advanced Search
Dubawa
12232
Ranar Isar da Sako: 2012/05/21
Takaitacciyar Tambaya
Me yasa Allah bai nufin shiryar da mutane gaba daya ba, kuma kowa ya sami alheri?
SWALI
A lokacin da muka kallin ayar nan mai girma: ((ولو شئنا لآتينا كل نفس هداها)). "Da mun so sai mu shiryar da kowanne mutum". Zai bayyana cewa Allah bai so kowa ya shiryu ba da Allah yana son kowa da alheri da ya shiryar da su gaba dayan su, sai dai Allah bai aikata hakan ba don me?
Amsa a Dunkule

Tabbas abin da aka gano a cikin wannan ayar ta 13 cikin Suratul Sujada mai albarka cewa Allah bai so mutane gaba dayansu su sami shiriya ba, wannan maganar ba haka ba ce, hakika abin sabanin haka ne domin Allah ya so kowa ya shiryu domin samun kamala, wannan shi ne abin da zamu gano a wadannan ayoyi:

  1. Shiriya kala biyu ce: shiriya ta asali da shiriya ta shari'a, shiriya ya asali ita ce shiriyar da aka bawa bakidan halitta a cikin duniya. Hakika Allah (S.W.T) ya tura halittar sa saboda abin da ya sa musu na tunani da ganewa zuwa ga kamala da kuma hadafin da aka dora su a kai.

Amma shiriya ta kebanta ne ga masu hankali wadanda suke tunani, kuma ta rataya da abubuwa na shari'a kamar akida mai kyau da dokokin Allah abin da ya dace ayi da wanda bai dace ba, wannan shiriyar tazo ne ta hanyar Annabawa da Imamai amincin Allah ya kara tabbata a gare shi irin wannan shiriyar ta game mutane gada daya kuma kyauta ce daga Allah yayi musu.

Dan haka duk mutane suna amfana da shiriya ta asali da ta shari'a

  1.  Akwai ayoyi da yawa wadanda suke nuni kan cewa mutum yana da zabi kamar abin da Allah ya ce:

"إنا هديناه السبيل إما شاكرا وإما كفورا"

Hakika mun shiryar da mutum dan ya gane hanyar tauhidi, ko ya gode wa Allah (yin tauhidi, ko ya butulce masa (kin yin tauhidi).

Wannan hakika (dama) zabin shima irin shiriyarwa ce ta asali daga Allah, wannan saboda baya yiwuwa ya kasance mafarin zabin mutum da kansa saboda hakan zai jawo dawu (abu ya je ya dawo yaje ya dawo) ko kuma ta saysuli (abu ya zarce yayita tafiya ba tare da yazo karshe ba).

  1. Tabbas tsarin duniya yana guda na a kan asalin dokar illiyya da ma'alaliyya ( sababin da wanda aka sababba wa a wata fassarar ace mai samarwa da wanda aka samar). Sunna ta Allah (S.W.T) taso abubuwa su gudana ta hanyar sabubban dabi'a acikin al'amarin shiriya Allah ke samadda  hanyoyi saboda abin da ake nufi ya bayyana ga duk wanda ke neman shiriya kuma yake son hanya ta fitofili, kuima dan bawa ya kai ga manufarsa a karshe yadda abin yake kemai yadda ayoyin kur'ani mai hikima suka nuna shiryarwa ta asali (Hidaya takwiniyya ) ta game baki dayan halitta, bugu da kari mutum ya sami kari da shiriya ta shari'a, sai dai mutum an sa masa nufi da zabi a dabi'arsa da asalin sa, saboda haka an bashi zabi ko yayi amfani da wannan shiriya ta Ubangiji (shiriya ta asali) domin yayiwa kansa shimfidar samun babbar shiriya, ko ya zabi hanyar tsaurin kai ya sabawa shiriya ta shari'a, harma ya runtse idansa ya rabu da ita sai ya tafi a hanyar da zata kawar dashi daga shiriya, karshen al'amari sai ya zama ya afka cikin kafurci da zalunci. Zai yiwu mu fahinci wannan ayar cewa Allah (S.W.T) idan yaso ya mai ya mai da mutum mara zabi kamar ragowar dabbobi zai iya sai dai Allah (S.W.T)  saboda ya bawa mutum zabi sai ya dorawa mutum nauyi a cikin shiriya ta asali (Shiriya takwiniyya) da shiriya ta shari'a. ta wannan hanyar gaskiya take bayyana da karya. Idan muka dauki wannan dokar da sunna ta Allah idan mutum ya zabi bin hanyar zalunci da kafirci tofa yadda abin yake shiriyar Allah bata da ayaka da zalunci da kafirci amma wanda ya zabi tafiya a hanyar gaskiya to zai yi dace da samun babbar shiriya.
Amsa Dalla-dalla

Kafin mu shiga bayani ya zama dole muyi nuni zuwa ga wasu alamomi masu muhiommanci:

  1. Allah (S.W.T) ya ce:

((و لو شئنا لا تينا كل نفس هداها و لكن حق اقول منى لأملأن جهنم من الجنة والناس أجمعين))

Da munso da kowacce rai mun shiryar da ita, sai dai maganata ta tabbata kan cewa zamu cike Jahannama da Aljanu da mutane.[1]

  1. Ma'anar shiriya: shiriya tana da ma'anar nusarwa tare danunawa mutum hanya saboda tausasawa (ludufin Allah wajibi ne wato tausasawa don samun shiriya) da nufin alheri.
  2. Shiriyar Allah iri-iri ce: idan muka kalli ayoyin kur'ani mai hikima game ga sun kasa shiriya kar biyu: 1. shiriya ta asali 2. Shiriya ta shari'a. shiriya ta asali ita ce wacce ta game komai kuma Allah (S.W.T) shike tura ababan halitta har su kai ga cika tare da samun biyan bukatar yinsu saboda kudurar da Allah ya basu ayar kur'ani ta nuna hakan inda Allah ke cewa:

((ربنا أعطى كل شيء خلقه ثم هدى)  [2]قال تعالى : ألذ من خلق فسوى" والذمن قدر فهدمن))[3]

Ubangijimu shi ne wanda ya bawa komai  kyautar halittarsa, bayan nan kuma ya shiryar da su.

Allah shi ne wanda ya yi halitta kuma ya dai daita ta, shi ne wanda ya iya kance komai sannan ya nuna masa hanya

Amma shiriya ta shari'a (Hidaya tashriyaya) shiriya ce kebantacciya wacce aka bawa masu hankali da tunani, kuma ta rataya da abubuwa na shari'a kamar akidoji na gaskiya da dokokin rila abin da ya kamata ayi da kuma abin da bai daceba, wannan shari'ar tazo ne daga wajen Annabawa da Imamai ma'asumai amincin Allah ya kara tabbata a gare shi, Allah yana cewa: 4

((فريقا هدمن وفريقا حق عليهم الصلالة)).

Wasu bangaren Allah ya shiryar da su wa kuma bata ya fada musu.[4]

A wata ayar Allah ya ce:     "والله يهدى من يشاء إلى صراط مستقم"

Allah ke ya shiryar da wanda yaso zuwa hanya madai-daiciya.[5]

Zamu gane cewa abin nufi da wannan shiriyar shiriya ce ta shari'a, kamar yadda shiriyar nan duk da yake ta kebanta da nufi ne ba ta da alaka da sauran ababan halitta, amma fa ta game dai-dai kun mutane (ko wanne mutum shari'a tana aiki a kan sa) 

  1. Zabin mutum a matsayin shirita ce ta asali (Hidaya takwiniyya) mutum saboda kasancewar Allah ne ya halicce shi, bawansa ne ya bambamta dasauran halitta domin Allah ya halicce shi mai 'yanci , akwai ayoyi dagugugwa a kur'ani wadanda suke karfafa 'yanci mutum da zabinsa Allah ya ce:

((وقل الحق من ربك فمن شاء فليؤمن ومن شاء فليكفر))[6]

"Ka fadi gaskiya duk wanda ya so ya yi imani, wanda ya so ya yi kafirci".

Allah ya kuma cewa:

((إنا هديناه السبيل إما شاكرا وإما كفورا))[7]

Tabbas mun nunawa mutum haya ko dai ya zama ya mika wuya ga Allah (godiyar ita ce muka wuya) ko kuma ya kafirce (ya ki gode masa), sabdoa haka, mutum idan ya so sai ya yi wani aiki idan bai so ba ba zai yi ba, wani mawaki ba'iraniye ya bayyana wasu baitoci yana cewa: "Hakika idan nace yi wannan ko wancan wannan yana nuna zabin mutum.[8]

Hakika wannan 'yancin wani bangare ne daga halittar mutum da kasancewarsa, kuma baya rabuwa da mutum a cikin kowanne yanayi cikin halaye, saboda haka mutum an dora shi a kan zabi da 'yanci, kuma da ya kasance wanda ake bawa zabi a cikin zabibn da aka bashi to fa a irin wannan yanayin zai iya zabar ya zamanto mara zabi ba a samun mutumn wanda zai zamanto mara zabi. To a nana zamu gane cewa asalin zabin mutum ba zai yiwu a ce shi ne mutum din ba idan ba haka ba to za a gamu da mushkilar daur (tafiyar abu gaba sa'annan ya dawo baya tare da maimaituwar hakan) ko kuma matsalar tasalsuli (abu ya zarce ba tare da yankewa ba). Shi mutum yana da zabin ayyukan sa, yana da 'yanci gwargwadon fidirar sa (asalin tsarin halittarsa) ko ya aikata ko ya bari wannan ce hidaya takwiniyya.

  1. Tsarin halitta da sunnar Allah: tsarin halitta ya dogara ne a kan tushen dokar iliyya da ma'aluliyya. Hakika sunnar Allah ce ta ta sabbaba gudana abubuwa a kan asalin sabubba da yanayin gudanar dabi'a, a cikin mas'alar shiriya Allah Allah madaukakin sarki ya cika duk hanayoyi da abubuwan da suke bayyana manufar sa tare da gano su, har ma akai gare su ga duk wanda ke son ya kai gare su, kuma don saboda bawa ya gano manufar Allah ta karshe.

Idan muka kalli wadannan nukudodi da aka ambata da idon lura kuma kamar yadda aya ta bayyana za mu ga hidaya takwiniyya (shirya ta asali) ta game komai. Tabbas mutum ya sami sharafin hidaya tashri'iyya bayan ya sami hidaya takwiniyya. Sai dai idan an duba za a ga mutum an halicce shi yana dauke da siffar zabi da 'yanci a dabi'ar sa da asalinsa, don haka ne yana da zabi dangane da neman taimakon shiriyar Allah (hidaya tasari'iyya) don ya share fagen samun shiriya babba, kamar yadda yake da ikon ya zabi yon tawaye ga shari'ar har ma kuma ya kau da kai daga gare ta har ya shiga wata hanyar da ba waccan ba, wanda karshen al'amari sai ya fada cikin kafirci da zalunci.

Ayar da muka kawo a farkon bayanin mu tana bada hasken cewa zamu iya gano cewa manufar Allah idan ta so zata iya sanya mutum halinsa ya zama tamkar na ragowar halittu wadanda basu da zabi (dabbobi da sauran su), sai dai manufar Allah ta bawa kowanne mutum shiriya ta asali da ta shari'a, kuma a dai-dai wannan lokacin ta ba shi 'yanci da hakkin zabi wanda wannan shi ne ya sa mutum aka dora masa nauyi (taklifi) dan ya banbance gaskiya daga karya.

Ya bayyana a fili da'awar cewa Allah Allah madaukakin sarki bai yi nufin shiryar da baki dayan mutane ba wannan idan mun dogara da aya 13 a suratus Sajda, wannan da'awar da'awa ce mara kyau, sabanin wannan maganar shi ne dai-dai domin Allah ya yi nufin shiryar da duk halitta, sai dai yadda sunnar Allah take gudana mutumin da ya zabi bin hanya mai duhu da zalunci har ma da kafirci to shiriya ta ALlah ba zata same shi ba, domin ba zai yiwu shiriyar Allah ta rataya da shi ba[9] amam mutumin da ya zabi tafiya a cikin hanyar gaskiya zai dace da samun shiriyar babba[10] Allah ya ce:

((والذين جاهدوا فينا لنهدينهم سبلنا وإن الله لمع المحسنين))

"Duk waanda suka yi kokari saboda mu to tabbas za mu nuna musu tare da shiryar da su hanyar mu, hakika Allah yana tare da masu kyautatawa". [11]da[12]

 


[1] Sajda, 13.

[2] Daha, 50.

[3] A'ala, 2-3.

[4] A'araf, 30.

[5] Bakara, 213.

[6] Kahfi, 29.

[7] Insan, 3

[8] Maulawiy, Masnawiy ma'anawiy.

[9]  Duba Albakara 264, Ma'ida 67, Tauba 37, Tauba 80.

[10] Duba Albakara 264, Ma'ida 67, Tauba 37, Tauba 80.

[11] Ankabut, 69.

[12] Mun dogara da littattafan da zamu kawo a wajen bada amsa: Allama tabataba'iy Tafsirul Mizan, I 14 sh 214 sh 214 sh 66 j17, sh 167, j32, sh 80. Makarimushshiyraziy, Tafsirul Amsal fi Tafsiri Kitabullahil Munazzal): I 1, sh 67 da 430 da j2 sh 259 da abinda ya zo baya j17, sh 166 da abinda ya zo baya da j25, sh 366 da j11 365, 233 har ya zuwa sh 226 da 420 da abinda ke bayansa.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa