Please Wait
20908
Babu wani ra’ayi mai karfi – kamar yadda ya zo a cikin abubuwan da suka faru a tarihi masu yawa game da adadin ‘ya’yan Adam (a.s), don haka ne muka ga sabani mai yawa da ra’ayoyi mabambanta kan sunayensu da adadinsu, kuma zai yiwu a samu sabani mai yawa kan wannan mas’ala sakamakon tsawon zamani mai yawa da ya faru a marhalolin tarihi tun lokacin da aka fara rubuta tarihi da dawwana shi, ko kuma ya faru saboda babu wani muhimmanci da marubuta suka bayar tun farko ga ambaton sunayen ‘ya’yan annabi Adam (a.s).
Alkali Nasiruddin alBaidhawai yana fada a littafin “Nizamut Tawarikh an adadi auladi Adam wa Hawwa”: Duk sa’adda Hawwa ta yi ciki to tana haife namiji da mace ne ‘yan tagwaye. Kuma duk mace ta wani cikin to tana aurar wani namijin ne na wani cikin (wato aure ana kulla shi ne ga mace ta wani cikin da namiji na wani cikin ba wanda aka haife su tare ba), haka nan ya ci gaba da fada har ya kai ga cewa: Hawwa ta haifi ciki dari da ishirin ne, kuma ta haifi Kabila a ciki na hudu ne.
Kuma bayan shekaru biyar da mutuwar Habila dan Adam (a.s), sai ta haifi wani da guda daya ba tare da mace tare da shi ba, da aka ambace shi da “Shis”, ya ce: Wannan shi ne musanyar Habila, kuma shi ne da mai yawan albarka da zai zama annabi daga baya[1]. Bisa wannan ra’ayin: Adam da Hawwa (a.s) suna da ‘ya’ya 239 ke nan.
Dabari yana kawo ra’ayoyi uku musamman kan wannan lamarin yana cewa kamar haka:
1. ‘Ya’ya dari da ishirin maza da mata.
2. Arba’in ne maza da mata.
3. ‘Ya’ya maza ishirin da biyar da mata hudu.
Don karin bayani: Tarikh Tabari, Tarihul Umam wal Muluk, j 1, s: 145.
Tarjamar: Hafiz Muhammad Sa'id