advanced Search
Dubawa
11839
Ranar Isar da Sako: 2007/01/28
Takaitacciyar Tambaya
shin mutanen da suke rayuwa a cikin koguna danganensu na komawa zuwa annabi Adam kuwa?
SWALI
shin mutanen da suke rayuwa a cikin koguna danganensu na komawa zuwa annabi Adam kuwa?
Amsa a Dunkule

Hakika zabar koguna da duwatsu domin rayuwa ga tsatson Adam amincin Allah ya tabbata a gare shi lamari ne da alkur'ani ya tabbatar da shi, amma dangane da abin da ya shafi mutanen da suka gabaci Adam amincinAllah ya tabbata a gare shi, akwai abubuwa masu yawa da ke nuna cewa bil’Adama ya rayu a cikin koguna, kuma wannan lamari ne da ba zai yiwu a musa shi ba, kuma ya zama wajibi a kokkoma ya zuwa alamomi da kuma rubuce rubucen da ke jikin bangwayen kogunan domin a gano zamanin da wadannan rubutun ke komawa zuwa gare shi.

 A bisa kowane yanayi dai halittar annabi Adam amincin Allah ya kara tabbata a gare shi ba ta komawa ya zuwa wani zamani mai tsawon gaske.

 Jawabi dalla dalla

Domin mu cimma fayyaceccen jawabi dalla-dalla babu makawa da yin nuni zuwa lamaura masu zuwa:

  1. Akwai dalilan masu yawa da ke yin nuni abisa samuwar bil’Adama a zamanin da ya gabacin na baban bil’Adama annabin Adama amincin Allah ya kara tabbata a gare shi.

Marigayi allama dabadaba’I yana cewa: daga cikin ayar nan ta suratul bakara za a yi shinshinowa cewa: dan Adam ya rayu a doron kasa kafin a halicci annabi Adam amincin Allah ya kara tabbata a gare shi kuma bisa wannan asasin ne ma mala’iku suka fuskantar da tambayar su zuwa ga ubangiji, a yayin da suka ce: “sai suka ce shin ka sa wanda zai yi barna a cikinta ya zubar da jinani alhali gamu muna yi maka sujjada kuma muna tsarkake ka”.[1] saboda abin da ke damfare a cikin kwakwalensu na daga yadda taruhin bil’Adama ya kasance kafin Adam amincin Allah ya kara tabbata a gare shi.[2] hakika saduk ya nakalto fadin imam assadik amincin Allah ya kara tabbata a gare shi a cikin littafin tauhidi, a inda yake cewa: “ta yiwu ka yi tsammanin cewa kadai wannan duniyar Allah ya halitta, kuma Allah bai halicci wasu mutane ba in ba ku ba, sam bah aka ba ne na rantsa da Allah, Allah ya halicci miliyoyin duniyoyi kuma da miliyoyin Adam, kuma kana rayuwa ne a cikin duniya ta karshen daga cikin wadannan duniyoyin”.[3]

  1. Za a iya tabbatar da samuwar irin dangin dan Adam din da ke rayuwa a yanzu wadanda suka kasance suna rayuwa a cikin kogo, wannan kuwa ta hanyar zane da rubuce-rubucen da aka sama a jigin bangon koguna,[4] sai dai shin wadannan alamomin suna nuni ya zuwa cewa su wadannan mutanen da suka rayu a cikin wadannan koguna suna da gantaka da bil’Adama wannan zamanin ko kuma danganen sun a hade wa da ibil’Adaman da ya rayu a zanin da ya gabata, wannan shi ne a binda muke kokarin tabbatarwa.[5]

 Sai dai, wasu daga cikin a yoyin sun yi nuni a sarari cewa bil’Adaman da ke rayuwa a wannan zamanin ba nasabar sa na tukewa ne zuwa ga annabi Adam amincin Allah ya kara tabbata a gare shi da kuma matar sa Hawa’u, Allah Madaukaki yana cewa: “ya ku `ya`yan Adam kar ku bari shedana ya rude ku kamar yadda -ya rudi mahaifanku - ya fitar da mahaifanku daga aljanna”.[6]

 Kuma mun san cewa lalle kur’ani littafi ne na dukkanin matane, kuma yana magana ne da dukkanin mutane, kuma yana fadi a cikin wata ayar “ya ku matane ku ji tsaro ubangijin ku wanda ya halicce ku daga mutum daya kuma ya halittar masa matar sa daga jinsinsa kama ya fitar da (ya yada) mazaje da mataye daga gare su”.[7]

 A bisa wannan asasin idana har aka sami wata alama da ke nuna cewa an sami wasu mutane da suka rayu a doron wannan kasar tun kimanin miliyoyin shekaru da suka wacce, babu makawa wadannan alamomin za su kasance ba na al’ummar da nasabar ta take dangane wa da wannan al’ummar ba ne. domin a bisa zahiri kissar ahalittar annabi Adam ba ta wacce shekara 7000 da suka gabata ba.[8]

 Amma idan alamomin na nuni ya zuwa cewa sun kebanta da bil’Adaman da ya rayu bayan wancen zamanin, ta ya tabbata ke nan alamaomin na da alaka da mutanen farko daga cikin dan Adam din wannan zamanin, kuma wannan na nuna cewa matanen farko daga cikin `ya`yan Adamu sun zauna a cikin koguna.

 Sanannen abu ne cewa ba zai taba yiuwa mu kwatanta yanayi da tsarin gidajen a zamanin da ba da kuma zamanin da muke cikin wannan kuma manuniya ce a sarari da ke nuna cewa gidaje a zamanin da suka gabata san kasance a saukake ba su kai sun kawo ba, wadanda ake yin su da saukakan abubuwa, har ta kai ga cewa mutanen farko kan fake a cikin lokuna da kuma kogunan da ke cikin duwatsu domin su kare kawukansu daga mummunan yanayin shekara mai cutarwa (kamar sanyi da zafi da ruwa) ko kuma dabbobi masu cutarwa, wannan kuwa abu da yanayi ke haifar da shi a sakamakon rashin isassun kayayyakin ginin da za a gina gida da su, kuma hakika Kur’ani yayinuni ya zuwa haka a yayin da yake cewa: “kuma ya sanya muku gidaje (mafaka) daga duwatsu”[9]

Kuma Kalmar na ta “aknan” jam’I ne na Kalmar “kannu” wanda ke nufin abin da zai suturta mutum ya rufe shi kuma saboda haka ne ma a ke kiran makwarkwadar duwatsu da lokunan su da kuma kogonsu da sunan mafaka “aknan, kuma yana da kyau a nan mu lura da cewa an ambaci gidaje ko wannan mazauna ta koguna a matsayin ni’ima babba wacce bai kamata a gafala daga gode mata ba,[10] kamar yadda ya tabbata cewaan ci gaba da rayuwa a cikin irin wadannan koguna zamani mai tsaho har ya zuwa zamanin kere-kere, har wala yau wannan na daga cikin a bin da ake sa shi a jerin ci gaba na dan Adam, kamar yadda wannan bayanin ya zo a cikin Kur’ani mai girma, a yayin da yake magana a kan mutanen da suka kasance suna fafake dutsai suna maid a shi gida kuma sun kasance suna rayuwa a cikin ni’ima da jin dadi.[11] Saboda haka lalle samuwar bil’Adaman da nasalar sa ke tukewa ga annabi Adama amincin Allah a gare shi ba wani a bu ba ne da yayinesa da tunani ba, kuma babu wata mishkila a cikin hakan.  

 


[1] Tarjamar al-mizan juzi'I na 4 shafu na 223

[2] Masdarin da ya gabata shafi na 231.

[3] Shashin mutane suna kudurce cewa yana daga cikin abubuwan da mazauna coguna su na daga cikin tsatson annabi Adam amincin Allah ya kara`1 tabbata a gare shi daga Da'iratul ma'arif sabo mujalladi na 4, shafi 331.

[4] Tarjamar al-mizan juzu'I na 4 shafi na 223.

[5] Tarjamar al-mizan dugun jama'atul mudarrisina juzu'I na 4 shafi na 223.

[6] Surar a'arafi, shafi 27.

[7] Surar nisa'I aya ta 1.

[8] Domin samin karin masaniya ka duba maudu'in: rayuwar jinsin dan Adam a cikin littafin manzurul kur'anil karim, tamba yata 701.

[9] Surar nahali aya ta 81.

[10] Duba: tafsiirul amsal juzu'I na 11 shadfi na 346.

[11] Duba: mawaka 149.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa