advanced Search
Dubawa
22510
Ranar Isar da Sako: 2006/06/03
Takaitacciyar Tambaya
Mana neman a fassara mana wannan ayar mai albarka: (لا إكراه فى الدين قد تبين الرشد من الغي...)) Tare da bayanin tafsirai daban-daban na ita ayar.
SWALI
Mana neman a fassara mana wannan ayar mai albarka: (لا إكراه فى الدين قد تبين الرشد من الغي...)) Tare da bayanin tafsirai daban-daban na ita ayar.
Amsa a Dunkule

Idan muka dubi tafsirin da aka kawo dangane da ayar nan mai albarka zamu iya qididdige tafsirin a cikin maganganu guda biyar, ingantacciyar maganar tana xauke da saqo wanda ya game kowa da kowa har ma da mutuntaka. Ma'anar ita ce: addini dai mas'alace ta aqida da abin da ya shafi zuciya ba damar tilastawa da takurawa a cikin fage na addini kuma an bawa bawa zavi. Wannan yana yin nuni a fili cewa maganar wxanda suke ganin cewa an tilasta mutum an xora shi dole ya karvi Musulunci, ko kafirci kuma an yi masa tilas ya yi ibada idan mai ibada ne (kamar yadda rana take fitowa, dole ta bada haske, ai kaga rana ba ta da zavi a haka aka yi ta, to shima mutum haka ne) idan mai savo ne shima haka Allah ya xora shi kai har ma sauran ayyukan mutum", kuma a wannan lokacin qarshen ayar idan an haxa shi da ayar dake binta yana kore wannan maganar kuma hujja ce a fili ga waxanda suka yadda da tafrid (Allah ya bar mutane) saboda sun riya cewa Allah maxaukakin sarki bayan da ya halicci mutum sai ya bar abubuwa ya miqa duk al'amura ga mutum da zavin sa wai shi Allah matsayinsa na mai kallo ne kawai har ya zuwa ranar alqiyama, wannan maganar ba dai-dai ba ce saboda qarshen ayar da abin da ke bayanta yana sanar da mu cewa babu wani abu da ya fita daga kulawar Allah da ikonsa.

A wani bayanin: kamar yadda ba tilastawa ba takurawa a fagen yin Imani da aqida, to fa mutum ba zai saddakai ba ya yi Imani dole dan an fi qarfinsa ba, bugu da qari ba zai yiwu ba mutum ya fice daga qarqashin mulkin Allah ba da qudurar sa da qarfin sa ba, ai kamar yadda abin yake gudana duk waxanda suka kafircewa xagutu (duk abin da ake bi ba Allah ba) suka yi imani da Allah Allah maxaukakin sarki, a qa'idar illiyya da ma'aluliyya (mai samarwa da abin samarwa) sun yi riqo da igiyar Allah amintacciya wacce ba ta tsinkewa kuma sun yi shimfixa mai kyau dan samun shiriya da kuvuta har ma da gujewa duhun da zai iya bijiro musu a hanyar su nan gaba, ai suna fafiya a cikin duhu don su kai ga riskar haske, savanin waxanda ba su saurari hujjoji maxaukaka ba da dalilai masu bayani a fili har ya zama sun zavi kafirci tare da tsaurin kai, haqiqa sun bar haske sun tafi wajen duhu haka yanayin yake kasancewa kuma dokar Allah ma haka take (wanda ya zavi kafirci to ya bar haske zuwa duhu).

Don haka, duk da cewa mutum yana da ikon zavi (ya yi mai kyau ko mara kyau) shi dai ba shi da ikon zavi a cikin aqibar aikin da ya zava da kuma abin da zai samu bayan zavin nasa, shi dai mai bi ne tare da miqa wuya ga yadda Allah ke gudanar da al'amura, ma'ana hakan tana nufin ba shi da zavi a sakamakon ayyukansa.

Abin da zamu gane daga ayoyin nan biyu masu albarka shi ne, zamu kai ga wata ma'ana kuma doka ce mai gamewa wacce ta zo daga hasken imaman Ahlul-baiti amincin Allah ya qara tabbata a gare shi:

((لا جبر ولا تفويل بل أمر بين أمرين)).

"Babu Jabr (tilastawa) babu tafwid (Allah ya barmu ba tare da ya jivince mu ba bayan da ya halicce mu) sai dai yadda abin yake al'amari ne tsa kanin jabru da tafwidu.

Amsa Dalla-dalla

Kafin bayanin ma'anar ayar mai albarka:

((لا إِكْرَاهَ فِي الدِّينِ قَدْ تَبَيَّنَ الرُّشْدُ مِنْ الغَيِّ فَمَنْ يَكْفُرْ بِالطَّاغُوتِ وَيُؤْمِنْ بِاللَّهِ فَقَدْ اسْتَمْسَكَ بِالْعُرْوَةِ الْوُثْقَى لا انفِصَامَ لَهَا وَاللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ))[1]

Kafin mu shiga cikin bayanin dole zamu ba da haske game da wasu muhimman wurare saboda yin sharar fage, kamar haka:

  1. Ma'anar ikrah ita ce tilastawa mutum yin wani aiki, ma'anar rushd kuma shiriya da samun kamala har da tsira, ijbar shi ne sa mutum abu ba tare da ya yadda ba[2] bugu da qari "algayyu" tana nufin tafiya a cikin halaka karkacewa dai-dai da nisancewa haqiqa[3] Allama Tabataba'iy yana cewa: "Warrushdu dacewa da al'amari da samun tsakiyar hanya kishiyar sa ko algayyu (vata) abubuwan nan guda biyu sun fi gamewa da faxi fiye da shiriya da vata.[4]
  2. Tabbas maganganun malaman tafsiri game da wannan ayar mai albarka ((لا إكراه فى الدين)) zai yiwu mu tattare su cikin maganganu biyar kamar yadda mai majma'ul bayan da wanin sa suke yi:
  • Ayar tana magana a kan ahlul kitabi ne kawai waxanda ake karvar jizya (haraji) a wajensu.
  • Ta shafi baki xayan kafirai sannan aka shafeta da ayoyin da suka ce ayi yaqi[5] da jihadi.[6]
  • Abin da ake nufi karku ce da wanda ya shiga Musulunci bayan yaqi ai ya shiga ne tilas saboda idan ya gamsu bayan yaqin ya inganta Musuluncin sa to ai bai zama wanda aka yiwa tilas ba.
  • Ta sauka ne a kan wasu vangare na ansar (mutanen Madina). Kamar yadda aka kawo qissoshi da yawa a kan saukar ta daga cikoi akwaii cewa: ta sauka ne saboda wani baqin bawa sunan sa Sabili uban gidansa ya tilasta masa sai ya Musulunta.
  • Wasu daga cikin malaman tafsiri sun ce ayar ba ta da wani dalilin sauka kevantacce, abin da ake nufi da ita shi ne babu takurawa a cikin addinin Allah shi dai bawa yana da zavi saboda haqiqanin addini aikin zuciya ne, amman abin da aka tilasta shi ya furta shi kamar sharaxa biyu (ash`hadu an la'ilaha illallahu wa ash`hadu anna Muhammadar rasululla) ba fa shi ne addinin ba, kamar yadda duk wanda aka tilasta shi ya yi lafazin kafirci bai zama kafiri ba, abin nufi da addini mai kyau sananne addinin Musulunci shi ne addinin da Allah ya yadda da shi.[7]  Abin da ya fito fili a baki xayan maganganun nan ita ce maganar qarshe wacce ta fi kusanci da inganci, zai yiwu mu gano abin da Qur'ani yake nufi a qarqashin wannan ayar, tabbas addini ba zai kasance abin tilastawa ba ba tare da zavin mutum ba saboda hanyar gaskiya da shiriya sun bayyana kamar yadda hanyar vata da halaka t bayyana a fili, duk mutum yana da 'yanci ko ya zavi imani ko kafirci, wanda ya so ya yi imani wanda ya so ya yi kafirci, zamu iya fito da wani asali mai gamewa wanda ya zo a harshen Imamai amincin Allah ya qara tabbata a gare su idan muka karanta wannan ayar maxaukakiya a tare da duban abin da ya zo kafinta da bayanta. Wannan asalin shi ne "ba tilastawa ba tafwid sai dai abu ne tsa kanin abubuwa guda biyu".[8] Saboda ayar da ta gabata ta bayyana mas'alar tauhidi a fili, abin da mutum yake iya gare shi da tunaninsa na haqiqa (na asali) kai da zarar mutum ya lura ya xan yi tunani kaxan zai gano hakan, sai masu tunani mara kyau zai yiwu su kawo gurvataccen tauhidi. Saboda haka ne wannan ayar da abin da ke bayan ta suka bada sura bayyananniya da bayanin qa'ida mai gamewa domin a hana su (masu gurvataccen tauhidi) samun dama.

Sannan asalin "ba jabru (tilastawa) ba tafwid (wato janyewar Allah) duk da yake tushen sa da wajen gudanar da aikin abu ne wanda ya shafi ilmul kalam sai dai zai yiwu mu gano hakan a wasu wuraren kamar ilimin siyasa da tattalin arziqi da sauran su.

A wani bayanin: wannan dalili ne a fili wajen yiwa 'yan jabru ridda masu cewa mutum an xora shi a cikin imanin sa da kafircin sa da ibadunsa da savon da yake yi da ma sauran ayyukan da yake yi, yadda al'amarin yake ai ba haka ba ne.[9] Haqiqa Allah maxaukakin sarki bai xora kowa ko ya takura shi ba, kamar yadda ayar za ta iya zama raddi a kan yan mufawadha masu cewa Alalh Allah maxaukakin sarki bayan da ya halicci mutum sai ya rabu da shi dan haka sai ya fauwala al'amura a hannun iradar mutum da zavinsa shi kuma matsayin sa kawai na me kula ne har zuwa ranar alqiyama, Abu Muslim ya ce: ma’anar al-Qafal ita ce: Allah bai gina al'amarin imani ba a kan jabru da tilas ba, shi dai Allah ya gina shi a kan zavi da yiwuwa, akwai wani abin da ke nuni ga wannan ma'anar ma shi ne yayin da Allah ya bayyana dalilan tauhidi bayani mai warkarwa sai ya ce: babu wani uzuri dangane da kafitrci sai dai idan an yiwa mutum dole ya yi imani, wannan kuma baya yiwuwa a duniya domin gida ne na jarrabawa domin idan aka takura aka tilasta mutum dan ya shiga addini to ai tun daga nan an vata maganar jarraba shin da aka ce. Ayar Allah tana qarfafa wannan maganar:

((قد تبين الرشد من الغي...)).

Yana nufin alamomi (dalilai) sun bayyana hujjoji sun fito fili, ba abin da ya yi saura sai hanyar tilastawa wato dole, wannan kuma hanyar ba ta dace ba domin ta savwa nauyin da aka xora masa (taklifanci) wannan abin da Abu Muslim da Qaffalu suka faxa ya dace da aqidar mu'utazila.[10] Ayar ai hujja ce a kan waxancan domin ba ta nuna kuskuren 'yan jabru sai ta biyo baya da wannan magana ba tare da jinkiri ba take mai cewa:

((فمن يكفر بالطاغوت ويؤمن بالله فقد استمسك بالعروة الوثقى لانفصام لها والله سميع عليم))

Duk wanda ya kafircewa xagutu (duk abin da ake bautawa ba Allah ba) ya yi imani da Allah to yayi riqo da igiya amintacciya wacce ba ta tsinkewa, Allah shi ne mai ji masani. Idan mun waiwayi ayar da ke bin wannan wacce take sanar da mu cewa jivintar Allah da sunnar sa zai yiwu mu gano a fili cewa ba wani abin wanda zai iya fita daga mulkin Allah da ikonsa.

A wata fassarar: dai-dai ne ba jabru ba tilastawa a cikin Imani da aqida, sai dai wannan baya nufin fita daga cikin mulkin Allah da masarautar sa, ai waxanda suka bijirewa kafirci suka kafircewa xagutu suka yi imani da Allah maxaukakin sarki da hukuncin dokar illiyya da ma'aluliyya haqiqa sun yi riqo da isiya amintacciya (mai qwari) wacce ba za ta tsinke ba. Kuma sun yi shimfixar da ta dace domin samun shiriya da rabauta kai har da kuvuta daga duhun da yake rufe musu hanya nan gaba, ai suna tafiya daga wajen duhu zuwa haske, saboda dalilan da suke bayani a fili har suka zavi kafirci da tsaurin kai to su waxannan a bisa ma'aunin waccan sunnar ta Allah da doka Allah suna tafiya ne daga haske zuwa duhu.

Sakamako: Daga abin da ya gabata zamu gano asalin kan maganar (ba jabru) abin da farkon aya maxaukakiya ke yin nuni zuwa gare shi,
((لا إكراه في الدين...)) ba dole ba takurawa a cikin addini ((ولا تفويض)) babu fauwalawa abin da qarshen ayar ke magana a kai ((فمن يكفر)) duk wanda ya kafirce. To wannan asalin zai taimaka mana a wajen warware qulle-qulle da yawa da mushkiloli na tunani waxanda suke bijirowa hanyar mu.

 


[1] Bakara, 256.

[2] "Kamusul Kur'an" j3, sh 100 Sayyid Ali Akbar Karashiy.

[3] Kamusul Kur'an" j3, sh 100 Sayyid Ali Akbar Karashiy.

[4] Tafsuryk nuzab j2 sh 342 Allama Tabataba'iy.

[5] Tauba, 5.

[6] Tauba, 73.

[7] Majma'ul bayan Allama Dabrasiy j 2, sh 631; tafsirul amuly, al'amuly Ibrahimiy, j 1, sh 515-516: Kashshaf, Zamkashriy, j 1, sh 487: Tafsirul Amsal, Makamush shiraziy j 2, sh 279 da 280.

[8] Kafiy j1, sh 160, Babul Jabri Wal Kadari.

[9] Tafsiri Adyatil bayan fi tafsiril Kur'an, sayyid Abdul Hussain j 3, sh 18.

[10] Attafsiril Kabiyr, Fakhruddeenirraziy j 3, sh 15; bahrul uhid j 2 sh 617.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa