advanced Search
Dubawa
5274
Ranar Isar da Sako: 2012/05/14
Takaitacciyar Tambaya
Shin zama hannu rabbana daga kan ruwayoyi tare da wadatuwa da al kur’ani mai girma ya isa hadin kai wajan al ummar musulmai?
SWALI
a wannan lokacin an samu wasu mutane na cewa su ba wahabiyawa bane, duk da cewa akidunsu na kama da na wahabiyawa suna kuma da shafin yanar gizo gizo (internet) na kowa da kowa da shafin kebantattun su. Suna cewa matsalar da ta haifar wa musulmi wadannan rabe raben bangarorin da suke fama dashi yanzu, shi ne rikonsu ga ruwayoyi da hadisai ta wani bangaren , ta wani bangare kuwa ilimin bin diidgin ruwayoyin hadisai (diraya) da mazajen hadisai wanda basu da wata kimar da za’a sanyasu wani ginshiki, wannan kuwa saboda zaka samu daga bangaren shi’a da sunna na riko da natijar wannan ilimi wajan fitar da natijar kowannensu ke riko da ita, a nan ne suke ganin abin da yafi dacewa shi ne yin halin ko in kula tare da dauke hannu wajan yin amfani da ruwayoyi a riki kurani kawai , da tsare (takaice) sunna wajan samota daga kurani kadai. 1. Shin zan iya yi wa wadannan mutane cikakken raddin da ya yi daidai da hankali da kuma wanda yai daidai da nassin addini?. 2. Me kuka sani game da wadannan bangare?.
Amsa a Dunkule
Wannan magana ko kuma muce wannan bangare bawai sabon bangare bane, asalinsa ya faro tun daga karshen rayuwar Manzo (s.a.w) inda wasu daga alamomin wadannan mutane ya bayyana, daga masu tunani kan mganar cewa “littafin Allah (s.w.t) ya ishemu riko” ta farune tun daga lokacin da Manzo (s.a.w) ya nemi a kawo tawada da alkalami zai rubuta musu abin da idan sukayi riko dashi bazasu taba bataba har abada, inda a nan take wasu suka nuna kinsu da hakan (Buhari a wasu ruwayoyinsa ya kawo cewa wanda ya hana a kawo wannan abin rubutu shi ne halifa Umar dan kattab ) inda suka hana a rubuta wannan wasiyya ta Manzo (s.a.w) a nan Umar ke furta cewa “littafin Allah (s.w.t) ya ishemu” wanda sananne ne a litattafan tarihi.
Sannan kuma babu wani musulmi da zai bugi kirjimn shi baya bukatuwa zuwa sunnah, tambaya a nan ita ce shin dukkan bangarorin hukunce hukunce samammune kamar yadda suke a kurani? Kuma shin dukkan bangarorin ibada kamar salla,azumi zakka,hajji,… akwai su a kurani mai girma?! Idan zamuyi duba zuwa kuran mai girma zaka samu babu wani kokwanto yana cewa “duk abin da Manzo (s.a.w) yazo muku das hi ku karbeshi, kuma duk abin da ya hana ku ku hanu , kuji tsoron Allah (s.w.t), hakika Allah (s.w.t) mai tsananin ukuba ne”. wannan a bayyane yake cewa duk umarni da hanin da Manzo (s.a.w) ya yi mana ita ce ainihin sunnar da Allah (s.w.t) ya umarcemu tare da wajabta mana riko da ita.
An rawaito daga Ahmad dan Hambali daya daga shugabannin mazhabobi hudu cikin musnadinsa yana cewa: daga abi Sa’idul khudry ya ce, daga Manzo (s.a.w) cewa “na bar muku nauyayan abubuwa biyu daya yafi daya girma a tsakaninsu su ne littafin Allah (s.w.t) wanda shi ne igiyar da ta sada sama da kasa da iyalan gidana wadanda abubuwa biyu ne bazasu taba rabuwa da juna ba har sai sun tarar dani a bakin tafkin alkausara” karin bayani shi ne Manzo (s.a.w) ya sanya iayalan gidansa cikin wannan hadisin kafada da kfada da al’kurani mai girma, ina nufin yadda ya zama dole ga musulmai suyi riko da alkur’ani haka ya zama dole suyi riko da ahlin gidan Manzo (s.a.w) tare da karbar duk abin da yazo daga wajansu, domin ini ka riki daya ka kyale daya kayi aiki marar inganci (dole sai su biyun saboda bashi da ma’ana) .
Akan wannan ne nake cewa bazai taba yiyuwa ba ga duk wanda ya zamo musulmi kuma yai watsi da sunna da rashin riko da ita wannan ba shi ne ya sanya sabani da rabuwa ba, kai rashin rike sunnar ydda ya dace shi ne ma abin da ya sanya sabani da rabuwar kai mai tsanani. Abin da muka sani game da maganar rabuwa da sunna ta bayyana akan wasu bangarori da ke kiran kansu “ahalin kurani” suka kuma halastawa kansu tafiya a kai, kungiyar ta fara samuwa tun shekara ishirin da biyar din farkon karnin hijira na sha hudu (14) a wani bangaren India.
Amsa Dalla-dalla
Wannan magana ko kuma muce bangare bawai sabon bangare bane, asalinsa ya faro tun daga karshen rayuwar Manzo (s.a.w) inda wasu daga almomin wadannan mutane ya bayyana , daga masu tunanai cewa “littafin Allah (s.w.t) ya ishemu riko” ta farune tun daga lokacin da Manzo (s.a.w) ya nemi a kawo tawada da alkalami zai rubuta musu abin da idansukayi riko das hi bazasu taba bataba har abada, inda a nan take wasu sukja nuna kinsu da hakan (Buhari a wasu ruwayoyinsa ya kawo cewa wanda ya hana a kawo wannan abin rubutu shi ne halifa Umar dan kattab ) inda suka hana a rubuta wannan wasiyya ta Manzo (s.a.w) a nan Umar ke furta cewa “littafin Allah (s.w.t) ya ishemu” asalin litattafan hadisi na makarantun sunnah sun tabbatar da hakikanin wannan hadisi kamar sihahun Bukhary, muslim da musnadin Ahmad da …
  1. Aliyyu dan Abdullahi da Abdurrazak sun fada mana cewa Mu’ammar ya labarta mana daga zuhriyyin daga Ubaidullah daga Abdullahi daga Utbata daga Abdullahi dan Abbas (RA) ya ce :yayin da Manzo (s.a.w) yazo cikawa, acikin gidan akwai mutane sai Manzo (s.a.w) ya ce “ku kawo (abin rubutu) zan rubuta muku abin da bazaku taba bataba a bayana” sai wasu daga mutanen ke fadawa wasunsu cewa hakika Manzo (s.a.w) na cikin magagin mutuwa (magagin mutuwane ke dibarsa) kuma kunada alkur’ani, littafin Allah (s.w.t) ya ishemu, sai mutanen da ke cikin gidan sukayi ta sabani tare da husuma juna, wasu na cewa ku kawo ya rubuta muku abin da bazaku taba bataba bayansa!, wasu kuma na fadin sabanin haka, (abin da Umar ya fada) yayin da jayayya da husuma suka tsananta sai Manzo (s.a.w) ya ce “ku tashi (ku ba ni waje)”. Ubaidullahi dan Umar ya ce: Abdullahi dan Abbas ya kasance yana cewa : <wanna masifa ta cika babbar masifa,na halin da Manzo (s.a.w) ya kasance (ya yi wafatinsa) akan wajan sabaninsu da hanawarsu wajan ya rubuta musu rubutun”[1]. A nan mun lura mutumin da ke cewa “magagin mutuwa ne ke dibansa ba’a bayyana shi ba domin kawai yadda aka nuna wani ne daga cikin mutanen da ke nan ya fada, amma Bukhary ya rawaito tare da kawoshi cikin sahihinsa da cewa wanda ke fadar wannan maganar shi ne Umar dan khattab.
  2. Umar dan khattab na cewa: Hakika magagin mutuwa ke diban Manzo (s.a.w), mu munada littafin Allah (s.w.t) ya isar mana[2]. zakaga a cikin wadannan hadisan kamar ba sa ganin girman wannan kalma (ta rashin girmamawa) da aka gayawa Manzo (s.a.w) yayin da ya bukaci ya rubutawa al’ummarsa, inda wasu daga sahabbai ke cewa wai yana cikin magagin mutuwa!!!, zaka samu Bukhary da kansa yana magana da mafi kaushi harshe (kan rashin ladabi ga Manzo (s.a.w)) shi ne zaka samu cikin hadisi na uku da ya rawaito shi ne.
  3. Daga Abdullahi dan Abbas (RA) yana cewa: wannan Alhamis!!! Wace irin bakar Alhamis ce wannan?! Ya dinga kuka yana zubar da hawaye mai kyalli a kan fuskarsa, sai ya ce : yayin da ciwon ajali ya tsananta ga Manzo (s.a.w) ranar alhamis sai Manzo (s.a.w) ya ce : “ku zomin da abin rubutu na rubuta muku abin da bazaku taba bataba a bayana har abada” sai suka dinga jayayya alhali bai kamata ba (babu ladabi) jayayya agaban Manzo (s.a.w), har da masu cewa Manzo (s.a.w) ya dimauce (bai san inda kansa yake ba)!!!. har ta kai Manzo (s.a.w) na cewa “ku tafi ku ba ni waje, na rantse da wanda yayini nafiku sanin abin da kuke kirana zuwa gareshi”[3]. Aiki da wannan banzan lafazi ga Manzo (s.a.w) cikin hadisai ukun da muka kawo, na nuna cewa wani ke fada (mutum daya) saidai shi Bukharin a sassauta munin Kalmar amma kuma ya fadi wanda yayita, amma shima a wani babi ya bayyana Kalmar da kaushi da cewa “Manzo (s.a.w) ya dimauce ne” duk da bai fadi wanda ya fada ba kawai dai ya yi amfani da Kalmar “sai sukace …”.
Raddi zaizo game da asalin masu fadir (tunanin) watsi da sunnah kamar yadda yazo cikin tambaya.
A nan zamuyi raddi ta bangarori biyu, bangaren amfani da nassin addini da bangaren da ya yi daidai da nassosin addini sosai kamar yadda malam mai tambaya ya nema.
 Na Farko: Dalilin Hankali
Da ace zamu sallamawa wannan tunani, abin nufi mu kaddara cewa duk musulmi yau sunzo gaba daya sun bi hakan, abin tambaya shi ne, shin kurani zai ishemu ba tare da mun bukatu zuwa ga sunna mai tsarki a rayuwarmu ba?!. Shin istinbadi (tsamo hukunci daga kurani) da neman tseratarwa daga kurani kadai zai ishemu kuwa? kuma shin zai yiyu kowa da kowa mutane su fahimci kurani fahimta daya sak?! Yiyuwar amsa wadannan tambayoyi, idan kuwa zai yiyu a bayyane yake wanda baya bukatar wani karin bayani ko sharhi, saidai duk da haka zamuyi kokarin nuna amsar ta hanya mai kyau.
  1. Muna ganin yadda aka samu rabuwar musulmi zuwa sunna da Shi’a cikin fahimtar ayoyin littafi mai hikima, kuma sabanin bai rage fahimtar juna tsakanin mazhabobin ba, kai harma muna ganin malamai cikin mazhaba daya, na smun sabanin fahimtar wasu ayoyin yayin da zaka samu mas’ala ta yi daidai da rassa ko tushe kuma ba’a samu sabani a cikinta ba[4].
  2. Shin akwai wanda ya taba tunanin rashin bukatuwa zuwa sunna kuwa?!, shin dukkan bangarorin hukunce hukunce daga kurani mai girma aka samo su? Shin dukkan abin da suka zo cikin sAllah (s.w.t), azumi , zakka da … akwai su cikin cikin kurani kuwa?!!
  3. Da zamu sallamawa wannan magana mene matsayin dukkan wadanna litattafan da aka tanada, da sauran litattafan hadisi kamar sihahu, sunanus sittah (sahihul Bukhary, muslim sunan, Abi dawud, …) da dubu daruruwan litattafan da aka rubuta game da hadisi dari da kuma sha kundum din hadisin makarantar Ahlul-bait (a.s) ?!
 Na Biyu: Ijma’i (Haduwar Malamai)
Wannan sananne ne cewa duk bangarori da mazhabobin musulunci sun hadu kan rashin wadatuwarsu da sunnar Manzo (s.a.w) mai tsarki, ta yadda bazasu samu wani mai Magana ko mai bincike da ke da imanin wadatuwa da sunna harma a iya aikata fikhu da sanin akida[5].
 Na Uku: KUR’ANI MAI GIRMA
Hakika Allah (s.w.t) ya karfafi riko da sunnar Manzo (s.a.w) da hadisai cikin kurani mai girma acikin ayoyi da dama na littafi mai hikima Allah (s.w.t) na cewa: “duk abin da Manzo (s.a.w) yazo muku dashi ku karbeshi, kuma duk abin da ya hana ku ku hanu , kuji tsoron Allah (s.w.t), hakika Allah (s.w.t) mai tsanani ukuba ne”[6]. wannan aya ta sauka ne kan ganimar banin nadheer sai dai ayar na magana ne da fadi fiye da wancan Magana ta ganima, kamar yadda malaman tafsiri ke fada. Ta wanzu da dalili tare da fadi harma ba sa bukatuwa zuwa sunna a dukkan fadin rayuwa .
Malaman tafsiri sunyi nuni kan wannan hakikar da cewa : “abin mamaki irin na wannan aya shi ne, cin fai’iy[7], hadi da hakan dukkan musulmi ta wajabta musu bin koyarwa da bin umarnin Manzo (s.a.w) tare da nisantar duk abin da ya hanesu, harma da bangaren gudanarwar hukumar musulunci, tattalin arziki (economy) da abin da ya shafi ibada da sauransu, musamman ma Allah (s.w.t) ya tsoratar a karshen ayar ga dukkan masu saba masa (manzon), tare da sanar dasu akwai azaba mai tsanani[8], ga dukkan wanda ya saba masa ta wani bangaren, wannan ya fayya ce cewa umarni da hanin Manzo (s.a.w) shi ne ainihin sunnar da Allah (s.w.t) ya sanya mana ma’ana ya umarcemu riko da ita a matsatyin wajabci, zamu iya tambayar me yasa Allah (s.w.t) ya lazimtawa dukkan mutane ba tare da togaciya ba wajan karbar koyarwa kai tsaye daga Manzo (s.a.w) ba tare da ka’ida ko sharadi ba? Wannan bayani na kara mana cewa Manzo (s.a.w) ma’asumine (baya kuskure da sabo koda kuwa bisa mantuwa ne) sabo da haka wannan ya zama gaskiya ga Manzo (s.a.w) da halifofinsa (ahalin gidansa) ma’asimai harma da wasu Abubuwa da dama[9]. bugu da kari idan mukayi duba da ra’ayoyi da dama sunyi nuni da wannan shi ne cewa hakika Allah (s.w.t) ya hana wadannan dukkan tantance tantancen ga Manzo (s.a.w) domin Allah (s.w.t) ya zabeshi kuma ya tsarkakesi cikakken tsarkakewa da irin Abin da ya dorashi a kai wato zama mafi kyan dabi’a da mukamin godiya saboda haka ya fifitashi da matsayi na gaskiya[10].
