advanced Search
Dubawa
11090
Ranar Isar da Sako: 2007/02/14
Takaitacciyar Tambaya
Wa ‘ya’yan Adamu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) suka aura?
SWALI
Wa Habil ya aura? Yaya tsatsun autan ya ci gaba bayan su?
Amsa a Dunkule

A kan sami ra’ayoyi guda biyu a kan maganar auren ‘ya’yan Adam (amincin Allah ya tabbata a gare shi).

  1. A wannan zamanin ba a sanya dokar haramcin dan’uwa ya auri ’yar’uwarsa ba, kuma ba wata hanyar kiyaye tsatso na mutane domin idan ba ta wannan hanyar ba, to ba za a sami al’umma ba a saboda haka ne ya zama ‘yan’uwa sun auri ‘yan’uwansu mata.
  2. Ra’ayi na biyu yana cewa, auren muharramai abu ne mai muni kuma hankali ba ya karbar sa, don haka ne ‘ya’yan Adamu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ba za su auri junansu ba. hakika ‘ya’yan Adamu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) sun auri wasu mata na wani tsatson wadanda suka kasance a doron kasa tun kafin Adamu (amincin Allah ya tabbata a gare shi), bayan auren sai ‘ya’yansu suka haofi ‘ya’yan suak hayayyaffa. Allama Tabataba’i  mai tafsirin Almizan ya tabbatar da ra’ayi na farko.
Amsa Dalla-dalla

An jeho wannan tambayar tuntuni,  su wa ‘ya’yan Adamu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) suka aura? Shin sun auri ‘yan’uwansu mata ne? shin sun auri mata ne daga mala’iku ko aljanu? Bagu da kari, idan mun dubi haramcin dan’uwa ya auri ‘yar’uwarsa a baki dayan shari’o’i da addinai. Yaya zai yiwu mu fassara wannan auren?

Ana samun ra’ayoyi guda biyu a wajen malaman musulunci a kan wannan mas’alar, kuma duk bangare biyun suna kafa dalili da ayoyin Alkur’ani da riwayoyi na hadisai. Za mu kawo ra’ayoyin bangarorin biyun da takaitaccen tsari na bayani.

  1. Ra’ayin farko: Tabbas sun auri ‘yan’uwansu mata, saboda a wannan zamanin babu shari’a daga wajen Allah ta’ala ko wata dokar haramta wa dan’uwa ya auri ‘yar’uwarsa ta wannan bangaren ke nan. Ta daya bangaren kuma babu wata hanya wacce za ta wanzar da samuwar mutane (al’umma) a doron kasa, sai dai wannan hanyar, saboda sashensu ya auri sashe, bagu da kari, hakkin sanya wa mutane shari’a ya kebanta ga Allah kamar yadda littafin Allah ya fada: “Babu hukunci sai na Allah”.[1]

Allamah Tabataba’i (Allah ya yarda da shi) ya yi magana a wannan fagen yake cewa, auren a lokacin Adamu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Hauwa’u ya tabbata tsakanin ‘yan’uwa maza da mata, domin babu hanyar samar da tsatso an yi hakan. To a bisa wannan asalin babu wata matsala, saboda shar’antawa ta kebanta ga Allah (tsarki ya tabbata a gare shi). don haka, Allah zai iya halatta abu a wani zamani bayan nan sai ya haramta shi.[2]

Mai tafsirin al’amsal bai ga wani abin mamaki ba a cikin wannan fahimtar ba yayin da yake cewa:

Yaya auren ‘ya’yan Adamu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya kasance?

Allah subhanahu wa ta’ala ya ce: Allah ya watsa maza da mata daga tsatson Adamu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Hauwa, wannan ayar tana ba da ma’anar watsuwar ‘ya’ya (zuriya) daga Adamu da Hauwa’u ne kawai, ba tare da shigowar wani bare ba (auren wani tsatso) sun auri junansu, domin idan auren ya tabbata tsakaninsu da wasunsu to maganar Allah fa ya za a yi da ita. Allah ya ce “daga gare su”.

Hadisai masu yawa sun zo a kan wannan mas’alar, ba wani abin mamaki ko sabon al’amari, domin ya dace da abin da ya zo a cikin hadisin ahlul baiti (amincin Allah ya tabbata a gare shi) cewa irin wannan auren halal ne tun da haramci bai zo ba sai daga baya. (auren dan uwa ga `yar uwarsa).

Abu ne a fili haramta abu yana hannun Allah (tsarki ya tabbata a gare shi), Mene ne zai hana bukatuwa mai karfi da masalaha sananniya jawo halatta wani abu a wani zamani sannan daga baya a haramta shi a wani lokaci.[3]

Masu wannan ra’ayin sun dogara da hujja ta Alkur’ani domin Ubangijin bayi yana cewa; Allah Shi ne ya watsa mazaje da mataye masu yawa daga Adamu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Hauwa’u.[4]

 Bugu da kari wannan fahimta tana karfafuwa da riwayar da dabins ya kawo a cikin Al’ihtijai ya karbo daga Imam Zainul Abidina (amincin Allah ya tabbata a gare shi).[5]

2.         Ra’ayi na biyu, ba ya yiwuwa ga ‘ya’yan Adamu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) su auri junansu, domin auren muharramai abu ne mai muni ba karbabbe ba, haramun ne a bnagaren shari’a. daga nan ne za mu gane ‘ya’yan sun auri matan wani jinsi ne. wasu tsatson wanda suke zaune a doron kasa tun kafin Adamu (amincin Allah ya tabbata a gare shi). Bayan haka, ’ya’yansu sun zamanto ‘ya’yan baffani, daga nan ne aure ya fara. Ana samun wasu riwayoyi wadanda suke karfafa wannan mahanga (fahimta), kuma suke karfafa cewa tsatson Adamu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ba shi ne tsatso na farko ba a kan doron kasa ba. akwai mutane wadanda suka rayuwa a ban kasa kafin Adamu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) sai dai wannan ra’ayin bai dace da zahirin ayoyin Alkur’ani ba, domin ayoyin Alkur’ani suna tabbatar da cewa tsatson mutum daga Adamu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Hauwa’u ne kawai. Wannan riwayoyin suna cin karo da littafin Allah, saboda haka ba za mu karbi wannan ba. a cikin kafa hujjoji da kuma dogaro da ayoyin Alkur’ani za mu iya kai wa ga matsayar cewa, gano mala’iku ko aljanu wannan ma mahanga ce (fahimta) ba daidai ba. Bugu da kari, ayar Alkur’ani ta yi nuni a kan tsatson mutane ya faru ne daga Adamu da Hauwa’u kawia [6] ba wand aya shigo domin wanzar da tsatson, ayar littafin Allah ta ce: “Daga gare su da ba haka ba ne sai aya ta ce, daga gare su daga wanin su”.

Allam Tabataba’i (Allah ya yarda da shi) ya ce, zahirin aya tsatson mutum wanda ke doron kasa yana dangantuwa ne zuwa Adamu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) da matarsa, ba tare da shigowar wani ba saboda Allah ya ce: “Ya watsa maza da mata daga su biyu”. Bai ce daga gare su ba kuma daga wasunsu ba”.[7]

A wannan halin ya wajaba gare mu, mu karfafa tare da bin riwayoyin da suka dace da ayoyin Alkur’ani, wannan shi ne yayi daidai da ra’ayi na farko.

 


[1] Yusif, 40.

[2] Almizan, 14, sh. 127.

[3] Tatsiyrul amsal j, 3 sh. 81.

[4] Annisa’i , 1.

[5] Al ihtijaj j.2 sh. 314.

[6] Annisa’i, 1.

[7] Almizan j. 4 sh. 127.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa