Please Wait
7269
- Shiriki
Majalissar kwararru ta zaben shugaba ta hada fakihai {wato masana a cikin fikhu} a cikin dokokin tsarin mulkin na jamhuriyyar musulunci ta iran a bisa doka ta 107, ya tanadi zabe wanda a keyi duk bayan shaikara takwas {8}domin zabar shugaba da kuma lura da yanda yake tafiyar da shugabanci, kuma wannan zaben mutane ne ke zaben kwararru su kuma su zabi shugaba daga cikin su wato wanda ya cika sharudda na shugabaci.
A doka ta 1 da kuma ta 2 ta tsarin mulki na nuni da cewa yan majalissar kwararru kar su wuce 86.
Sharuddan zama dan majalissar kwararru.
Dokoki na tsarin mulki ba su bayyana wasu sharudda ba na zama dan majalissar kwararru ba, sai dai a doka ta 108 a karo na farko an bar abun a hannun yan majalissar kare kundi tsarin mulki da ga baya kuma abun ya koma hannun yan majalissar kwararru, sai dai abin da za mu lura shi ne akwai wasu sharudda wanda dole ne dan takara ya cika su.
Na daya: dole ne ya kai matakin fakih {wato wanda zai iya fidda hukunci} ya kuma zamo masanin siyasa da kuma al'amurran ya da kullun, ta yadda zai iya fidda wanda yafi kowa sani a fuskar fikihu da al'amurran siyasa da kuma na yau da kullun ko kuma wanda yafi karbuwa ga mutane.
Na biyu: ya kuma zamo mai tsoran Allah {s. w, t} domin kada ya sa san rai a cikin bayanen sa ta yadda sai dai duk abin da zai fada domin musulunci ne da musulmi ba wai amfani kan shi ko kuma na yan kunkiyar sa. Ta wata fuska kuma in ya zaman to mutun ne mai fadi baya aiki da abin da ya fada ko kuma ya na da mumunan tarihi a cikin siyasa da al'umma, saboda haka ba zai yiwu ba ayarda da abin da ya faba ba.
Sharuddan zaben yan majalissar kwararru kamar haka:
- Riko da addini da kuma halaye na gari
- Ijtihad {wato ilimi mai yawa} wanda zai iya fidda hukunci a cikin mas'alolin fikh ta yadda zai iya ganewa da kuma fitar da wanda yafi kowa can can ta da ya zamo shugaba.
- Hangen nesa ta mahangar siyasa da rayuwa da kuma al'amuran yau da gobe
- Imani da tsarin jamhuruyar musulunci ta iran
- Rashin mumunan tarihi na siyasa da kuma rashin laifufuka a cikin mutane
Idan muka dubi wadannan sharuddan na zama dan majalissar kwararru na shugabanci ba wani sharadi da ya ce dole dan takara ya zamo namiji; saboda haka ba wata doka da ta hana mace shiga majalissar kwararru, sai dai abun lura shi ne ba wai dukkan wanda ya shiga majalissar kwararru bay a na nufin zai iya zama shugaba ba ne, ba kuma a na nufin dukkan wanda ya cika sharuddan zama dan majalissar kwararru bay a zamo ya cika sharuddan zama shugaba ba; saboda kowa nen su na da sharuddan da suka shafe shi,
Saboda haka in aka lura da cewa a cikin sharuddan zama shugaba akwai sharadin afta {wato mafi ilimi} kuma daga cikin sharadin afta[1] {wato mafi ilimi} akwai ba da fatawa[2] {wato ba da hukunci} a cikin sharadin ba da hukunci akwai ya zamo namiji, abisa asashe mahangar masana na musulunci dole ne ayi koyi da mujtahidi {tagalidi} namiji[3], saboda haka mace baza ta iya zama shugaba ba.
Amsar ayatullahi mahdi hadawi {Allah yai mai albarka} kamar haka:
Ba hani Shigar mata cikin majalissar kwararru, sai dai bayana nufin za su iya zama shugaba ba ne, bai halasta ba mace da zamo shugaba ba abisa zance mafi karfi.
[1] Asalin doka ta 108 ta dokokin jamhuriyar musulinci tai ran,
[2] Tahririlwasilah jildi na 3 shafi na 175 zuwa 182,
[3] Tauzihe masa'il { almahsha lilimam khumaini } jildi na 1 shafi na 13 .