaddara. Amma a mahangar koyarwa ta Ahlul-baiti amincin Allah ya kara tabbata a gare su wacce take dacewa da zahirin ayoyin Al-Kur'ani mai girma, hakika mutum yana da zabi a cikin ayyukan sa, sai dai wannan ba ya nuni ya zuwa cewa yana cin gashin kansa bane, ita dai kudurar Allah madaukakin sarki ta rataya da ayyukansa ta hanyar zabi. A wani bayanin kuwa, iradar Alalh (wato nufinsa) ta rataya da aikin mutum a matayin sa wani bangare na tarayyar illoli da suka hadu suka samar da illa cikakkiya wacce take tabbatar wa da mutum zabi kuma shi din wani bangare ne na illar, saboda haka sai ya zama aikin ya kasance saboda ya nufe shi, sakamakon wannan maganar hakika aikin dole ne, sai dai mutum yana da zabi a cikin yi ko bari.
Abin nufi a nan shi aikin idan an danganta shi zuwa ga baki dayan bangarorin illar sa cikakkiya dole ne zai faru, amma idan an danganta shi ga dayan sasannin illarsa - shi ne mutum, to aikin ya zama na zabi ne kuma mai yiwuwa ne ya kasance.[3]
Littattafan da muka yi amfani da su a wannan maudu'in:
- "Ma'aafatul Insan" Mahmud Rajabiy, Fasali na 5,6.
- Manhajul Jadiyd fi ta'allumil falsafa, Misbahul yazdiy, 72, darasi na 69.
- Aladlul'ilahiy, Murtadha mudahhari.
[1] Imam da illa ta zama ta wadatar a wajen samar da abin samarwa kuma samuwar sa ta zama ba ta dogara da wani abu ba in ba mai samarwar ba, da wata hausar,wato samuwar mai samawar ta zamo lalle ce domin a tabbatar samuwar wanda a ka samar a wnannan yanayi a na kiran masamarwar da (cikakkiyar illa, mai samarwa ta baki daya).
Amma farali na biyu duk da cewa mai samarwar ta kasance larura ce a wajen samar da abin samarwa; sai dai irin wannan illar ba za ta isar ba a wajen samar wannan samuwar ba, hakika bukatarsa za ta wanzu tana rataye da wasu abubuwa na daban, ko wasu illoli na gefe (idhafiyya ba na asali ba) domin samuwar abin samarwar ta zama lalle. A irin wannan yanayin ana kiran illa (tauyayyiyar illa).
[2] Aldaba’dab’’I, sayyid Muhammad Husain a cikin littafin al shi’ah fil islam shafi na 78 madba ar manshurat.
[3]Aldaba’dab’’I, sayyid Muhammad Husain a cikin littafin al shi’ah fil islam shafi na 79, madba ar manshurat.