 
 Na Hudu: Hadisi
Hadisai da dama daga bangaren sunnnah da Shi’a sun (nuna mana da) umarcemu da muyi riko da sunnah tare da bincike a kanta kamar hadisin thakalain wanda yazo a littafin farikain (bangarori biyu). An rawaito daga Ahmad dan hambali daya daga malaman mazhabobin sunna hudu cikin musnadinsa : aswad dan Amiru ya zantar damu abu Israel wato Abi isma’il dan abi Ishak ‘Almala’iy’ ya labarta mana daga attayya daga Abi sa’idul khudry ya ce Manzo (s.a.w) ya ce “na bar muku nauyayan abubuwa biyu daya yafi daya girma a tsakaninsu, su ne littafin Allah (s.w.t) wanda shi ne igiyar da ta sada sama da kasa da iyalan gidana wadanda (ahalin gidana) abubuwa biyune bazasu taba rabuwa da juna ba har sai sun tarar dani a bakin tafkin alkausara”[11].
Akan wannan ne nake cewa bazai taba yiyuwa ba ga duk wanda ya zamo musulmi kuma yai watsi da sunna da rashin riko da ita, wannan ba shi ne ya sanya sabani da rabuwa ba, kai rashin rike sunnar ydda ya dace ma shi ne abin da ya sanya sabani da rabuwar kai mai tsanani. Abin da muka sani game da maganar rabuwa (a kyale) da sunna ta bayyan akan wasu bangarori da ke kiran kansu “ahalin kurani” suka kuma halastawa kansu tafiya a kai, kungiyar ta fara samuwa tun shekara ishirin da biyar din farkon karnin hijira na sha hudu (14) a wani bangaren India. a hannun wasu daga tsatson wadancen mutanen wadannan yanki wadannan masu assasata na daga wadanda suka tasirantu da tunnai mautanen yamma da suke ganin riko da sunnah na hana ci gaba ga Al’ummar musulmi daga cikinsu akwai mutanen gillain Ahmad yaba’az wanda aka fi san da yaru baziyya[12].
 

[1] Sahihul Bukhary bolume 17 page 417 babin rashin lafiyar Manzo (s.a.w) da wafatinsa hadisi na 5237; sahihu Muslim bolume 8, page 414; Musnad Ahmad bolume 6,page 368, 478; masdarin littafin :mauky’ul Islam , http://www.al-islam.com
[2] Sahihul Bukhary babu kitabatul ilmi da babu karahiyyatul akhlak.
[3] Sahihul Bukhary babin ‘hal yastash fi’u ila ahlith thimmati wa mu’amalatihim.
[4] Domin inganta wannan Magana duba tafsirin da manyan malamai suka rubuta.
[5] Ba muna nufin ijma’i a nan shi ne ijma’I na isdilahin fikihu ba a’a abin nufi rashin sabani da haduwa a kai.
[6] Suratul hashr: aya ta 7.
[7] Fakhruddeenur razy , Abu Abdulahi Muhammad bin umar, mafpatihul kaib , bolume 29 page 507, yadawar daru turathul Araby , Beirut second edition (bugu na biyu) 1420, tabatabiy, sayyid Muhammad Husain tafsirul mizan bolume 19 page 200-204, muassasatun nashrul islamy daya daga makaratun Hauzar ilimi da ke Kum 1417 AH fifth edition (bugu na biyar) Kum.
[8] Mukarimush shirazy Nasir tafsirul amthal bolume 18 page 181, yadawar madrasatu Imam Ali (a.s) dan abi talib 1421 first edition (bugun farko) Kum.
[9] Ruwayoyin da sukazo da wanna Magana sunada yawa, zaku iya duba tafsiru nuruth thakalayn bolume 5 page 279-283.
[10] Tafsirul amthal bolume 18 page 183.
[11] Musnad Ahmad bolume 22 page 226, 253, 324, bolume 39 page, 308.
[12] Duba Usman dan mu’allim Mahmud dan sheikh Ali shubuhatul kur’an (shubuhohin kurani) a gabatarwar (mukaddimar) littafin.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa