advanced Search
Dubawa
14519
Ranar Isar da Sako: 2006/05/22
Takaitacciyar Tambaya
Me ye ma’anar ayyanawa da ma’anar zabi, wanne ne ya dace da wilayatul fakihi (Jagorancin Malami)?
SWALI
Me ye ma’anar ayyanawa da ma’anar zabi, wanne ne ya dace da wilayatul fakihi (Jagorancin Malami)?
Amsa a Dunkule

Wasu suna kokarin cewa akwai fahimtoci da yawa wajen malaman musulunci game da hukumar musulunci, har ma suna kokarin gina tunanin da ke tabbatar da ‘mahangar tabbatar da shugabancin fakihi (malami), daya daga cikin fahimtoci masu yawa a cikin wannan maudu’I ta tafi a kan cewa lalle fahimtar shgugabancin malami ya rabu rabo biyu:

  1. fahimtar ayyanawa
  2. fahimtar zabi

Sai dai maganganun malamanmu wadanda suka yi fice ba sa gushewa suna bayyana cewa fahimtar da suka dogara da ita ita ce: ‘fahimtar ayyana malami da siffar cewa shi majibinci ne kuma jagora’.

A cikin fahimtar ayyanawa, shari’a ce take da alhakin ayyana malami da siffar cewa shi majibinci ne, amma a matafiya ta zabe, shari’a ce take iyakance sharudda da siffofi wadanda suka kebanta ga malami daga ragowar, sai a zabi daya daga cikin malaman (fukaha’u) wanda ya cika wadannan sharudda da siffofi.

Wasu suna ganin ayyana malami a matsayin jagora na gaba daya abu ne korarre. Sai suka ce, idan malamai masu yawa suka hadu, kuma sun cika sharudda a lokaci guda, to a nan akwai yiwuwar abubuwa biyar dangane da fahimtar ayyanawa.

  1. Kowanne daga cikinsu imamai (amincin Allah ya tabbata a gare shi) sun ayyana shi a matsayin jagora, zai iya gudanar da jagoranci mai ‘yanci ta wannan gefen.
  2. Baki dayansu an zabe su a matsayin jagorori, sai dai fakihi daya daga cikinsu ke da ikon shimfida ikonsa.
  3. Su zabi malami daya kawai domin ya zam jagora.
  4. Duk baki dayansu, an zabe su a matsayin majibinta, sai dai kowa ba zai shimfida ikonsa ba har sai ya dace da ragowar malamai.
  5. Dukkanin su an ayyana su a matsayin jagorori, ta yadda za su zamana tamkar jagora daya. Wannan ma dai ya zama irin shigen magana ta hudu.

Wasu malaman sun kore yiwuwar wadannan maganganu, bugu da kari sun yi bayani a kan magana ta farko.

Hakan zai haifar da rashin tsari, da rashin bin doka, domin kowane daga cikin jagororin zai kawo ra’ayinsa wanda yake saba wa ra’ayin dayan, wanda haka zai bata tsari, kuma ba za a taba samun biyan bukata ba, kamar tsaruwar al’umma da al’umma, wanda ya ci karo da hikimar Allah.

Sai dai mu muna karfafa maganar farko, kuma muna kawar da mushkila ta faruwar rashin tsari da rashin doka, ta karkashin abubuwa biyu:

  1. Wajibcin da’a ga hukuncin waliyyi fakihi ga kowa, har ma da su ragowar fakihan.
  2. Bai halatta ba wasu har ma da fakihai su shiga da’irar (fage) nauyin da waliyyi fakihi ya dauka ba. to saboda haka ba za mu fuskanci wata matsala ba.
Amsa Dalla-dalla

Wasu suna kokarin cewa akwai fahimtoci da yawa a wajen malaman musulunci a kan mas’alar Hukuma Islamiyya, sannan suna kokarin gina wani tunani wanda zai tabbatar da fahimtar jibintar da fakihi. Cewar akwai fahimtoci da yawa a karkashin wannan maudu’in, sannan wannan fahimtar ta kasu kaso biyu: “fahimtar ayyanawa” da kuma “fahimtar zabe”. Sai dai maganganun malamanmu wadanda suke yi fice ba su gushe ba suna bayyana cewa wannan fahimtar daya ce wacce suka dogara a kanta ita ce: fahimtar ayyana fakihi a matsayin majibinci kuma jagora. Idan ya zamana akwai wasu fahimtoci to fa an jefar da su a wannan lokacin karshen zamani har ma da can wato tun farkon tarihin fikihan shi’a, wasu mazaje masu yawa daga malamai masu fice su ma sun jefar da wannan tunanin.[1]

Hukuma ta fikihi gwargwadon fahimtar ayyanawa tana samo hujjojinta ne daga shari’a mai tsarki da imamai (amincin Allah ya tabbata a gare shi). A cikin wannan fahimta, shari’a ta musulunci ce take da alhakin ayyana fakihi waliyyi, ba zaben mutane ba. Sai dai fahimtar yin zabe tana nassanta cewa mutane su zabi fakihi kuma su ayyana shi a cikin mutane. Shari’a ba ta da wata gudunmawa sai dai wajen iyakance sharuddan zabin waliyyi majibinci domin su zabe su gwargwadon yadda ya cika sharudda.

Hakika dalilan wilaya ta fakihi, suna bayyana ayyana fakihi ya zama majibinci, babu wani masani wanda yake kokwanto, kuma masanin ka’idojin ijtihadi, kuma wani sashen malamai yana ganin koruwa tabbatuwar wilaya ga duk wanda ya sami darajar ijtihadi, sai ya dora riwayoyin da suke yin nuni a kan (jibintar aiki) a kan (dacewar wilaya), wato ma’anar maganar ita ce; shi wannan malamin ya tabbatar da cewar riwayoyin nan suna yin nuni a fili game da “fahimtar ayyanawa” sai dai yana ganin hakan wai a hankalce ba zai taba yiyiwa ba (na mustahili ne). Wai ya wajaba a dauki wannan riwayoyin a yi musu tawilin cewa, fakihi ya cancanci ya sami wannan matsayin, saboda haka, sai a ce; masu kawo shari’a (ma’asumai) sun bayyana dacewar fakihai wajen jagorancin al’umma. Sai dai wadannan riwayoyin ba su bayyana wani daga cikin fakihai ba, wanda zai karbi wannan jagorancin al’umma kuma riwayoyin sun bar al’amarin ga zabin mutane.[2]

Sai dai meye zai hana fakihi ya zama jagora?

Ina mai ba da amsa: Yayin da aka fakihai da yawa, duk sun cika sharudda,[3] to za a sami halaccin yiwuwar abubuwa guda biyar ga fahimtar ayyana jagora:

  1. Kowane Imamai (amincin Allah ya tabbata a gare su) sun ayyana shi a matsayin jagora, kuma zai yi duk abin da ya ga ya dace a wannan bangaren.
  2. Baki dayan su an zabe su domin jagoranci, sai dai malami daya daga cikinsu kawai yake da salladuwa a kansu.
  3. Fakihi daya ne kawai aka zaba don jagoranci.
  4. Dukkanin su an zabe su a matsayin majibinta, sai dai dayansu ba zai zartar da abu ba har sai ragowar sun amince.
  5. Kowannen su an ayyana shi a matsayin jagora, amma dukkanin su a matsayin abu guda suke: shugaba daya.

Abin da zai kasance sakamakon wannan fahimta, irin na fahimta ta hudu ne cewar: mutum daya ba zai zartar da al’amari ba face sai ragowar sun yi muwafaka da shi. Sannan idan aka yi watsi da wannan maganganun, to abin da zai biyo baya shi ne:

Kawar da magana ta (1) zai jawo rashin bin doka da ka’ida a cikin al’umma, saboda kowa zai kawo ra’ayin da yake iya saba wa daya malamin, wanda wannan shi ne zai bata tsarin, bugu da kari abin da ake son tabbatarwa, kamar tsara al’amura na al’umma da gudanar da bangarori mabambanta duk ba za su tabbata ba. Hakan kuma ya saba wa hikima ta Allah (tsarki ya tabbata a gare shi).

2,3 Idan aka yi watsi da magana ta (2) to fa ba zai yiwu ba, a iya ayyana malami wato fakihi mai ikon shimfida shugabancinsa ba. Ta wani bangaren ma waliccin ragowar fakihai, sai wilayar ta zama yasasshen zance, wannan kuwa abu ne mai muni, saboda haka, Allah ba zai yi haka ba, kuma ta haka magana ta (3) ita rushe.

4,5 Duk su bayin suna cin karo da matifiyar masu hankali da ta masu sharia da kari babu wanda zai amince da haka.[4]

Ana samun amsoshi a kan haka:

  1. Duk malaman an ayyana su domin jagoranci, saboda haka daukan nauyin wannan matsayin idan an jingina shi gare su “wajibi ne na isarwa” [5] ai idan dayansu ya sauke nauyin ya dauke wa ragowar.[6]
  2. Tabbas wilaya ba kamar limancin salla ba ne, ballantana mu ce kowane adali zai iya yin limanci, ai matsayin wilaya daraja ce ta musamman, tana dangantuwa zuwa ga mafi ilmi, sadauki, maf itsoron Allah, mafi kula da iya gudanar da al’amura fiye da ragowar mutane.[7]

Jawabi na farko ba ya kawar da ishkalin, kamar yadda yake gudana a hukunce-hukuncen da aka dora wa baligi ba hukunce-hukunce da aka sanya su a wani yanayi ba, kamar wilaya.[8] Saboda wajibi kafa’i yana zamantowa wajibi a kan daidaikun mutane kafin wani ya aikata shi. Saboda haka duk wadannan abubuwan guda biyar za su kasance ba tare da an warware matsalar ba a wajen.

Jawabi na biyu: Duk da cewa ba dalili a kan wannan maganar, za a sami matsala idan mun kaddara cewa mutane biyu sun daidaita a wadancan siffofin da aka fada, duk da yake wasu suna ganin faruwar hakan ya yi karanci kwarai, sai dai yiwuwar faruwar hakan yana da yawa yayin gwada mutane ko kuma gwargwadon yadda ma masoya da mataimaka suka gwada mutane tare da auna su.[9] Bugu da kari, wannan bayanin yana shakkala wani nau’i na furta matsala, sannan yana kebantar da ayyana mafi yawan ilmi, mafi tsoron Allah, mafi sadaukantaka, ba fa wai ya gane sauran malamai ba ne (fukaha’u). Tare da haka, zai yiwu a yi maganin matsalar, saboda ko wane malami yana ganin idan jagora ko majibinci ya fito da wani hukunci, to fa ya wajaba ga sauran fakihai su bi shi, har da wadanda suka cika sharuddan jibinta (wato wilaya). Dalilai na hujjojin wilaya sun hukunta haka, kuma kamar haka lamarin yake idan fakihi ya raba wani abu na abubuwan wakilci, bai halatta ba ga sauran fakihai su shiga cikin janibin aikin na sa ba duk da yake wasu sun cika sharudda.

Dangane da haka, muna karfafa magana ta farko ai baki dayan fakihai wadanda suka cika sharudda sun rabauta da matsayi na jibinta (wilaya). Ta haka ne za mu yi maganin matsalar faruwar zaman kara zube ba doka ba oda ta hanyoyi duga biyu kamar haka:

  1. Wajibcin biyayya ga hukuncin waliyyi fakihi a kan kowa yake har ma da sauran fakihan.
  2. Bai halata ba ga ragowar fakihai da sauran mutane su yi karambanin shiga cikin al’amuran da suka rataya a wuyansu ba.

Saboda haka mahangar nan ta shugabancin malami ba ta fuskanci ko wace irin mastala ba kuma ita ce mahangar mafiya yawan manya –manyan malaman shi’a, wanda daga cikn su akwai imam khomaini (Allah ya yi masa rahama) daidai ne ba banbanci a matakin tabbatar sa a shari’a ne da kuma a matakin aiwatarwa.

Tare da haka idan har muna so mu sanya doka ta dindindin wacce ba ta da iyaka da wani waje ko kuma lokaci ba za mu sami wata han ba in bat a zabin mutane ba.[10]

Domin mu bayyana lamari sai mu ce: duk ka da cewa nada dukkanin malaman da suka cika sharadan shugabanci ba zai sabbaba wata mushkila ba a wajen gudanarwa ba ko kuma ta bangaren manuniyar dalilan, (abin da za a iya fahamta daga ayoyi da hadisai ke nuni kan hakan) kuma ko wane mutan na da cikakkiyar dama komawa malamin da yake ganin cewa ya cika wadannan sharaddan sai ya nemi haske a wajen sa kan lamarin shugabanci,[11] sai dai idan muka kalli shugabancin a matsayin sa na al’amarina al’umma wanda ke bakatar kama in kama wajen tafiyar da lamuran al’umma kuma ya zama muna so mu sanya wannan lamarin doka – ko da ma kuma a bisa mahangar nan ce ingantacciya ta ayyanawa – kenan ya zama lalle mu yi riko da mahangar nan ta hanyar yin zabe.

Sai dai wannan zaben zai tabbata ne ta hanyar ayyana “malamin da ya cika sharadai” ba ayyanawar nan ta “ zaben wanda ya cika sharadai daga cikin malamai ba”, na daga abin da aka ambata a nazariyyar (mahangar) nan ta zabe. Ma’ana mutane za su zabbi malamin (shugaban) da ya cika sharadai shagabanci, ba su zabbi malamin majibincin lamarin daga cikin malaman da suka cika sharadai ba.

Domin neman karin bayani ka duba:-

Mahadi hadawi daharani a cikin walayat wa diyanat “alwilaya wald diyana” mu’assatu farhange khane dar “muassasatu darul akale assakafiyya”         Kum, bugu na 2 1380.

 


[1] Wasu Daga Cikin Malamai na baya-baya Sun yi tsa kanci daban daban kan mas’alar, misali zabin mutane ga shagaba a amatsayin san a shugaba. Dss.

[2] Almuntazari wilayatul fakihi  juzu’I na1 shafi na 408-409.

[3] A bin da a ke nufin da shi ne malamin da ya cikia sharadin shugabanci.

[4]  Almuntazari wilayatul fakihi  juzu’I na1 shafi na 409-415.

[5] Abin da ya wajaba kan tarayyar wasu daga cikin mutane kuma idan wasu ko wani ya aiwatar da shi to ya isar ga sauran kuma ya saraya daga kansu kuma ana kiransa  “wajibul kifa’i”.

[6]  Ka duba jawadi amuli shugabancin malami (srahbari danr islam)  shafi 186.

[7]  Ka duba jawadi amuli shugabancin malami (srahbari danr islam)  shafi 186.

[8] Hukunci na taklifi (alhukumut taklifi) shi ne wanda ke fuskantar ayyukan baligi kai tsaye kuma ya kasu kaso 5 , wajibi haram, mustahabbi, mukruhi da hala. (alhukumul wadha’I ) shi ne wanda ba ya fuskantar ayyukan baligi kai tsaye kamar su nasastuwa tsarki sharadi kasantuwara abu wani yanki, dss.

[9] Maana ko wane malami da m atema kansa sauna ganin shi ne mafdi ilimi, mafi tsoron Allah mafi sadaukantaka.

[10] Saboda haka ne majalisar kwararru a fagen tsara kundin mulki a kan alamarin zabe tare da cewa sun tabbatarda mahangar nan ta ayyanawa. Hakika sun y ioittifaki kan a rika gudanar da zaben ba kai tsaye ba.

[11] Wannan it ace hanyae dab a ta gud=she ba tana kuma ba za ta gushe ba it ace mafi yawan faruwa, a wajen malamai marja’o’i.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa