Please Wait
17410
"Ashsharab" abin nufi duk abin sha "Addahiru" abin nufi mai tsaki mai tsarkakewa wannan kalma an yi amfani da ita a cikin ayoyi daban-daban a gidan aljanna ana samun abin sha mai tsarki mai dadi iri-iri mai yanayi kala-kala, hakika Kur'ani mai girma ya kawo maganar sa a wata aya:
((وسقاهم ربهم شرابا طهورا)).
Allah ya shayar da 'yan Aljanna abin sha mai tsarki.
Meye abin sha mai tsarki? Idan zamu bada amsar tambayar nan akwai maganganu guda uku wadanda suka zo:
- Wani Malami ya ce: Abin da ake nufi da abin sha mai tsarki shi ne abin da 'yan aljanna suke sha bayan sun ci abin ci, saboda haka sai ya kau da duk dattin ciki, ba abin da zai wanzu sai gumi mai kamshi wanda ke tsattsafowa daga fatarsu.
- Wata fassara kuma tana cewa abin da ake nufi shi ne fa'idojin ruhi da kuma gyaruwar sa har ma da cigaban sa, kamar yadda aka rawaito daga Imam Sadik (A.S): Tabbas mumini yana shan abin sha mai tsarki sai ya rabu da komai banda Allah, ba zai fuskanto komai ba sai Allah. An karbo daga Imam Bakir amincin Allah ya kara tabbata a gare shi: Hakika muminai a lokacin da ska sha abin sha mai tsarki Allah zai tsarkake zukatan su daga hassada saboda ya ce amincin Allah ya kara tabbata a gare shi: "Sai a shayar da su sai Allah ya tsarkake zukatan su).
- Wasu daga cikin malamai sun hada tsa kanin maganganun nan suke cewa: ai mutum an halicce shi da turbaya kuma ake cudanya shi da ruhi. Haka kuma an kara masa kyaututtuka da baye-baye na zahiri da na ruhi a kan arzikin sa na duniya, haka nan mutane sun sha ban-ban a matsayin tafiyarsu da tarbiyyar su da kamalar su, hakika kyautar da ake yi musu da amfanin da suka yi da 'ya'yan itatuwan aljanna da abincin gidan Aljanna duk sun sassaba.
Kur'ani mai girma a cikin ayoyinsa ya siffanta abin sha na gidan Aljanna da mafi kyawun siffatuwa tare da bayanin siffofin masu shayar da su ('yan aljanna) masu kyawun fuska ne da tsayi madai-daici da idanuwa masu kyau suna kaikawo a kan 'yan Aljanna tare da kare masu kyau farare masu dadin shan abin sha, ba abin da ke bata hankali, kuma ba abin da ke gurbata su, abin sha ne tatacce mai tsarki ba abu mara kyau a ciki. Riwayoyi sun zo da bayani iri-iri wajen siffanta abin shan gidan Aljanna, sun siffanta cewa abin shan baye ne masu nagarta ('yan aljanna) riwayar tana cewa "abin sha ne rufaffe" an kare shi daga duk abin da ba shi da kyau kuma baya gurbata zahirinsa ko badininsa, amma bayin Allah makusantan abin shan su daga idan ruwan tasniym yake kuma Allah ke shayar da su.
An rawaito daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi yana cewa: "Tasniym shi ne yafi sharafi daga kowane abin sha a gidan Aljanna, sayyadina Muhammad tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi da alayensa daga gare shi su ke sha, amma ma'abota dama da ragowar 'yan aljanna suna sha daga tasniym din da aka cudanya shi.
Sanadiyyar hakan saboda matsayin mutane da darajojin su tun a duniya sun banbanta, to kamar haka 'yan Aljanna suma matsayi matsayi ne, wasu Allah ya ambace su "Ashabul yamin" wasu kuma "Al'aabar" (masu nagarta) wasu an anbace su da mukarrabun *makusanta). To dan haka kyatar da Allah ay yi musu da sakamakon su ya sha ban-ban tare da fifikon darajojin su a gidan Aljanna.
"Ashsharab": Ma'ana wannan lafazi duk abin da ake iya sha[1] hakika ya zo da wannan ma'anar inda Allah ke cewa:
((يدعون فيها بفاكهة كثيرة وشراب)).[2]
Suna cewa a kawo musu kayan marmari da yawa da abin sha.
((هو الذى أنزل من السماء ماء لكم فيه شراب))[3]
Shi ne ya samar muku da ruwa daga sama kuma kuna sha daga gare shi "Dahur" shione abu mai tsarki[4] a karan kansa mai tsarkake waninsa[5], Allah ya ce:
((وأنزل من السماء ماء طهور)).[6]
Mun samar da rua mai yawan tasrki daga sama.
Abin sha mai tsarki.
Zamu fahimci a karkashin wadannan ayoyin a gidan Aljanna akwai abubuwan sha iri daban-daban maus tasrki[7] da kuma dadi wadanda ke gudana a koramun gidan Aljanna, kuma wadannan abubuwa sha sun sabawa na duniya idan an kalli ainihinsa da asalinsu da kuma irin yadda suke. Saboda abin da yake gudana cikin koramar duniya ruwa ne kawai ba komai. Abu ne mai yiwuwa ruwan ya lalace idan ya zauna waje daya har ma ya dinga wari a wasu lokutan, amma abin da yake gudana a gidan Aljanna ya banbanta da na duniya ta fuska biyu, kamar yadda muka gano a littafin Allah, ayoyin Al-Kur'ani mai girma sun yi nuni a kan nau'i hudu na abin sha wadanda ke gudana a cikin koraman gidan Aljanna.[8] Koramar da ruwa ke gudana don kar da kishirwa, koramar nono don maganin yunwa, koramar zuma saboda samun karfin jiki da jin dadin bakin su, koramar giya mai sanya nishadi, wadannan koramu hudu an yi su ta yadda ba zasu caja ba, ba kuma zasu lalace ba komai tsahon zamani.[9] Tabbas ayoyin littafi mai girma sun yi nuni ga wasu sunaye kamar rahiykul makhtun ko tasniym[10] ko sharabul mamzuj bil kafur[11] ko zanjabil.[12] A wata ayar guda daya jumlar ta zo da cewa "Sharaban dahura" a inda Allah ke cewa:
((وسقاهم ربهم شرابا طهور))[13]
Allah dai shi ne mai shayarwar
RA'AYOYIN MALAMAN TAFSIRI:
Zai yiwu mu tattaro maganganun masu tafsiri da ra'ayoyin su dangane da abin sha na gidan Aljanna karkashin fahimta uku.
- Abin da ake nufi da abin sha mai tsarki wani nau'I ne na abin sha wanda 'yan Aljanna suke sha bayan sun ci 'ya'yan itatuwa da abinci, sai abin shan ya kori dattin da ke ciki daga jikin su ba abin da yake wanzuwa sai gumi mai kamshi da kuma tashin kamshin da ke fitowa har ma ya dinga watsuwa.[14] Ma'anar hakan abin sha mai tasrki shi ne: abu ne na ni'imar gidan Aljanna da 'ya'yan itatuwan ta, sai dai yanayin sa madaukaki ne da wasu siffofi da jin dadi haka riwayoyi suka kawo[15]. Ayoyin Kur'ani sun siffanta abubuwan sha na Aljanna da abin da ake shayar da mutanen gidan Aljanna, hakika ayoyin sun siffanta abin shan da masu shayarwa da mafi kyawun siffofi ta yanayin sa da kyansa da fusakunsu da ni'imar su da idanuwan su. Haka ma koren da suke dauke da su, suna kewaya 'yan Aljanna da koren giya farare abin shan mai dadi ga masu shan ('yan Aljanna). Giyar bata kawar musu da hankali, sannan ba ta isar su har ta ginshe su.[16]
- Abin nufi da abin sha mai tsarki fa'ida ce ta ma'ana da ruhi a yanayin halayya da kokari da gyaran ruhi, tabbas Allama Tabatabi'iy a tafsirin sa Almizan ya nuna mana tsarkin ruhi dangane da abin sha mai tsarki cewa yana kore kowane irin gurbatar da ta zo sanadiyyar gafala daga Allah Allah madaukakin sarki kuma yana kawar da dukkanin wani hijabin da ke hana a fuskanci Allah Allah madaukakin sarki saboda Allah yaec: Abin has mai tsarki ai mai matukar tsakakewa bayabarin kazanta har sai ya kau da ita ai kazantar shagala da gafala itama kazanta ce domin tana hana mutum fuskantar Allah (komawa gare shi)[17] kamar yadda aka rawaito daga Imam Sadik amincin Allah ya kara tabbata a gare shi: "Abin shan yana tsakake su daga komai banda Allah, saboda ba mai tsarkake wanda ya cudanya da dauda sai Allah".[18] Ya zo a cikin Adyalul bayan: hakika abin shan nan mai tsarki yana tsarkake zukatan bayi na gari daga dukkanin siffofi masu muni da bakaken tunani haka nan ma Allah zai tasrkake su daga bakin ciki da bacin rai.[19] An rawaito daga Imam Bakir amincin Allah ya kara tabbata a gare shi Allah yana tsarkake zukatan muminai daga hassada lokacin da suke shan abin shan, a yayin da yake cewa: “sai ashayar da su mako daga cikin sa sai allah ya tsarkake zukatansu daga hassada.[20]
Wasu daga cikin malamai sun ce: shiga cikin tauhidi tare da yankewa komai zuwa ga Allah shi ne cikakken tsarki, duk abin da bai dace da wannan ma'anar ba to ya rasa siffar tasrki, to kamar haka ne idan aka danganta irin wannan abin shan da ake shayar da su ta hannun masu shayarwa yana tsarkake mutum daga duk abin da ba Allah Allah madaukakin sarki ba, kamar yadda wannan ma'anar ta zo a cikin kyawawan koyarwar Ahlul-baiti amincin Allah ya kara tabbata a gare shi a matsayin tushe wanda ya tattaro bayani.[21] An rawaito daga Imam Sadik amincin Allah ya kara tabbata a gare shi yana cewa: "tabbas wannan abin shan yana tsarkake jikin su da ruhin su daga komai sai dai zatin Allah mai tsarki, saboda ambaton Allah Allah madaukakin sarki da zatinsa da ambaton sunan sa shi ne yake hana mutum gurbata da lalacewa har ma da ci baya, yana tsarkake su daga komai banda Allah, domin ba mai tsarki ko mai tsarkakewa daga dauda sai Allah".[22]
- Wasu daga malaman tafsiri sun hada bayanan nan guda biyu sai suka ce:[23] tun da mutum ya kasance an yi shi da turbaya da ruhi (wato rai) to an bashi arziki na zahiri tare da bashi kyauta ta ruhi, saboda mutane sun saba a yanayin halayyar su da ma'anar su har ma da yanayin kamarlar su to dole su banbanta a wajen amfana da cin moriyar ni'imar Aljanna. Wasu daga cikin su wato masu nagarta suna shan "rahiykum makhtum" wanda yake kare su daga dukkanin shirme kuma ya tsarkake su daga baki dayan lalacewar ruhi, amma mukarrabun (makusanta) abin shan su daga idan ruwan tasniym ne, ruwa ne tsantsa mai sanyi mai dadi na asali. Hadisin Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya zo, Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya ce: "Tasniym shi ne mafi sharafin abin sha a gidan Aljanna Muhammad (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) da alayensa suna sha daga tasniym, amman ma'abota dama (ashabul yamin) da sauran 'yan Aljana suna sha da ga macudanyinsa".[24] Kuma mai shayarwar shi ne Allah madaukakin sarki {وسقاهم ربهم شرابا طهورا} {kuma ubangijinsu ya shayar das u a bin sha mai tsarki}[25] kuma kofin wannan abin shan shi ne hakikanin sanin sa da tsananin son sa.
إن الأبرار لفي نعيم... يسقون من رحيق مختوم{[26]
Bayi masu nagarta suna cikin ni'ima ana shayar da su giya rufaffiya.
Abin da ya gabata yana bayyana mana cewa kamar yadda mutane suke da mabambantan darajoji a duniya to haka matsayinsa ya sha ban-ban a Aljanna, duk da yake kowannen su yana cin moriyar ni'imar Aljannar da 'ya'yan itatuwanta, hakan yana tafiya ne tare da kudurar ruhinsu da kuma cancantar su da haka ne bayanin Kur'ani ya zo daban-daban tare da ambaton 'yan Aljanna da sunaye iri-iri da lakabobi, sai ya ambaci wasu da Ashabul Yamiyn, wasu kuma da "Abrar" (masu nagarta) kuma ya siffanta wasu da "mukarrabiyna" (makusanta) duk wadannan suna cin moriyar Aljanna kowa gwargwadon darajarsa da matsayin sa kowa ya yadda cewa ni'imar gidan Aljanna da alherin da ke ciki cike take ta jin dadi da farin ciki da karin lafiya, sai dai ba irin yadda muke surantawa ba a duniya.
[1] Kamusul Kur'an, J4, sh 12.
[2] Shafi na 15.
[3] Suratun Nahl, 10.
[4] Kamusul Kur'an, J4, sh 242.
[5] Fakrurraziy, Tafsirul Kabir J30, sh 254.
[6] Suratul Furkan, aya ta 48.
[7] Zahirin magana ba wani bahasi game da tasrkin abin sha na gidan Aljanna ta bangaren tsarki, kamar yadda ake kawowa a duniya, saboda ba najasa da kazanta a gidan Aljanna, abin da ake nufi da tsarki a gidan Aljanna marhala ce ta samun kamala da shiriya.
[8] Suratu Muhamad aya ta 15.
[9] Makwuminshshiraziy, Alma'ad fil Kur'an J6, sh 244.
[10] Makwuminshshiraziy, Alma'ad fil Kur'an J6, sh 244.
[11] Suratud dahr 5-6.
[12] Dahr, 17-18.
[13] Dahr, 21.
[14] Fakrurraziy, Tafsirul Kabir J3, sh 254, Majma'ull bayan j10, sh 623.
[15] A komawa rayuwar Abdullahi bn Sinan daga Imam Sadik (A.S) a cikin nurussakalaini j5, sh 32-33 hadisi na 30.
[16] Suratus saffat 4-5 da 47, Zukruf, 7.
[17] Tabataba'iy, Almizan j20, sh 130.
[18] Manhajussadikiyn j10, sh 110 da majma'ul bayani, j10, sh 623.
[19] Tafsirul Adyabil bayan j13 sh 327.
[20] Tafsirissafiy minallafiy, Sayyid Ali Akbar kurashiy j11, sh 27.
[21] Jawadiy Amuly, Tafsirul maudu'iy fy Kur'an j5, sh 298-502.
[22] Dabrisiy, majma'ul bayan j10, sh 623.
[23] Jawadiy Amuly, Tafsirin Tasniym j1, sh 23.
[24] Baharul anwar j44, ilmul yakin j2 sh 1253 naklan an tasniym, an ruwaito daga Annabi (SAW) Tasniym shi ne mafi sharafin abin sha zai zo musu daga wani tudu ya dinga zubowa cikin gidajen 'yan Aljanna makusanta ke sha daga gare shi, Manzon Allah Nana Khadija, Aliyu bn Abi Dalib da zuriyar su mukusantan san a asali suna shan tasnimu zallal sauran muminai kuma na shan sa abin gaurayawa.
[25] Surar insan 21.
[26] Surar mudaffifina aya ta 27 da ta 28.