advanced Search
Dubawa
8638
Ranar Isar da Sako: 2016/07/12
Takaitacciyar Tambaya
wanene mu”azu dan jabal?
SWALI
ina bukatar sanin tarihin rayuwar mu”azu dan jabal?
Amsa a Dunkule
Mu”azu dan jabal dan amru dan ausu dan a”izu, ane masa alukunya da baban Abdurrahman, sannan ya na daga cikin mataimakan manzon Allah {s.a.w}.[1]
mu”azu dan jabal tare da mutane 70 na daga cikin wadanda sukai mubaya”mar akaba sannan suka yi tarayya cikin yakoki misalin badar da uhud.[2]
 
Mu”azu dan jabal bayan ya yi tarayya cikin yakin tabuk lokacin yana shekaru 28 manzon Allah {s.a.w} ya tura shi kasar yaman da sunan mai koyarwa, hatta lokacin da manzon rahama ya yi wafati mu”azu ya kasane a kasar yaman, zamanin halifancin Abubakar mu”azu ya samu kwamandancin yankin jundu da ke yaman.[3]
 
Mu”azu dan jabal bayan wani lokaci ya dawo makka sannan ya koma kasar sham yankin amawas wanda sunan wata nahiya ce a kasar jodan wadda aka jarrabe su da wata musiba, mu”azu dan jabal ya bar duniya ya na da shekaru 38 zamanin halifancin umar dan kaddab sannan zuriyarsa ba ta wanzu ba.[4]
 
Ahlus sunna sun rawaito sun rawaito riwayoyi masu tarin yawa game da falalar mu”azu dan jabal, amma mafi shahara daga riwayoyin ita ce wadda ke bayani kan aiki da ra”ayi wadda ke nuna cewa manzon Allah {s.a.w} ya goyi baya da karfafa aiki da ra”ayi lokacin da aka rasa hukunci cikin littafin Allah da hadisi. Wannan sha”ani ya samu karbuwar ahlus sunna ta yadda idan suka rasa hukunce daga tushe biyu ma”ana kur”ani da sunna to suna komawa aiki da ra”ayi.
 
Kamar yadda ya zo cikin littafan sunna: zamanin da  manzon Allah {s.a.w} ya aika mu”azu kasar yaman mu”azu ya tam manzon rahama ya tambaye shi ya na mai cewa: idan ka rasa hukunci cikin littafin Allah ya za ka yi?  Sai mu”azu ya ce: zan komawa sunna, sai manazon rahama ya kara tambayarsa ya ce: idan ka rasa hukuncin a sunna ya za ka yi? Sai mu”azu ya ce: to a irin wannan yanayi ba tare da ko wane irin wahami ba ina yin  ijtihadi da ra”ayi na, sai manzon Allah {s.a.w} ya daki  kan kirjin mu”azu ya ce: godiya ta tabbata ga Allah wanda ya datar da dan aiken manzon Allah {s.a.w} kan abin da manzon Allah {s.a.w} ke yarda.5
A cikin littafin irshadul kulub Dailami ya rawaito cewa mu’azu a zahiri ya yi da-na-sani kan rashin bawa imam Ali (as) goyon baya kan halifanci manzo (saw).[5]  
 

[1]1 Al”isti”ab fi ma”arifatul  as”hab juz 3 sh 1402  
[2]  Usudul gaba juz 4 sh 418.2
[3]  Dabkatul kubarah juz 7 sh 2763
[4] Dabkatul kubrah juz 7 sh 273
[5] Irshadul kulub ila sawab juz 2 sh 391
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa